Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Dangane da ma’ana, “Bazawara ita ce matar da aurenta ya mutu, ko mijinta ya mutu ta gama idda tana zaman gida kafin ta sami wani miji” (CNHN, 2006 sh. 43). Muhammad (2020) ya bayyana asalin kalmar bazawara kamar haka:
A zamanin da, matuƙar
Bahaushe ya aurar da ‘yarsa
a gidan miji, idan ta fito, al’adarsa
ta hana ya zauna da ita a ɗakin
uwarta, sai dai a toshe ƙofar zaure ta waje sai ya zama ɗaki
ta zuba kayanta. Daga nan sai a sara wata ƙofar a jikin katanga, wadda ake kira
sare. Idan abokan wasan waccan mata sun shigo sai su rinƙa tsokanarta suna ce
mata, matar aure, ko ta zaure, ko bazauriya, ko zaura, da haka har dai ya koma
Bazawara. (Muhammad, 2020 sh. 315)
Akwai wani ra’ayin ko bayan
wannan. Wasu na ganin kalmar zaura ta samu ne daga kalmar saura. Wato gonar da
ba a nomawa. Alƙur’ani
mai girma ya kwatanta mata da gonaki ga mazajensu. Duk gonar da ba a noma ba ba
ta buƙatar
jewaya domin ta zama saura. Da haka, yau da gobe sai kalmar ta sauya zuwa
zaura.
Hausawa sun ƙirƙiri
karin magana masu yawa da suka alaƙanta da bazawara. Daga cikinsu akwai:
1. Abin na yi ne, an biya wa
bazawara Hajji
2. Bazawara uwar son banza
3. Daga baya ke nan, an yi sadaka
da bazawara
4. Kai waye, bazawara da jaka
5. Son kira kamar bazawara
A ƙasa an kawo sharhin wasu daga cikin karin
magana da suka shafi bazawara:
1. Zawara zauren ƙarya
Zaure yana nufin, ɗaki mai ƙofa
biyu wanda ake fara shiga ta cikinsa kafin a shiga cikin gida. Kafin tsarin
gine-gine na zamani, zaure yana ɗaya
daga cikin fitattun siffofin gidajen Hausawa.
Wannan karin magana tana nuna
yadda al’ada take kallon zawara a matsayin mace mai yawan ƙarya
domin ta cimma burinta na rayuwa; a lokacin zawarcinta. An jingina ta ga zaure
ne, kasancewa ga al’adar
Hausawa ta zamanin gargajiya zaure ne ake fara shiga, kafin a shiga cikin gida.
Kasancewar ita bazawara mai fuska biyu, shi ya sa aka danganta ta da zaure, ga
shi kuma bugu da ƙari, ga al’ada
zaure ake mayar wa ɗakinta.
Bazawara na iya cewa, bazawari ɗaya
ke gareta, alhali kuma sun fi goma, haka kuma tana iya cewa, ga abin da ya
rabota da tsohon gidan mijinta, amma ƙarya take yi ba haka abun yake ba.
A wasu lokuta, akan yi amfani da
wannan karin magana ga wanda ya faye faɗin
maganar da ba gaskiya ba. Ana kuma amfani da karin maganar domin jaddada halin ƙarya
ko wani salon rayuwa marar kyau da wata bazawara ta nuna, tamkar dai a jaddada
cewa ‘za ta rina.’
2. Son kira, kamar bazawara
Wannan karin magana shaguɓe ne da ke nuna cewa mace
bazawara tana tsananin buƙatar kira daga masoya domin kyautatuwar rayuwarta da kuma fita
daga cikin yanayin da ta samu kanta na rashin miji. Ana kuma amfani da wannan
karin magana a yi shaguɓe
ga duk wani mutum da yake tsananin buƙatar wani abu, kuma ya kasance yana
sauraron ya ji ina ne zai samu mafita, da hanyar cimma wannan abun.
3. Kai waye, bazawara da jaka
Wannan karin magana tana nuna
cewa manufar bayyananna ce bazawara da jaka (Jikka) wato, kasancewar al’ada
tana kallonta da halayya ta mace mai son a yi mata kyauta. Da kuwa an yi mata
kyauta sakawa kawai za ta yi cikin jaka a sauƙaƙe ba tare da wata wahala ba. Ana amfani
da wannan karin magana a nuna cewa, mai jiran tsammani ya yi tanadi domin
shirin ko-ta-kwana.
4. Bazawara uwar son banza
Wannan kirarin yana nuna cewa,
bazawara mace ce wadda ta fi sauran mata tsananin son a ba ta kyauta ba tare da
ta yi wani aiki ba, haka kawai. Haka kuma, ta faye cewa, a ba ta, don ita a
wannan lokaci ba ta da wata sauran kunya a idonta, kuma in har kana zuwa gunta
zance ba ka ba ta komi, to sai ta yi ƙoƙarin tallataka a matsayin matsolo wanda
ba ya da alkhairi, amma da zarar kana zuwa zance kana ba ta kuɗi da wasu kaya, to ko ba ta
son ka za ta riƙe ka a matsayin wanda ke biya mata wasu buƙatu
nata. Ana amfani da wannan kirarin ne wurin wanda ya faye son banza, wato a ba
shi a ba shi kullum, ba shi da wata moriya ga jama’a.
5. Abin na yi ne, an biya wa
bazawara hajji
Wannan karin magana tana nuna
cewa akwai alamar kawo ƙarshen zaman zawarci da kuma shiga a cikin sabuwar rayuwar
aure, kasancewar an biya mata hajji. Hajji babbar ibada ce wadda ake kashe kuɗi da yawa wurin yin ta,
saboda haka sai babban masoyi na gaskiya ne kawai yake biya wa mutum ibadar
Hajji.
6. Daga baya ke nan, an yi sadaka
da bazawara
Wannan karin magana tana nuna
cewa an makara ƙwarai da aka yi sadaka da bazawara. Ga al’ada ana bayar da mace
sadaka ne tun tana budurwa ta fuskar aure. Ana amfani da wannan karin magana
wajen mayar da martani ga duk wanda ya yi wani abu, bayan lokacin da ya dace ya
yi shi ya wuce, domin a nuna masa cewa ya makara da bai yi abin cikin lokaci
ba.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.