Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Kamar yadda aka kawo bayani a sama, gwauro da bazawara, wasu mutane ne waɗanda ke zaune a cikin al’umma ba tare da aure ba. Sun taɓa yin aure, auren ya mutu sanadiyar rabuwa ko mutuwar ɗaya daga ciki (mutuwar miji idan bazawara ce, sannan mutuwar mata idan gwauro ne). Haka kuma, suna zaman cin gashin kansu. Su ne suke yi wa kansu lalura ta yau da kullum saboda ba sa ƙarƙashin kulawar kowa.
A sama an ga misalan karin magana da suka shafi gwauro da
bazawara a keɓance. A wannan gaɓar kuwa, za a kawo misalan waɗanda
suka ƙunshi gwauro da bazawara a cikin
furuci guda. Wannan yana nuni ga alaƙarsu
bisa mahangar falsafar al’adun Hausawa. Ga misalai a ƙasa:
1. Aikin banza, karen gwauro ya kori bazawara
Ɗaya
daga cikin manyan dalilan ajiye kare a gida shi ne gadi. Yakan kori waɗanda suka zo gidan domin aikata ɓarna, kamar yara ko ɓarayi. Wani lokaci kuma yakan yi
haushi domin ya fargar da masu gidan cewa ga wasu baƙin da ba su saba zuwa ba sun zo.
A bangare ɗaya kuwa, gwauro ba shi da burin
da ya wuce yin zance da mace. Yayin da karen gauro ya kori bazawara, lallai ne
an yi aikin banza. Wannan ne ya sa ake amfani da karin maganar domin nuna wani
aikin banza da aka aikata. Ga misali a ƙasa:
Laraba: Sanata Larai ta ce ta fahimci
kuskurenta. Idan aka sake zaɓen ta, za ta yi aiki tuƙuru bisa adalci da riƙon amana.
Kuluwa: Aikin banza, karen
gwauro ya kori
bazawara!
2. Da rashin sani, karen gwauro ya kori bazawara
Tubalan da aka gida karin maganar da aka kawo a sama, da
irinsu aka gina wannan karin maganar. Bambancinsu kawai shi ne, wannan karin
magana yana nuni ne da da-na-sani ko aikata wani aiki bisa rashin sani – kamar
dai yadda karen gwauro ya kori bazawara a bisa rashin sani. Da a ce karen ya
san bazawara abin nema ce ga gwauro, lallai ba zai kore ta ba.
Ana amfani da wannan karin maganar domin yin tsokaci game da
wani lamari da ya haifar da da-na-sani, ko wanda aka aikata a cikin rashin
sani. Misali:
Audu: Ina ta jiran yaron da aka aiko,
har yanzu bai zo ba.
Lado: Ah, ba Musa kake nufi ba? Shi ne
fa ya wuce ta nan da abokinsa Iliyasu. Sun ce kai ne ka ce su koma gida.
Audu: Allah mai iko! Lallai yaran sun
tsaya a can suna hayaniya, ni kuwa na ce su yi gida. Rashin sani, karen gwauro
ya kori bazawara.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.