Ticker

6/recent/ticker-posts

Dagacin Shinkafi Wato Magajin Shinkafi Ibrahim II

Dagacin Shinkafi wato Magajin Shinkafi Ibrahim II
Jagora:

Na taho yima barka da zuwa Hausa,

Naji labarin

Jagora /Y/amshi:

Wada kaw wa maza kamak kwanakki,

Madogara na Malan,

Iro uban Bawa maigida Shinkahi

Jagora:

Riƙa da gaskiya Ibrafin,

Mai taimakonka Allah na nan

Jagora /Y/amshi:

Zan kawa maza gurnani,

Madogara na Malan,

Iro uban Bawa maigida Shinkahi

Jagora:

Mai kamak ka Ibrafin,

Kaga ya sha hura da nono kundum,

Yaci tuwo da nama,

Ga sutura gashi had da doki ɗamre,

Yab biye mutanen zamani sun ka kai shi hanyaɓ ɓanna

Jagora /Y/amshi:

Ga iggiyar ruwa sun ka bash shi,

Yau gashi nan da ragga cinjim,

Dole sai ya sha rummaye,

Madogara na Malan,

Iro uban Bawa maigida Shinkahi.

An samo waɗannan batutuwa ne☝️☝️daga cikin waƙar Makaɗa Alh. (Dr.) Ibrahim Narambaɗa Tubali wadda ya yiwa Marigayi mai girma Dagacin Shinkafi wato Magajin Shinkafi Ibrahim II (wanda yake kira da Ibrahimu na Guraguri) mai amshi "Madogara na Malan, Iro uban Bawa mai gida Shinkahi".

Ya yi masa wannan waƙa a ƙarshe ƙarshen 1950s (Ibrahim II ya yi sarauta daga shekarar 1950 zuwa rasuwarsa a shekarar 1990).

Wato wata waƙi'a ce ta faru a lokacin, aka kai ƙarar Magaji Ibrahim II a Isa inda Uban Ƙasa/Hakimin Gundumar dake duba Shinkafi da zummar a cire shi. Wasa-wasa magana tayi tsauri har zuwa majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi a Sakkwato. Bayan dogon bincike aka wanke Magaji Ibrahim II ya dawo ya ci gaba da mulkinsa.

"Na taho yi ma barka da zuwa Hausa, naji labarin wada kaw wa maza kamak kwanakki" inji Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali. Wato tunda an wanke shi kuma ya dawo gida lafiya daga Sakkwato ( ita yake kira Hausa) inda aka kai shi ƙara to ya zo ya yi masa barka da zuwa. A cikin wannan ɗiyan waƙa ya nuna ba wannan ne karo na farko da ake ƙullawa Ibrahim II irin wannan makirci ba kuma a kowane lokaci sai Allah ya kuɓutar dashi, " Naji labarin wada kaw wa maza kamak kwanakki" kenan ko a wasu kwanuka a can baya an yi masa irin wannan ƙullalliya amma ya fito lafiya.

A cikin waƙar dai ya ci gaba da bayyana yadda zamantakewar fada da mutanen fada da kuma mu'amalar jama'a take. Masu biyayya ga Sarki suna cikin ni'ima da wadata da kwanciyar hankali, daga baya sai wasu masu neman tayar da zaune tsaye su shiga su fita saboda su haddasa husuma a tsakanin Sarki da yan uwansa da sauran jama'arsa.

Shi ne Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ke cewa "Mai kamak Ibrafin kaga ya sha hura da nono kundum, ya ci tuwo da nama ga sutura, gashi had doki ɗamre, yab biye mutanen zamani sun ka kai shi hanyaɓ ɓanna.. Kenan ya na nufin jagoran wannan lamari zuwa Isa da Sakkwato a can baya yana biye da Magaji Ibrahim II kai da ƙafa, bai kuma rasa komai ba sai shukara amma daga baya ya fara ɗaukar shawarwari daga mutanen da basu ƙaunar a zauna lafiya. Bayan ya ɗauki maganganunsu to bai samu nasara akan Magaji ba, "Ga iggiyar ruwa sun ka bash shi, yau ga shi nan da ragga cinjim dole sai ya sha rummaye" inji Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali. Sun iza shi sun gaza fitar dashi, ya janyowa kansa matsala, babu sutura babu kwanciyar hankali babu abinci mai kyau sai dafaffen ganyen tafasa ko zogale a cikin gumbar hatsi /gero (shi ne rummaye /rummace) tare da tsumma/tsummokara a matsayin suturarsa (sune yake kira ragga).

Ya nunawa Magaji Ibrahim II muhimmanci zama namijin tsaye a sha'anin mulki da kuma gaskata Allah SWT "Riƙa da gaskiya Ibrafin mai taimakonka Allah na nan, zan kawa maza gurnani" (gurnani shi ne irin wada Zaki ko Damisa ko Kura ke furta wasu alamomi daga bakunansu saboda su tsorata sauran dabbobi).

Makaɗan baka na Hausa musamman na fada/sarauta suna da hanyoyi masu dama dasu ake amfani dasu wajen taskace wasu muhimamman abubuwa da suka faru a cikin al'umma, wani lokaci su bayyana su ƙarara a cikin waƙoƙinsu a wasu lokuta kuma su sakaya. Ala kulli halin dai suna biye /suna sane da faruwar manya da ƙananan al'amurra a fadoji/masarautun da suke mu'amala dasu kamar dai yadda a waɗannan ɗiyan waƙa Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya taskace muna wannan waƙi'a.

Magaji Ibrahim II shi ne Dagacin Shinkafi na 10 tun daga maƙirƙirin gidan sarautar na farko wato Muhammadun Badarawa da ya yi mulki daga 1751 zuwa 1821 da hedikwata a Badarawa.

Ibrahim II ɗan Magaji Dango ne wanda shi ne Dagaci na 8 daga 1919 - 1939. Shi kuma ɗan Malam Abubakar ne shi kuma ɗan Magaji Umaru ne Dagaci na 5 da ya yi sarauta daga shekarar 1883-1890, shi kuma ɗan Magaji Muhammadu Sanusi ne wato Dagaci na 3 da ya yi mulki daga shekarar 1884 zuwa 1852, shi kuma ɗan Malam Muhammadun Badarawa ne wato ma'assasin gidan da ya yi mulki daga 1751 zuwa 1821.

Bayan wafatinsa a shekarar 1821 ɗansa (ɗan uwa Magaji Muhammadu Sanusi) da ake kira Malam Muhamman Bello ne ya gaje/gade shi har zuwa 1844.

Turawan mulkin mallaka ne suka ƙarfafa dawowar hedikwatar mulki daga Badarawa zuwa Shinkafi a lokacin mulkin Magaji Ahmadu Lamiɗo Dagaci na 9 da ya yi sarauta daga shekarar 1939 zuwa 1950.

Shinkafi ta ci gaba da kasancewa garin Dagaci a ƙarƙashin gundumar Isa, Jihar Sakkwato har zuwa ƙirƙiro Jihar Zamfara daga Tsohuwar Jihar Sakkwato a shekarar 1996 lokacin da aka ciro ta daga gundumar Isa, Jihar Sakkwato zuwa Jihar Zamfara aka ɗaukaka darajar ta zuwa gunduma da kuma hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Shinkafi a Jihar Zamfara. A halin yanzu Shinkafi masarauta ce da Sarki mai daraja ta biyu a Jihar Zamfara da laƙabin Sarkin Gabas.

Mai martaba Alh. Muhammad Makwashi Isah ne ke rike da wannan sarauta ta Sarkin Gabas Shinkafi daga gidan sarauta na Malam Muhamman Bello ɗan Malam Muhammadun Badarawa. Allah ya ƙarawa mai martaba Sarki lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

Wannan hoto marigayi mai girma Dagacin Shinkafi na 10 ne, wato Alhaji Ibrahim II wanda a cikin waƙar da Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya yi masa ne muka ciro batutuwan da muka yi sharhi akan su.

Allah SWT ya jaddadawa dukan magabatanmu rahama ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Fiyayyen Halitta Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

Daga alƙalamin:

Hon. Dr. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.

25/07/2026.

Post a Comment

0 Comments