Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Fati Nijar (Hajiya Binta Labaran)

An ciro daga littafin:

FASIHIYA BINTA LABARAN
Fati Nijar Da Waƙoƙinta

Na

Abu-Ubaida Sani
Halima Daura Kabir
Abdullahi Bashir

Manazarta

Sani, A-U., Kabir, H.D., & Bashir, A. (2024). Fasihiya Binta Labaran (Fati Nijar Da Waƙoƙinta). SAS Publishers. ISBN: 978-978-795-635-7. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513195

Fasihiya Binta Labaran (Fati Nijar Da Waƙoƙinta)







Tarihin Fati Nijar (Hajiya Binta Labaran)

1.0 Shimfiɗa

Tattara waƙoƙin fitacciyar mawaƙiya kamar Fati Nijar ba zai samu cikakken armashi ba har sai an haɗa da tarihin rayuwarta. Makaranta da manazarta da dama za su so jin tarihin mutane irinta. Bugu da ƙari, tarihin zai kasance wata makaranta ga masu karatu. Masu karatu sukan iya cin karo da bayanai ko salailan rayuwa da za su kwaikwaya a wani mataki na neman cigaba a rayuwa.

Shi kuwa tarihin Fati Nijar za a iya kallon sa ta fuskoki guda biyu. Wannan ya shafi rayuwarta kafin ta fara waƙa a ɓangare guda, da kuma rayuwarta a matsayin mawaƙiya a ɗaya ɓangaren. Tussan bayanai na farko da wannan bincike ya dogara a kansa shi ne “Waƙa a bakin mai ita.” Kayan manazartan sun tsinke a gindin kaba inda suka shafe tsawon watanni suna tattaunawa da wadda ake rubutun a kanta a-kai-a-kai. Bayan nan, an nazarci waɗansu ayyuka da aka gabatar a kan mawaƙiyar a matakin ilimi daban-daban. Sun haɗa da kundayen digiri da maƙalu da littattafai daban daban. A nan, za mu bi matakan ilimi na nazarin ƙwaƙƙwafi domin tabbatar da ingancin bayanan da aka tattaro.

1.1 Taliyon Tsatson Hajiya Fati Nijar

Hausawa suna cewa “In ka ji wane ba banza ba.” Lallai wannan batu haka yake. Ɗaukakar Hajiya Fati Nijar abu ne da za a iya cin samun salsalarsa a cikin tarihin rayuwarta. Wannan kuwa ya fara ne tun daga kakanninta. Tarihin kakannin Fati yana cike da rayuwar malanta da fasaha da jajircewa tare da aiki tuƙuru. An dai kuwa san da cewa, “Barewa ba ta gudu ‘yarta ta yi rarrafe.” A taƙaice dai albasa ce ta yi halin ruwa. Za a bi diddigin tarihin kakannin Fati ta ɓangarori biyu: ɓangaren mahaifiya da ɓangaren mahaifi.

Fati ta fi sanin tarihin kakanninta na ɓangaren mahaifiya. Dalili kuwa shi ne, ta yi rayuwa tare da mahaifiyar tata. Wannan ne ya ba ta damar samun labarai da dama game da kakanninta ta wannan tsatso. A ɓangare ɗaya kuwa, ba ta san kakanninta na ɓangaren mahaifi sosai ba, duk da cewa ta san su a suna.

1.1.2 Kakannin Fati Nijar Na Ɓangaren Mahaifi

Kamar yadda aka bayyana a sama (ƙarƙashin 1.1), Fati ta fi samun bayanai game da kakanninta na ɓangaren mahaifiya. Duk da haka, da farko ta fi sanin sunayen kakanninta na ɓangaren mahaifi. Sunan kakan mahaifin Fati Nijar Muhammad. Sunan babansa kuma Ibrahim. Mahaifin nata kuwa sunansa Abdurrahman. Ke nan Muhammad ya haifi Ibrahim, Ibrahim ya haifi Abdurrahman, mahaifin Fati. Ga yadda abin yake:

Giraf 1.1 Kakannin Fati Nijar Na Ɓangaren Mahaifinta

Kakannin Fati Nijar Na Ɓangaren Mahaifinta

Madogora: Tattaunawa da Hajiya Fati Nijar (an tantance bayanai).

A ɓangaren mahaifi, zuriyar Fati Nijar ‘yan asalin jihar Barno ne da ke arewa maso gabashin Nijeriya. Sai dai wani hanzari ba gudu ba shi ne, tarihi bai fayyace ko kakan mahaifin Fati da ma ɗan asalin Borno ne ko kuma sun taso ne daga wani wuri daban ba. Ke nan a wannan ɓangaren, taliyon tarihin Fati zai tsaya ne a Borno.

“Babana ya faɗa mana cewa, shi ya san kakansa Muhammad. Ya ce fari ne sosai. Wannan ne ma ya bar mana alamar tambayar cewa, anya kuwa su asalin ‘yan Borno ne, ba daga wani wuri suka taho ba?” (Fati Abdurrahman, 2021}.

Daga Borno ne Malam Muhammad ya tafi Nijar wurin neman karatu. A can Nijar ne kuma ya sake kafa wata sabuwar zuriya. A can ya haifi Malam Ibrahim, shi kuwa Malam Ibrahim ya haifi mahaifin Fati wato Malam Abdurrahman (Labaran). Kakannin Fati ta ɓangaren mahaifinta malamai ne. Hasali ma neman ilimi ne ya baro kakan babanta daga Barno zuwa ƙasar Nijar.

1.1.2.2 Malam Muhammad (Baban Kakan Fati Nijar)

A nan, ba a samu bayanai masu yawa ba dangane da rayuwar Malam Muhammad. Wannan ya faru ne sakamakon tsawon lokaci a bagiren tarihi da kuma rashin kundataccen bayani game da rayuwarsa. Muhimman abubuwa da za a iya tunawa game da Malam Muhammadu su ne:

1. Shi fari ne

2. Ya taso ne daga Barno zuwa Nijar saboda neman ilimi

3. Shi Malami ne

4. Shi ne mahaifin Malam Ibrahim (Kakan Fati Nijar)

1.1.2.3 Malam Ibrahim (Kakan Fati Nijar)

Shi ma Malam Ibrahim ba a samu bayanai masu yawa game da rayuwarsa ba. Ya tabbata cewa, Malam Ibrahim manomi ne. Noma ne sana’ar da ya dogara da ita wajen rayuwa da ci da iyalansa. Sunan matarsa Aljima.

1.1.2.4 Iyayen Hajiya Fati Nijar

Sunan mahaifiyar Fati Nijar A’ishatu, amma an fi saninta da Amma. Sunan mahaifin Amma Hassan. Sunan kakanta kuwa Tanko.

A ɓangare ɗaya kuwa, mahaifin Fati shi ne Malam Abdurrahman. Shi kuwa an fi sanin sa da suna Labaran. Wannan inkiya tasa ta yi tasiri matuƙa yadda har sunansa na asali ya ɓace. Hakan ne ma ya sa ake kiran ta da suna Fatima Binta Labaran. Ba kowa ne ya san asalin sunan mahaifin nata ba.

Iyayen Fati Nijar sun zauna a garin Madawa. Wannan gari ne da ke Jahar Tawa a Jamhuriyar Nijar. Mahaifinta ya kasance ɗan kasuwa. Kasuwancinsa ya ta’allaƙa a kan zuwa cin manya da ƙananan kasuwanni na kusa da na nesa. Sun haɗa da kasuwannin garuruwa da na ƙauyuka. Bayan kasuwannin da yake ci a cikin ƙasar Nijar, kuma yakan fita har maƙwabtan ƙasashe irin su Nijeriya da Chadi da sauransu.

1.1.2.5 Haihuwar Hajiya Fati

An haifi Fati Nijar ne a garin Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan gari shi ne na biyu a girma a illahirin ƙasar. An haife ta ranar Talata 26 ga watan Janairu na shekarar 1988. Fati tana da ‘yan uwa guda biyar kamar haka:

i. Saudatu

ii. Usman

iii. Ibrahim

iv. Isah

v. Musa

A taƙaice ke nan, ana iya kallon tarihin Fati Nijar cikin taswirar bishiyar da ke ƙasa:

Tarihin Fati Nijar

1.1.2.6 Sunanta da Laƙabinta

Sunan Fati Nijar na asali shi ne Fatima. Ana yi mata laƙabi da Binta Labaran sakamakon inkiyar mahaifinta wato Labaran. Ma’ana ke nan, akan kira ta da ‘Yar Labaran a Hausance.

A ɓangare ɗaya kuwa, fitaccen laƙabinta shi ne Fati Nijar. Abin lura a nan shi ne, wannan laƙabi ba na ƙuruciya ne ba. Domin kuwa bai samu ba har sai da ta shigo Nijeriya har ta fara hulɗa da mutane. Wannan laƙabi da shi aka fi sanin ta. Kuma shi ne sunanta wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta da duniyar intanet baki ɗaya. Manyan dalilai biyu ne suka samar da wannan laƙabi gare ta. Su ne:

1. Fati ‘yar Nijar ce. Daga Jamhuriyar Nijar ta shigo Nijeriya. Don haka, wannan ba abin mamaki ne ba a yayin da aka ambaci mutum da ƙasarsa ta asali.

2. Fati Nijar ta bayyana cewa, a lokacin da ta fara hulɗa da masu harkar finafinai da waƙoƙi a Nijeriya, ba ita kaɗai ce mai suna Fati ba. Domin rarrabewa, shi ne akan yi mata inkiya da Fati Nijar. Wato tamkar dai wannan laƙabi ya samo asali ne yayin da abokai ko ƙawaye da abokan aiki sukan alaƙanta ta da ƙasarta ta asali domin bambance sunanta daga sunan sauran ƙawayenta.

Fati da kanta ta bayyana sunanta da laƙabinta a cikin wata waƙarta mai suna So Yanayi. Ta ce:

Ehhh Binta Labaran Mulaƙƙabu kuma sunana,
Fati Nijar wasu jama’ar ke ta kira na,
Na yi jinjina gare ku dukka masoyona,
Na gaishe ku Abubakar Sani da Yayana ALA.

1.1.2.7 Tasowarta

Kamar yadda Fati ta bayyana wa Bashir, da wasu (2010 p. 5), ta faro yaruntarta ne a garin Maraɗi na Jamhuriyar Nijar. Bayan wani lokaci ne kuma suka koma ƙauyen Wurno da zama. A inda a wannan ƙauye ne ta taso har ta yi wayo.

A lokacin yaruntarta, ta kasance mai sha’awar wasan kayan taɓo. Hakan ba ya rasa nasaba da kasancewar sun taso kusa da rafi. A wancan lokaci, ta nuna baiwar fasahar hannu. Ya kai ga har tana iya haɗa abubuwan aikace-aikacen gida daban-daban ta hanyar yin amfani da taɓo. Sun haɗa da:

a. Kasko

b. Tanda

c. Tukunya (tukunyar ƙasa)

d. Tulu

Ko bayan waɗannan, ta iya sarrafa taɓo/laka domin samar da kayayyakin wasa ta sigar mutum-mutumin namun daji. Sun haɗa da:

a. Akuya

b. Giwa

c. Raƙumi

d. Sa

Wani babi a rayuwar ƙuruciyar Fati shi ne zuwa daji domin kamo fari tare da sauran yara. Ta kasance sha-aike sakamakon ba ta da ƙiuya. Bayan haka, ita ba mai son yawan faɗa ce ba.

Baiwa da ilhamar waƙa da Ubangiji ya bai wa Fati ya sa tun tana ƙarama ta fara fuskantar ƙyashi da hassada daga saointa. Takan yi zarra sosai a lokutan waƙoƙin wasannin dandali. Wannan ya haɗa da abin da ya shafi zaɓin murya da iya rerawa da kuma kawo ɗiyan waƙoƙi daidai.

Tun tasowarta take sha’awar waƙoƙin dandali. Ta bayyana cewa, tun tana ƙarama take rera waƙoƙi a gaban yan wasa yayin kaɗe-kaɗen gargajiya. Sannu a hankali har ta fara fice sakamakon zarra da ta yi a fagen zaƙin murya a cikin tsara. Abin ya kai har mutane suna shaawar ya kasance ita ce za ta rera waƙoƙi yayin kaɗe-kaɗen gargajiya a ƙauyen.

1.1.2.8 Karatunta

Binta Labaran ta fara karatun allo tun tana ƙarama. Ta kasance mai ƙwazo matuƙa. A mafi yawan lokuta akan riga yi mata ƙari kafin sauran abokan karatunta. Wannan yana faruwa ne kasancewar takan riga su saurin hardace karatun da aka ba ta. Ta dage sosai a wannan turba inda har ta samu izu/hizufi talatin (30).

A lokacin da suke wannan karatu, sun rinƙa halartar tarukan sauƙan karatun Alƙurani na sauran ɗalibai. Bayan haka, sukan halarci tarukan Maulidi daban-daban. A wurin waɗannan taruka, sukan karanta abin da ya sauwaƙa musu daga Alƙurani, kamar dai yadda lamarin yake gudana a wurin tarukan Maulidi a yau.

1.2 Naɗewa

Kamar yadda a mafi yawan lokuta waƙa baiwa ce da ilhama da Ubangiji ke bai wa waɗanda ya so, haka abin ya kasance ga Binta Labaran. Za a iya lura da hakan yayin da aka bibiyi yadda rayuwarta takasance tun farko, wato yadda ta taso da zalaƙa da zaƙin murya sannan ta yi fintinkau a wannan fage tun lokacin yarunta. A wannan babi an ga tarihin Fati a taƙaice, musamman abin da ya shafi taliyon asali, da haihuwa da kuma tasowarta. A babi na gaba, za a dubi lamarin waƙarta da ɗaukakarta a wannan fage.

Post a Comment

0 Comments