Ticker

6/recent/ticker-posts

Daukakar Hajiya Fati Nijar a Duniyar Waka

An ciro daga littafin:

FASIHIYA BINTA LABARAN
Fati Nijar Da Waƙoƙinta

Na

Abu-Ubaida Sani
Halima Daura Kabir
Abdullahi Bashir

Manazarta

Sani, A-U., Kabir, H.D., & Bashir, A. (2024). Fasihiya Binta Labaran (Fati Nijar Da Waƙoƙinta). SAS Publishers. ISBN: 978-978-795-635-7. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513195

Fasihiya Binta Labaran (Fati Nijar Da Waƙoƙinta)






 

IN KA JI WANE... ƊAUKAKAR HAJIYA FATI NIJAR A DUNIYAR WAƘA

2.0 Shimfiɗa

Kawo tarihi tiryan-tiryan abu ne mai matuƙar wahala musamman idan ba a riga an kundace shi yayin da abubuwan ke faruwa ba. Wahalarsa na ƙaruwa yayin da ya kasance ya shafi wanda ke da ɗawainiyoyin rayuwa masu tarin yawa tare da hulɗa da mutane daban-daban kamar dai yadda lamarin yake ga Binta Labaran. Duk da haka, wannan babi ya yi bakin ƙoƙari wajen kalato muhimman bayanai da suka shafi ɗaukakar Hajiya Fati a duniyar waƙa.

2.1 Fara Waƙar Fati Nijar

Waƙa ita ce sana’a ta farko da Binta Labaran ta fara. Kafin fara waƙarta, ba ta da wata sanaa takamaimai da take yi. A maimakon haka, ta duƙufa ne kawai kan karatun addini, musamman na Alƙurani mai tsarki. Rungumar sanaar waƙa da ta yi ya zo mata da babbar riba. Domin kuwa, tuni ta biya Haji inda ta sauke farali. Haka kuma, ta biya wa iyayenta. Ko bayan nan, wannan sanaa ta ba ta damar mallakar gidaje da motoci kamar yadda Bashir, da wasu (2010 p. 8) suka bayyana.

Hajiya Fati ba ta gaji waƙa ba. Ta taso ne kawai da baiwarta. Da yake kuwa ta kasance hanyar cin abinci gare ta, sai ta faɗa cikinta gadan-daban. A taƙaice ke nan, ta fara waƙa cikin yanayin da Gusau (2008) ya bayyana da ɗabi’a, wato fara waƙa ba tare da gado a wurin wani ko naƙalta ta hanyar bin ubangida ba.

2.2 Waƙoƙinta na Farko

A farko Fati Nijar ba waƙoƙinta na kanta take rerawa ba. Ta fara ne da rera waƙoƙin finafinai da akan buƙaci ta tsara. Maana, akan ba ta tsari da salon da ake buƙatar waƙoƙin su kasance, daidai da labarin fim ɗin da waƙar za ta fito a cikinsa. Waƙar da ta fara rerawa a wannan tsari tana da suna Al’amarin Hassan Yana Bam Mamaki.

Daga baya Hajiya Fati ta bunƙasa sanaar ta hanyar rera waƙoƙinta masu cin gashin kansu. Ire-iren waƙoƙin nan takan yi su ne bisa yadda take so sannan ta tallata su. Na farko-farko a wannan tsari su ne:

a. Girma-Girma

b. ‘Yan Matan Arewa

Ta buɗe waƙar Girma-Girma da bayanin kanta inda take cewa:

Na yi godiya a gare ku masoyana,

Girma girma Allahu Shi ne mai girma,

Mu riƙe amana da kwaikwayon halin Manzon Allah.

 

Ehhh Binta Labaran Mulanƙabun kuma sunana,

Fati Nijar wasu jama’ar ke ta kira na,

Na yi jinjina gare ku dukka masoyana,

Na gaishe ku Abubakar Sani da yayana ALA.

A cikin waɗannan baituka biyu, ana iya ganin nason tasirin karatunta na allo. Kuma ta bayyana sunan da aka fi sanin ta da shi kafin laƙabinta ya dusashe shi, wato Binta Labaran. Daga bisani kuma ta bayana laƙabin da ake yi mata na Fati Nijar. Wani abin da za a ƙara tsinta a cikin waƙar shi ne, tsohuwar tarayyar zamantakewa (ta fuskar sanaa) da take da shi da Aminu Ladan Abubakar (ALA) inda har ta kira shi da yayanta.

Ko bayan wannan, akwai waƙoƙinta na farko-farko da ke nuni da nason karatun Muhammadiyya da zabiyar ta muamalantu da shi. Daga cikin ire-iren waƙoƙin akwai waƙar Ɗan Amina Fiyayye. A cikin waƙar tana cewa:

Amshi: Ya Rasulullah, Ya Rasulullah,

Ɗan Amina fiyayye a gai da kai manzona.

 

Na kirayi maƙagi na ruhu da fuskata,

Masanin sirrina ka amsan buƙatata,

Taimako zan nema gare ka Sarkin kyauta,

Ka zama ban basira in yabo gurin manzona.

 

Ƙaro dubu na salati gurin manzona,

Almustafa Muhammadu Ɗaha uban Nana,

Wannan da shi na riƙa madogarar begena,

Ɗan Aminatu gaishe ka Musɗafa manzona.

 

A cikin salatin Yaa Rabbi mai girma,

Roƙo nake ka haɗa har ahalin mai girma,

Tsatso ga Faɗima Binta Zahara ‘yar mai girma,

Kamar Hassan da Hussaini ‘ya’yan manzona.

 

A cikin sahabu Rasulu su ma ba zan yar ba,

Domin ko sun yi rawar gani gun sa ɗan babba,

Sun taimaka wa Rasulu a dalilin Rabba,

Jinjina nai maku manya-manyan masoyana.

 

A yanzu zan koma in yo yabon manzona,

Domin ko shi na riƙe ya zam abin cetona,

Ya zamo sutura a gare ni ni da dangina,

Allah ya ƙaran ƙaunar Rasulu manzona.

 

Ya Rasulu Manzon tsira yabonka naƙ ƙaga,

Shugaban duniya riƙe da hannun dama,

In kai riƙo a gare ni wallahi na girma,

Ɗaha ka dafa min Almukhtari manzona.

Wata hanyar samun kuɗi daga waƙa ga Fati Nijar ita ce talla. Wato kamar dai sauran fitattun mawaƙa, tana iya yin waƙa domin tallata wata haja. Wata daɗaɗɗiyar waƙar talla da Binta Labaran ta yi ita ce ta G. Cell. Ta yi wannan waƙar a kamfanin sadarwa na G. Cell a farko-farkon shigowar kamfanin (wajen 2001). A wani baitin waƙar tana cewa:

G Cell na kowa ne an yo shi don karkara da birane,

Ga sabuwar hanyar sadarwa karkara da gari,

Ga wacce ke tace iska mai sada albishiri,

G Cell yanzu yana a jiha uku mun yi alƙawari,

Sai mun haɗe da ƙasa domin G Cell na kowane ne.

2.3 Ɗaukaka Da Ficen Fati a Fagen Waƙa

Binta Labaran na cikin rukunin mawaƙan zamani. Masana ba su kai matsaya a kan takamaiman sunan da ya dace a kira nau’in waƙoƙinsu ba. Wannan ya sa ake kiran su da sunaye daban-daban. Daga ciki akwai:

a. Waƙoƙin zamani

b. Waƙoƙin baka na zamani

c. Ruwa biyu[1]

d. Jemagun waƙoƙi

e. Waƙoƙin situdiyo

Ko ma dai yaya abin yake, waɗannan waƙoƙi sun cancanci a kira su na zamani. Zamani ne ya zo da su. Kayan kiɗan situdiyo ararru ne daga baƙin alummu, musamman Turawa. A taƙaice ke nan, ana iya cewa Binta Labaran mawaƙiyar zamani ce. Waƙoƙinta kuwa, ana iya kiran su waƙoƙin zamani.

Fati ta yi suna sosai a duniyar waƙa. Sunanta ya watsu a lungunan ƙasar Hausa. Ta kuma kasance abin kwatance da kwaikwayo tsakanin mata matasa da dama. Yadda take gudanar da ayyukan kiɗa da waƙa tare da sauran mawaƙa na nuni ga irin zaman lafiya da lumana da ke tsakaninsu. Wani babban misali shi ne yadda suke waƙar haɗaka (ɗani) da waɗansu mawaƙan na daban. Daga cikin ire-iren waƙoƙin ɗani da ta yi akwai na siyasa da kuma na ta’aziyyar Ɗanmaraya Jos.

Tarin waƙoƙin da ta yi na ƙara nuni da bunƙasar fasaharta a fagen waƙa. Ta kasance wadda ake girmamawa a tsakanin mawaƙa.

2.4 Ƙalubale a Cikin Gwagwarmayar Rayuwar Fati

Kamar yadda aka bayyana a ƙarƙashin 1.2.5 da ke sama, Fati Nijar ta fara fuskantar ƙalubalen rayuwa ne tun lokacin ƙuruciyarta. Ƙalubale na farko shi ne mayar da ita da aka yi sha-aike kasancewar ba ta da ƙiuya. Daga nan kuma sai ta fara fuskantar ƙalubalen hassada da kishi sakamakon baiwar waƙa da Allah ya ba ta.

Wani babin ƙalubale da Fati Nijar ta fuskanta shi ne gwagwarmayar rayuwa a Nijeriya. Ya kasance sabon muhalli a gare ta. Da taimakon Ubangiji, ta gina sabuwar rayuwa tare da yin sababbin abokan arziki da abokan aiki.

A ɓangare ɗaya kuwa, sanannen abu ne a ƙasar Hausa cewa dukkannin mawaƙa da masu harkar finafinai na fuskantar ƙalubalen tsangwama da zargi. Wannan ƙalubale ya fi yawa ga mata. Ya haɗa da kuɗin goro da ake yi musu a matsayin masu fanɗare wa koyarwar addini da al’ada.

Tarin ƙalubale da Fati Nijar ta fuskanta bai sa ta yi ƙasa a guiwa ba. Domin kuwa, ta ci gaba da fafutukar tabbatar da mafarkinta. Sannu a hankali har ta yi fice, ta yi suna sosai a tsakanin mawaƙa. Har ta kai da cewa amon sunanta ya zagaya ƙasar Hausa da zaurukan sada zumunta a kafafen intanet.

2.5 Naɗewa

Lallai “Idan ka ji wane ba banza ba.” Binta Labaran ta biyo waɗansu matakan rayuwa da ke tattare da zaƙaƙuranci da fasaha. Ta sha gwagwarmayar rayuwa inda har ta baro ƙasarta ta haihuwa ɗungurungun ta dawo Nijeriya da zama. Game da ƙalubalen rayuwa da ta fuskanta kuwa, lallai za a iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu.



[1] A duba Usman, (2018).

Post a Comment

0 Comments