Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunayen Mutuntawa/Girmamawa a Sunayen Kanuri (Barebari)

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Al’ummar Kanuri (Barebari) sun shahara wajen girmama na gabansu (manyan), waɗanda da suka ƙunshi tsofaffi da masana da shugabannin al’umma. Sakamakon haka ne suke gabatar da kalmar Baa ga dukkan sunayen magabata maza. Kalmar tana ɗauke da ma’anar Baba. Yayin da suke gabatar da kalmar Ya ga sunayen mata, wadda take nufin Inna ba tare da la’akari da shekarun wanda ake kira ba, kamar yadda Waziri (2000 p. 23) ya bayyana.

Ita kuwa kalmar Yaa takan gabaci (kan zo kafin) sunan wa ko yaya ko kaka da ke nufin mahaifiyar uwa ko uba. A bisa wannan tarbiyyar ce, mai suna Garba sai ƙaninsa ya kira shi da Yaa Garba. Yayin da sa’ar (tsarar) ‘ya’yansa za su kira shi da Baa Garba. Baba Garba ke nan. Su kuwa tsarar jikokinsa su ce Kaka Garba.

Ta fuskar mata kuwa, ga misali, mai suna Aisa sukan kira ta da Yaa Aisa ko Kaka Aisa tamkar yadda akan ambaci namiji domin girmamawa. Sakamakon haka ne sai a wayi gari ya kasance mutum ya shahara da ɗafa-goshin da aka yi masa, wato sai a cigaba da ambatonsa/ta, da Baa ko Kaka ko Yaa.

A bisa tsarin tarbiyyar Kanuri (Barebari), ɗanyan baki ne (batsa ko rashin kunya) mutum ya kira mahaifinsa ko na wani ko na gaba da shi da ainahin tsagwaron sunansa. Sakamakon al’ada ta shata yadda za a rinƙa ambaton na gaba a bisa wannan tsarin:

Jad. na 25: Sunayen Mutuntawa/Girmamawa a Tsakanin Kanuri

 

Suna

Dangantaka

Kwatankwaci a Hausa

1.       

Baa ko Baba, ko Abbanyio

Mahaifi

Baba

2.       

Baa Kura

Wan mahaifi

Baffa ko baba babba

3.       

Awana

Ƙanen mahaifi

Baffa ko baba ƙarami

4.       

Bawa

‘Yar’uwa

‘Yar’uwa

5.       

Ya

Mahaifiya

Inna ko mama

6.       

Ina

Ƙanwar uwa

Inna

7.       

Ya Kura

‘Yar’wa

‘Yaruwa

8.       

Rawa

‘Yaruwar mahaifiya

Inna

Yayin da aka raɗa wa jinjiri sunan ɗaya daga cikin waɗannan dangin da aka ambata, girmamawar da ake yi masa tana naso a kansa (shafar sa). A sakamakon haka ne suke ɗafa-ƙeyar Gana (ƙarin kalmar Gana a ƙarshen kalmar) wadda ke ɗauke da ma’anar ƙarami. Don haka, idan aka sanya wa jinjiri sunan mahaifin uban yaron sai a dinga kiransa da Baba Gana ko Abbanyi Gana. A wasu lokutan akan ambace shi da Abatcha, kamar yadda aka bayyana a sama. Wasu kuwa kan yi amfani da Awuzu, ko Buchu ko kuma Mbatcha ba tare da ɗafa-ƙeyar Gana ba.

Waɗanda suka zana wa ‘ya’yansu sunayen mahaifiyarsu, a sakamakon laƙabin sukan kira su da: Yagana ko Yanyi Gana, wanda ke ɗauke da ma’anar ƙaramar uwa. Su kuwa waɗanda suka zana wa ‘ya’yansu sunayen kakanninsu, sukan kira su da: Kaka Gana ko Ƙyari (Dattijo) ga ɗa namiji, mace kuwa a kira ta: Ka’ana ko kuma Ƙumurso, kamar yadda Waziri (2000 p. 23) ya nuna.

Shigar giragizai da ya wanzu a tsakanin wannan al’umma da waccan ta fuskar al’adu da ɗabi’u sakamakon auratayya, wanda ya zama ruwan dare a tsakanin Kanuri da Shuwa-Arab. Ya haifar da nason sunaye a tsakaninsu. Inda har aka sami ɗauko wasu sunayen mutuntawa daga Shuwa-Arab. Misalai daga cikinsu sun haɗa da:

Jad. na 26: Sunayen Sakayawa a Tsakanin Kanuri

 

Sunan Girmamawa

Jinsi

Dangantaka

1.       

Abui ko Ab

Namiji

Takwaran sunan mahaifi (mai sunan mahaifi)

2.       

Ajus

Mace

Takwaran kaka mace (mai sunan kaka mace)

3.       

Ammui ko Inna

Mace

Takwaran mahaifiya (mai sunan mahaifiya)

4.       

Jidda ko Asheik

Namiji

Takwaran kaka namiji (mai sunan kaka namiji)

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments