Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Bunƙasar Sunaye a Al’ummar Kanuri
An sami bunƙasar sunaye a tsakanin al’ummar Kanuri (Barebari) sakamakon bayyanar addinin Musulunci da yadda suka karɓe shi, tun a zamanin rayuwar Sayyidina Abubakar Siddiƙu. Rungumar addinin Musuluncin da sarakunan al’ummar suka yi. Ya kawo sauyin rayuwa da zamantakewar al’umma da wayewar kai tare da kafuwar makarantun addinin Musulunci da bunƙasar su a faɗin masarautar. Sakamakon haka ne ya haifar da wanzuwar shigar wasu nau’o’in sunayen Musulunci a tsakanin al’ummar. Irin waɗannan sunaye sun haɗa da:
(i) Sunayen Allah MasuTsarki.
(ii) Sunayen Mala’ikun Allah.
(iii) Sunayen Annabawan Allah.
Irin waɗannan sunayen an cirato su ne daga cikin Alƙur’ani mai tsarki ko hadisan Annabi S. A. W. ko kuma daga cikin littattafan tauhidi.
Samar da Suna ta Amfani da Sunayen Allah Kyawawa
Al’ummar Kanuri kan yi amfani
da sunayen Allah kyawawa wajen raɗa wa ‘ya’yansu suna. Sukan yi haka ne ta hanyar yi wa sunayen ɗafa-goshin ƙwayar ma’anar. Misali, “Abdu” a farkon kalmar sunanyen Allah Kyawawa. Wasu daga cikin
irin waɗannan sunaye da suka tusgo daga cikin Alƙur’ani mai tsarki sun haɗa da:
Allah,
wanda aka ambata sau 2699.
Ar-Rahmaan, wanda
aka ambata sau 57.
Ar-Rahim, wanda
aka ambata sau 123.
Al-Ƙuddus,
wanda aka ambata sau
2.
As-Salam,
wanda aka ambata sau
1.
Al-Mu’min,
wanda aka ambata sau
1.
Al-Malik,
wanda aka ambata sau
5.
Al-Ƙaadir,
wanda aka ambata sau 12,
da sauransu.
Keɓaɓɓun sunayen da Kanuri suka fi shahara da su wajen raɗa wa
‘ya’yansu tare da ɗafa-goshi na Abdu mai ɗauke
da ma’anar “bawan” sun haɗa
da:
Jad. na 27: Sunayen Kanuri Daga Sunayen Allah
|
|
Asalin Suna |
Ma’ana |
Taƙaitawa |
Tsokaci |
|
1. |
Abdullahi |
Bawan
Allah |
Abdu ko Dala ko Dallai ko Buji |
Kalmomin Dala, da Dallai da Buji duk na harshen Kanuri ne da suke kiran
mai wannan sunan, kamar yadda Hausawa da Fulani suke kiran mai sunan “Maiboɗinga” ko “Maikano” ko
“Maigwandu” |
|
2. |
Abdur-Rahman |
Bawan
Mai-Rahama |
Ramanu |
Sukan kira mai sunan
da “Darman”.
|
|
3. |
Abdul-Ƙudus |
Bawan
Mai-Tsarki |
Gudus |
Ɗaiɗaikun mutane
ne ke amfani
da shi.
|
|
4. |
Abdus-Salam |
Bawan
Mai-Aminci |
|
|
|
5. |
Abdul-Muminu |
Bawan
Mai-Amintarwa |
Mumin |
|
|
6. |
Abdul-Ƙadir |
Bawan
Mai-Iko |
Ƙadi
ko Kadar |
|
Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 17)
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.