Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
A sakamakon aukuwar wasu lamura da ke zagaye da haihuwar mutum da suke haddasa a sanya wa abin haihuwa laƙabi a tsakanin al’umma. Wani zubin iyalin gida kan fuskanci annobar yawan mutuwar jarirai. A sakamakon haka akan bai wa jinjirin laƙabin da ke nuna yanayin da aka haife shi, domin babu tabbacin tsayawarsa (rayuwarsa). Galibi irin waɗannan laƙubban suna nuna shakkun ɗorewar rayuwar abin da aka haifa ɗin. Misalai daga cikinsu sun haɗa da:
Jad. na 24: Raɗa Sunayen
Kanuri ta La’akari da Aukuwar Abubuwa
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Amorja |
In
yaron na buƙatar ya rayu |
|
2. |
Gabchia |
In
yaron ya yarda ya tsaya |
|
3. |
Kolo/Kolojiya |
Ƙilan ya rayu |
|
4. |
Naj’a |
Idan
an bar shi ya rayu |
|
5. |
Kasatchia |
In ta
yarda ta zauna |
|
6. |
Ndowuro |
Tsawon
wane zamani |
Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 22)
A wani zubin kuwa, wani daga cikin iyayen abin haihuwar kan karɓa kiran
Ubangijinsa, yayin da aka samu juna-biyu ko bayan haihuwar. A al’adar Kanuri, sukan ba abin
haihuwar suna na musamman. Misali:
Waganifor: Shi ne wanda mahaifinsa ya rasu
aka bar shi a ciki. Mace kuwa suna yi mata
laƙabi da “Durtu” (Waziri, 2000 p. 22).
Yayin da ɗaya daga cikin kakannin abin
da aka haifa
ya rasu ba da
jimawa ba. Sukan
raɗa masa sunan wanda ya rasun su kuma yi masa laƙabi da Abatcha ko Awuzu ko Buchu (Awa
Chabe) wanda ke ƙunshe da ma’anar an sake haihuwar “Baba”
(uba). Idan kuwa kaka ce ta rasu aka haifi mace, sukan yi mata laƙabi da Yecce ko Yedza (Yachabe), mai ɗauke da ma’anar “Mama”
(uwa).
Haka kuma binciken Waziri, (2000 p. 22) ya nuna cewa, akan sa wa yaron da aka haifa sunan ɗan’uwansa da ya rasu ba da daɗewa ba, sai su yi masa laƙabi da “Surambi” wato, mayarwa.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.