Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunayen Hausawa Masu Alaka Da Dadewar Abin Haihuwa a Ciki

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Wata hanya da al’ummar Hausawa suke amfani da ita wajen ba abin da aka haifa musu suna ita ce, ta duban tsawon lokacin da abin ya ɗauka a cikin mahaifa kafin ya fito duniya. Sakamakon haka ya wanzar da samuwar sunaye kamar:

a. Bakwai: Shi ne wanda aka haifa bayan watanni bakwai da shigar cikinsa. Wato wanda aka haifa yana da watanni bakwai a ciki (Abubakar, 2015 p. 35). A ƙasar Nijar sukan kira wanda ya kasance na bakwai a jerin haihuwar ɗakinsu.

b. Shekarau: Wanda aka haifa bayan ya shekara a cikin mahaifiyarsa ko kuma ya haura shekara. A wasu sassan ƙasar Hausa kuwa ana kiran sa da laƙabin Shekare, musamman a karin harshen Hausar Yamma. Mace kuwa akan kira ta Shekara.

c. Tambai: Wanda ya daɗe a ciki ba a haife shi ba, har aka kai ana tambayar labarin haihuwarsa. Mace kuwa ana kiran ta Tambaya. A wasu garuruwan ƙasar Hausa Tambaya suna ne na Tarayya, wato ana kiran mace da namiji. Misali, a Tsafe da ke Jahar Zamfara.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments