Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
A ƙasar Hausa akan ba mutum suna ta la’akari da irin saurin ko kaifin fahimtarsa ga lamuran rayuwa. A dalilin haka ne al’ummar Hausawa sukan bai wa mutane sunaye da ke nuni da haka. Su irin waɗannan sunayen akan bayar da su ne bayan mutum ya soma girma.
a. Akwara: Wanda ya tashi da haziƙanci
tun yana yaro, har ya fi gaban a wuce (zarce) shi, kuma bai ɗaukar raini ballantana a
wulaƙanta
shi. An kamanta mai irin wannan siffa ne da itaciyar akwara, saboda ta fi gaban
a sharce ta, duk wanda ya sharci ganyanta da hannu zai ji rauni.
b. Mamari: Wanda ya tashi da basira, wato saurin fahimtar abubuwa tare da kiyaye (haddace) duk abin da ya ji da kunnensa. Shi ya sa Bahaushe kan bai wa ɗansa sunan wannan kayan kamun kifi don ya kasance kamar mamari dan ya kama kifi bai kuɓuce masa.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.