Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
A ƙasar Hausa akan laƙaba wa abin da aka haifa suna ta hanyar kula da yanayin sukunin da al’umma suke ciki. Wato idan haihuwar ta kasance a daidai lokacin da al’umma ke cikin wadatar arziki, kowa na cikin raha da nuna jin daɗi da nishaɗi ba matsawa. Inda kowa sai annashawa yake cikin yanayi na sakin fuska da ke nuni da walwala. Aukuwar haihuwa a irin wannan lokaci, shi ya wanzar da samuwar sunaye kamar:
a. Arzika: Wanda aka haifa
lokacin wadata, kuma akan ce masa Wadata ko Yakana. Mace kuwa ana ce mata
Arziki. A wasu sassan ƙasar Hausa da ke cikin Jamhuriyar Nijar, sukan danganta mai laƙabin
Arzika da wanda mahaifiyarsa ta wahala wajen naƙudar haihuwarsa.
b. Barka: Wanda aka haifa lokacin
wadata, kuma akan kira shi Albarka, mace kuwa a kira ta Baraka.
c. Goshi: Wadda aka sami wadata a
lokacin haihuwarta.
d. Ƙosau: Shi ne wanda aka haifa lokacin
kaka, wato yanayin da babu yunwa, kowa yana da wadataccen abinci.
e. Maikuɗi: Wanda iyayensa suka sami kuɗi ranar haihuwarsa.
f. Maisa’a: Wanda a lokacin
haihuwarsa aka sami alheri ko kyauta daga al’umma. A wasu ƙasashe
kuwa, shi suke kira Mainasara.
g. Shawai: Shi ne wanda aka haifa
a lokacin da al’umma ke shan wuya (wahala). Wato, yayin da al’umma ke cikin
matsi (halin ƙaƙa-ni-ka-yi). Ga al’ada,
macce da namiji na karɓa
sunan. A wasu wurare akan kira shi Sha-wuya.
h. Yalwa: Wadda aka sami yalwatar abinci a daidai lokacin haihuwarta.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.