Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunayen Hausawa Kafin Zuwan Addinin Musulunci

A tsarin sunayen gargajiyar Bahaushe tun kafin bayyanar addinin Musulunci, za a tarar suna ƙunshe da ma’anoni na musamman da kuma dalilan da suka sa aka sanya wa mai amsa su. Kodayake wasu sunayen ma’anoninsu sukan kasance a cikin duhu. Misalan irin waɗannan sunaye su ne: Barbushe, Bagauda, Mazauda, Kanoki, Burum-Burum (Adamu, 2011 p. 116-117). A jerin sarakunan Daura ma akwai: Gatama, Batatume, Sandamata, Jamata, Hamata (Adamu, 2011 p. 115).

A jerin sarakunan Zamfara ma akwai ire-iren waɗannan sunaye da suka haɗa da: Jimir, Kokai-kokai, Bukurukuru, Bakara, Gatamma, Bardau, Gubarau, Tasgarin, Ƙigaya, Burum, Taritu, Zartai, Tasau, Zande, Jimirra, Falkari, kamar yadda Harris (1938 p. 114-115) ya nuna. Ta fuskar sunayen talakawa kuwa akan sami irin su: Biju, Bodari, Ribau, Gubusani, Bauri, Gazawari da sauransu. Wannan ya faru ne sakamakon rashin taskace ma’anonin a rubuce. A wancan zamanin, mafi yawan mutanen da ke zaune a farfajiyar Afirka ta Yamma ba su da hanyar karatu da rubutu, ciki kuwa har da al’ummar Hausawa, kamar yadda Adamu (1997 p. 54) ya nuna.

Sunayen sarakunan ƙasar Hausa sun so su yi kama da na Larabawa na zamanin jahiliyya. Sakamakon sukan saka wa ‘ya’yansu sunayen iskoki, kamar: Duna, Inna, Jittakoko da sauransu. Haka sukan sa sunayen dabbobin daji da abubuwan da ke tattare da ƙwanƙwamai da waɗanda ba kasafai akan tari gabansu a take lafiya ba. Misalan irin waɗannan sunaye sun haɗa da: Jandamisa, Jankare, Guguwa, Giwa, Agwaragi, Janhazo, Tsaga-Rana, Karya Giwa, kamar yadda Ingawa (1990 p. 34) ya zo da tsarin.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments