Ticker

6/recent/ticker-posts

Fa’idar Bayar da Suna

Fa’ida, asalinta Balarabiyar kalma ce da Hausawa suka aro. Larabawa sukan kira ta da FA’IDATUN (فائدة), wadda Hausawa suka yi wa kwaskwarima don ta dace da tsarin ginin kalmomin Hausa. Kalmar tana cikin tsarin kalmomin Hausa wadda ta kasance cikin jinsin suna na mata, jam’i kuwa fa’idoji, kamar yadda CNHN, (2006 p. 130) da Garba (1990 p. 47) suka nuna. Kalmar tana ɗauke da ma’anar amfani, don haka a nan, ana nufin alfanun da ke tattare wajen bayar da suna. Wato sanya wa abu ko mutane sunaye. Daga cikin fa’idojin da suke tattare da sanya suna, sun haɗa da:

(i) Domin idan an kira mutum ya san da shi ake

(ii) Domin ambaton mutum, dabba, tsuntsu da tsirrai

(iii) Domin rarrabewa tsakanin wata al’umma da jinsi ko addini da sauransu

(iv) Domin danganta mutum da al’ummar da ya fito

Naɗewa

Suna na da gurbi na musamman ga rayuwa baki ɗayanta. Ko bayan dogon tarihi da ya samo a addinance tun lokacin halittar ɗan’adam, yana da tasiri ga rayuwar yau da kullum. Kalmomin suna na kan gaba wajen waɗanda aka fi amfani da su a maganganun yau da kullum. Akan samu sauƙin sadarwa da fahimtar juna ne da taimakonsu. 

 Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments