Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Samar Da Sunaye Daga Dabbobi
A wasu lokutan, sakamakon mu’amalar da Bahaushe ke yi da dabbobi ne ya sa yakan ɗauki sunayen wasu daga cikinsu ya sa wa ‘ya’yansa. Yakan yi haka ne ko don saboda jaruntakarsu, ko don faɗan da ke gare su, ko kuma domin lalacin su. Yakan yi haka ne domin sunayen su yi tasiri a rayuwar ‘ya’yan nasa. Misalai daga cikin irin sunayen su ne:
Jad. na 2: Sunayen Hausawa Daga Dabbobi
|
|
Suna |
Dalilin Sakawa |
|
1. |
Zaki |
Saboda ƙarfinsa ake sa wa namiji sunan zaki |
|
2. |
Giwa |
Saboda ƙarfinta ake sa wa
mace suna giwa |
|
3. |
Doki |
Saboda ƙarfinsa ake sa wa namiji suna doki |
|
4. |
Kura |
Saboda zalunci
da tsoronta ake sawa
mace suna kura |
|
5. |
Dila |
Saboda wayonsa ake sa wa namiji suna dila |
|
6. |
Gwamki |
Saboda ƙarfinsa ake sa wa namiji suna gwamki |
Samar da Sunaye Daga Tsuntsaye
Bahaushe bai taƙaita kansa
ga sanya wa ‘ya’yansa sunayen dabbobi ba, har
ma yakan ba su na tsuntsaye. Yakan bayar
da sunayen ne yayin da ‘ya’yan suka
kai wani munzili suka rinƙa aiwatar da wasu halaye.
Misali:
Jad. na 3: Samar da Sunayen Hausawa Daga Tsuntsaye
|
|
Suna |
Dalilin Sakawa |
|
1. |
Kaza |
Ya kankira
mace “kaza” saboda yawan haihuwa.
|
|
2. |
Kuti |
Yakan kira
mace “kuti” (agwagwa) saboda yawan tsabta. |
|
3. |
Maiki |
Akan
sanya wa mutum sunan
ne domin ya kasance
da siga irin
ta wannan Tsuntsu wanda ya kasance mai bajinta
da hangen nesa
da jin ƙanshin wani abu daga nisan zango
da tashi sama
can ƙololiya da nisa. |
|
4. |
Zabuwa |
Akan
kira mace “zabuwa” saboda ta kasance mai yawan tsabta
da kwalliya
tamkar yadda sifar zabuwa
take. |
|
5. |
Zakara |
Yakan kira namiji
“zakara” saboda ya fiye
son matarsa |
|
6. |
Suda |
Yakan kira
mace “suda” saboda ta fiye surutu. |
Samar da Sunaye Daga Ƙwari
Bahaushe kan sa wa ‘ya’yansa sunayen ƙwari, ta la’akari
da halayen wanda aka ba wa. Wani zubin kuma yakan bayar
da sunan ne da nufin laƙabin ya yi tasiri
ga mai amsa shi.
Misali:
a. Zuma akan ba da sunan ne ga mutum mai kyauta
da faɗa. Wasu lokutan akan ba abin haihuwa sunan ne domin ya kasance tamkar zuma yayin
da ya girma. Wato ya zama mai daɗaɗa wa al’umma
tare da rashin ɗaukar reni kamar zuma. Ya zama mai
son haɗin
kai da sauran al’umma don samar da cigaba
da riga-kafin aukuwar annobar ƙare dangi (East da Imam, 1986 p. 293).
b. Ƙuda akan ba da sunan ne ga abin haihuwa domin ya kasance mai kaifin gani da hangen nesa da kazar-kazar da rashin kasala da taka-tsantsan wajen gudanar da kowane irin lamarin rayuwar duniya (East da Imam, 1986 p. 261-262).
Samar da Sunaye Daga Tsirrai
Su ma tsirai Bahaushe bai ƙyale su ba, saboda muhimmancinsu ga rayuwarsa. Wannan ne ya sa ya samar wa ‘ya’yansa da garuruwansa sunaye daga gare su. Misali:
Jad. na 4: Samar da Sunayen Hausawa Daga Tsirrai
|
|
Suna |
Tushe |
|
1. |
Kalgo |
Sunan
gari ne |
|
2. |
Sabara |
Sunan
gari ne |
|
3. |
Dogon
Kaɗe |
Sunan
gari ne |
|
4. |
Tsamiya |
Sunan
mutum ne |
|
5. |
‘Yartsamiya |
Sunan
gari ne |
|
6. |
‘Yarkuka |
Sunan
gari ne |
|
7. |
Gamji |
Sunan
gari ne, kuma ana kiran mutum Gamji |
|
8. |
Sure |
Sunan mutum
ne |
|
9. |
Kurna |
Sunan mutum
ne |
|
10. |
Tumfafiya |
Sunan mutum
ne |
Samar da Sunaye Daga Sararin Samaniya
Hausawa kan ba
‘ya’yansu sunayen abubuwan da ke sararin samaniya, saboda yadda suka ɗauke ta da muhimmanci a
rayuwarsu ta yau-da-kullum. Domin
ta nan ne suke fahimtar lokutan yini
da makamantan haka. Misalan irin waɗannan sunaye sun haɗa
da: Hadari, Walƙiya, Zara
da sauransu.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.