Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Samar da Suna ta Sifar Abin Haihuwa
Fulani sukan yi la’akari da girma ko kamannin abin haihuwa wajen bayar da sunaye ga ‘ya’yan da aka haifa musu. A dalilin haka ne aka samu sunayen da ke nuni ga daidaitacciyar sifar abin da aka haifa, kamar:
Jad. na 34: Sanya Sunayen Fulani ta La’akari Sifa
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Danejo |
Mace
wankar darza |
|
2. |
Boɗuɗo |
Kyakkyawa |
|
3. |
Baleeri |
Baƙi |
|
4. |
Bodejo |
Ja |
|
5. |
Tauɗo |
Wanda
aka haifa dogo |
Samar da Suna ta La’akari da Halin Mutum
Al’ummar Fulani kamar sauran al’ummomi
ne, wajen saka wa mutum suna ta la’akari da ɗabi’arsa, wato halayensa na yau-da-kullum, kamar: Dauriya,
fara’a, da sauransu. Irin wannan ne ya wanzar
da bayyanar sunaye kamar:
Jad. na 35: Sanya Sunayen Fulani ta La’akari Hali
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Chenido |
Yana
nufin mai haƙuri |
|
2. |
Gaɓɓule |
Mai
tsaurin ido |
|
3. |
Muido |
Mahaƙurci |
Samar da Suna ta Duban Tsarin Haihuwa
A kowace al’umma ba
za a rasa hanyoyin da sukan saka wa ‘ya’yan da aka haifa musu suna ba. Sukan yi haka ne ta la’akari da kallon yadda aka haifa musu jerin jinsin maza
ko mata a jere da juna, kafin a haifi wani jinsin na daban. A sakamakon haka ne al’ummar Fulani ke
da sunaye kamar:
Jad. na 36: Sanya Sunayen Fulani ta La’akari Tsarin
Haihuwa
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Dudu ko Duduwa |
Wadda
aka haifa bayan haihuwar jerin ‘ya’ya maza
|
|
2. |
Jaɓɓo |
Sunan na da ma’anar “sannu da zuwa” ko “barka da zuwa. ”
Akan sa wa abin da aka haifa wanda aka daɗe ana mararin
haihuwar. |
|
3. |
Yuguda |
Wanda
aka haifa bayan haihuwar jeri ‘ya’ya mata |
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.