Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Sunayen da Ake La’akari da Lokuttan Yini
Sunaye ne da Fulani ke yi wa abin da aka haifa musu ta la’akari da lokacin da haihuwar ta wanzu tun daga fitar rana har zuwa faɗuwarta. Irin waɗannan sunayen sun haɗa da:
i. Beti:Yaron
da aka haifa da sassafe, mace kuwa su kira ta da Betuwa.
ii. Yeli: Yaron da aka haifa da rana, mace kuwa su kira
ta da Yele.
iii. Kiiro: Wanda aka haifa da dare.
Sunayen da Ake La’akari da Yanayin Shekara
Al’ummar Fulani kan sanya wa
‘ya’yan da aka haifa
musu sunaye ta
la’akari da hali irin wanda ake ciki, kamar na damina ko sanyi ko zafi da sauransu, a
lokacin da haihuwar ta auku. Wannan ne ya wanzar
da samuwar sunaye kamar:
Jad. na 32: Sanya Sunayen Fulani ta La’akari da Yanayin
Shekara
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Diyale (akan kuma ce Tabo) |
Wanda
aka haifa ana tsuga (makaka) ruwan sama |
|
2. |
Gyareɗo |
Wanda
aka haifa ana shangiya |
|
3. |
Harina |
Wadda
aka haifa a lokacin da ake cin wake[1] |
|
4. |
Harrande |
Wanda
aka haifalokacin kaka |
|
5. |
Mudiyam |
Wanda
aka haifa da damina |
|
6. |
Nduudi |
Wanda
aka haifa lokacin iskar hadari |
|
7. |
Setto |
Wanda
aka haifa ana shuka |
|
8. |
Tobo (akan kuma ce Diyale) |
Wanda
aka haifa ana tsuga (makaka) ruwan sama |
|
9. |
Turbe |
Wanda
aka haifa ana noma |
Samar da Suna ta Aukuwar Wasu Abubuwa a Tsakanin Zuriya
Fulani kan samar da sunaye ta hanyar duba ga wasu abubuwa
da suka auku na tarihi ga zuri’ar a sakamakon haihuwa ko bayan an haihu ɗin. Dalilin haka ne sukan sa wa ‘ya’yansu sunaye
da suka haɗa
da:
Jad. na 33: Sanya Sunayen Fulani ta La’akari da Aukuwar Waɗansu Abubuwa
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Audi (akan kuma ce Yoole) |
Wanda
aka haifa bayan rasuwar mahaifinsa |
|
2. |
Ɓaidu |
Wanda
aka haifa bayan auren ya
kusa mutuwa |
|
3. |
Bano |
Wanda
aka haifa bayan iyayensa sun fitar da zuciyar sake samun haihuwa |
|
4. |
Ɓanyi |
Wanda
aka samu yaɗuwar arziki mai yawa
a gidansu a lokacin haihuwarsa |
|
5. |
Cusu |
Wanda
aka haifa bayan an saki mahaifiyarsa |
|
6. |
Ja’eh |
Macen da aka haifa lokacin da aka dawo daga kiwo (namiji shi ne Ja’o) |
|
7. |
Ja’o |
Namijin da aka haifa lokacin da aka dawo daga kiwo
(mace ita ce Ja’eh) |
|
8. |
Riskuwa |
Wanda
aka samu wadata
a lokacin haihuwarsa |
|
9. |
Sajo |
Wanda
aka haifa bayan an haifi tagwaye |
|
10. |
Susi |
Yarinyar da aka haifa bayan an saki mahaifiyarta |
|
11. |
Yoole (akan kuma ce Audi) |
Wanda
aka haifa bayan rasuwar mahaifinsa |
[1]Akan taƙaita a ce “Hari. ”
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.