Ticker

6/recent/ticker-posts

Samar Da Sunayen Fulani Ta Fuskar Buri

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Al’ummar Fulani kan sanya wa abin da aka haifa musu sunayen da suke fatar ‘ya’yansu su kasance a rayuwarsu. Irin waɗannan manufofi ne suka haifar da samuwar sunaye kamar:

Jad. na 37: Sunayen Buri a Tsakanin Fulani

 

Suna

Ma’ana

1.       

Geede

Rabo

2.       

Kwairanga

Alheri

3.       

Barkindo

Albarkantacce

4.       

Gabɗo

Farin-ciki

5.       

Chubaɗo

Zaɓaɓɓe

6.       

Labbo

Takobi

7.       

Ballowa

Mai taimako

8.       

Mujalli

Wanda ya mallaki saniya

9.       

Jagordo

Jagora

10.   

Jauro

Yarima

11.   

Arɗo

Shugaba

12.   

Giɗaɗo

Masoyi[1]

13.   

Jangudo

Dalili (sanadi)

14.   

Chuto

Ɗantagwaye

15.   

Gaji

Ɗan’auta

 Idan aka dubi irin waɗannan sunaye na gargajiya da Fulani ke ba ‘ya’yansu, za a tarar cewa, wasu na ƙunshe da fatar abin da iyayen suke son su kasance in sun girma. Wasu kuma an sa su ne ta la’akari da lokaci da yanayin haihuwar abin da aka haifa.


[1]Wasu kuma sun nuna cewa, laƙabi ne na wanda aka haifa bayan haihuwar mata da yawa, kuma aka samu gudummawa mai yawa a lokacin haihuwarsa.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments