Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunayen Fulani Ta La’akari Da Dadewar Jariri a Ciki

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Shimfiɗa

Kalmar Fulani jam’i ce ta Bafillatani, wadda ta kasance suna na namiji, mace kuwa a kira ta Bafillatana. Ita wannan kalma tana ɗauke da ma’anar mutumin da yake magana da harshen Filatanci. A wata ma’ana ta biyu kuwa, tana nufin wanda yake asalinsa Fulani ne, amma yanzu ba ya jin Fulatanci, kamar yadda CNHN, (2006 p. 24) ya nuna.

Abubakar (2015 p. 141) kuwa, cewa ya yi: Fulani, kalmar suna ce jinsin mace da ke ƙunshe da ma’ana kamar haka:

i. Ƙabila masu magana da harshen Fulatanci da sana’ar kiwo.

ii. Suna ne na mace ‘yar sarki.

Al’ummomi kamar Fulani su ma ba a bar su a baya ba, domin suna da ta su hanyar da suke la’akari da ita wajen sanya wa ‘ya’yansu sunaye tun kafin bayyanar Addinin Musulunci. Fulani kan yi la’akari da tsarin haihuwa da ƙirar jikin abin da aka haifa (sifa) da yanayin shekara da sauransu. A sakamakon waɗannan abubuwa ne aka samu nau’o’in sunaye da suka jiɓinci abubuwa da dama kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya. Waɗannan abubuwa sun haɗa da:

Sunayen Sanadin Tsawon Kasancewa a Ciki

Haihuwa al’amari ne da take aukuwa a bisa tsarin Ubangiji. Akasarin abin haihuwa kan zauna a cikin mahaifa na tsawon watanni tara (9). Wato, tun daga shigar juna biyu har zuwansa sararin duniya. A wasu lokutan akan haihu ƙasa da wata tara ko ma fiye da haka. Wannan ne ya haddasa samuwar sunaye a al’ummar Fulani da suke ishara da tsawon lokacin da jinjiri ya yi a cikin mahaifiyarsa. Misali:

(i) Leɓɓe:Yaro ko yarinyar da aka haifa bayan ya ko ta shekara a ciki.

(ii) Ɓoyi: Wanda aka haifa bayan ya fi wata tara a ciki. Mace kuwa ana kiran ta Jimaɗe. A wani karin harshe ana kiran ta Nebi.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments