Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunayen Dangantaka

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

A al’adar Hausa ta girmama na gaba tare da mutumta shi, ta kai hatta da sunansa ba su faɗa a zahirinsa. Hasali ma mai takwaran sunan ba sa kiransa da shi, sai dai su sakaya. Sakamakon wannan ne ya samar da sunaye kamar:

a. Babangida: Shi ne wanda aka raɗa wa sunan kakansa.

b. Kaka: Shi ne mahaifin uwa ko uba ko mahaifiyar uba ko uwa. A al’adar ƙasar Hausa, yadda ɗa bai faɗar sunan mahaifansa haka bai faɗar sunan kakanninsa. Hasali ma, mai takwaran sunan yakan kira shi da laƙabin Kaka.

c. Ƙane: Shi ne laƙabin da mutum kan kira mai sunan wanda ke binsa a haihuwa, musamman idan yana jin nauyin faɗar sunan. Mace kuwa sai a ce mata Ƙanwa.

d. Sarki: Shi ne wanda aka raɗa wa sunan sarkin ƙasarsu. Misali, a Zariya akan kira mai suna Aminu da laƙabin Sarki a Maru kuwa Maigari laƙabi ne da ake yi wa mai suna Yunusa. 

e. Uwani: Ita ce wadda aka zana wa sunan kakarta ta fuskar uwa ko uba.

f. Yaya: Shi ne laƙabin da ƙane ke kiran Wa da shi. Wato ɗan’uwan haihuwa da ya fi yawan shekaru. Haka mutum kan kira wanda sunan yankansa/ta ya zo ɗaya da na wansa ko yarsa. Ita ma amarya takan kira uwargida da laƙabin. Yayin da matan ƙani kan kira wan ko yar mijinsu da laƙabin Yaya. A ƙasar Nijar shi sukan kira Babba.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments