Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakubban Sunayen Hausawa Da Suke Ishara Da Auren Zumunci

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Hausawa al’umma ce da ke ƙoƙarin ƙarfafa dangantakarsu ta jini da take tsakanin ‘yan’uwa ta fuskar haɗa auratayya tsakanin dangi. Sakamakon haka ne ya haifar da samuwar sunayen laƙubba kamar:

a. Dada: Shi ne wanda mahaifiyarsa da mahaifinsa dangin juna ne, wato auren zumunta aka yi a tsakaninsu.

b. Kadada: Ita ce wadda mahaifiyarta da mahaifinta dangin juna ne, wato auren zumunta aka yi a tsakaninsu.

Naɗewa

Kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, Hausawa suna raɗa suna ne ta hanyar la’akari da abubuwa daban-daban. Sun shafi halittu mabambanta da ke kewaye da Hausawa, ciki har da dabbobi da tsirrai. A ɓangare guda kuwa, yanayin lokaci ake dubawa domin samar da sunayen. Akan kuma yi la’akari da siffar abin da aka haifa ko lamuran zamantakewa da suka faru ko suke faruwa ga ahalin domin raɗa suna. Wannan fasaha ta yi kama sosai da matakan samar da sunayen al’ummomin Kanuri da Fulani da aka tattauna a babi na biyu da na uku.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments