Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Zuwan Musuluci farfajiyar ƙasar Hausa, ya sa al’ummar Hausawa laƙaba wa ‘ya’yan da aka haifa musu a lokutan hidimomin addinin. Sunayen suna ishara ga irin yanayin lokacin da haihuwar ta wanzu. Misalan irin waɗannan sunayen sun haɗa da:
a. Alhaji: Wanda aka haifa
ranar babbar salla. Ana kuma kiransa Baita. Mace kuwa ana yi mata laƙabi da Tasalla.
b. Azumi: Wadda aka haifa a
cikin watan Ramadan (watan azumi). Namiji kuwa ana kiransa Ɗan’azumi.
c. Labaran: Wanda aka haifa
a watan azumi. A wasu ƙasashe
kuwa sukan ce Lamaran ko Ramadan.
d. Ladan: Wanda aka haifa a
daidai lokacin da ake kiran assalatu. Kuma akan kira shi Maisalati.
e. Sallau: Wanda aka haifa
ranar salla, akan kira shi Nasalla. Mace kuwa ana kiran ta Salluwa ko Tasalla.
f. Yawale: Wanda aka haifa a
kan hanyar zuwa Makka. Mace kuwa ana yi mata laƙabi
da Yabi.
Naɗewa
Zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa ya samar da sauye-sauye masu
tarin yawa ga rayuwar Hausawa. Waɗannan
sauye-sauye sun yi tasiri har ga lamarin raɗa
sunaye kamar yadda aka tattauna a cikin wannan babin. Hausawa sun fara amfani
da sababbin sunaye masu tarin yawa sakamakon abubuwan da addinin ya zo da su.
Daga ciki har da sunayen Ubangiji da na mala’iku da mazanni da salihan bayi da
makamantansu. A ɓangare guda kuwa, har ranaku
da shagulgulan da suka samu a sakamakon zuwan addinin na taka rawar gani wajen
samar da sababbin sunayen Hausawa.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.