Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa ya wanzar da samuwar sababbin sunayen alkunya a tsakanin al’ummar Hausawa. Irin waɗannan sunayen sun ƙunshi waɗanda suke ishara da dangantaka ta jini, ko ta mulki ko ayyukkan da suka jiɓinci ibada da sauransu, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.
Dangantaka ta Jini
Yayin da Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, ya tarar da al’ummar Hausawa ba sa ambaton
haƙiƙanin
sunayen iyayensu. Wannan ne ma ya sa akan ji ko Bamagujen ƙasar Hausa bai faɗar
sunan mahaifinsa ko na surikinsa, sai dai ka ji sukan kira shi da Maigida da
sauransu. Da Musulunciya zo sai ya ƙarfafa
wannan alkunyar har aka samu kalmomin harshen Larabci da ake amfani da su,
saboda irin tasirin da addinin ya yi a gare su. Irin wannan tasirin ne ya sa
idan aka haifa wa mutum ɗa ko ‘ya, ya sanya mata ko
masa sunan mahaifiya ko mahaifi yakan yi amfani da laƙubban alkunya wajen sakayawa. Misali:
a. Abba: Wanda aka raɗa wa
sunan kakansa, al’ummar wannan gidan, saboda jin nauyin (kunyar) faɗar
sunan, sukan kira shi da suna Abba, ko Babangida.
b. Ummi: Wadda aka raɗa wa
sunan kakarta, al’ummar wannan gidan sukan riƙa
ambaton ta da suna Ummi, saboda jin nauyin (kunyar) ambaton sunan domin
girmamawa gare ta. Don haka sukan kira ta da suna Ummi.
Alkunya da ta Danganci
Shugabanci
A ƙasar Hausa, al’ummar Hausawa, sukan ji
nauyin faɗar (ambaton) sunan wanda Allah Ya
shugabantar a kansu ta fuskar ɗaukar nauyin jan ragamar
lamuran rayuwarsu ta yau-da-kullum. Wannan ne ya sa ba sa faɗin
sunan shugabansu domin girmamawa gare shi. Kuma an ɗauki
duk wanda yake ambaton sunan shugabansa na yanka a matsayin marar ta’ido
(kunya). Ire-iren waɗannan sunayen sun haɗa
da:
a. Alƙali: Wanda aka naɗa
domin gudanar da shari’a tare da yanke hukunci a tsakanin masu jayayya a kan
wani abu ko wata matsala, domin sasanta su ko tsawatarwa.
b. Hakimi: Wanda aka naɗa
domin ya shugabanci al’ummar wata gunduma da take ƙarƙashin
riƙon wata masarauta.
c. Ladan: Wanda ya zamanto
yana kiran salla domin faɗakar da al’ummar Musulmi
lokacin gudanar da ita ya yi.
d. Liman: Wanda ya kasance
yana jagorancin al’umma wajen gudanar da sallolin farilla na yini da na Juma’a.
e. Malam: Wanda ya nemi
ilimin addinin Musulunci, ya kuma mallake shi, har ya zamanto yana koyar da shi
a tsakanin al’umma. Mace kuwa akan kira ta Malama.
f. Muhuti: Malami mai ba Alƙali shawara game da hukunci da ya dace a
zartar.
g. Na’ibi: Wanda yakan
wakilci liman wajen jagorancin salla a duk lokacin da wata lalura ta hana liman
halartar masallacin.
h. Sarki: Wanda aka naɗa ya
shugabanci al’ummar gari ko ƙasar
da take tattare da garuruwa a ƙarƙashinta.
i. Sayyadi: Alkunya ce da
ake yi wa kowane Musulmi domin girmamawa.
j. Waziri: Babban mai ba
sarki shawara wajen gudanar da mulkin masarauta.
k. Yari: Wanda aka naɗa a
matsayin shugaban da yake kula da gidan turu (kurkuku).
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.