Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Shimfiɗa
Al’ummar Kanuri tamkar sauran al’ummomi ne ta wajen bayar da sunaye ga ‘ya’yan da Allah Ya albarkace su da haihuwa. Tun a zamanin duhun kai (jahiliyya) sun riƙa sanya wa ’ya’yansu sunayen abubuwa mabambanta kamar: Dabbobi da tsuntsaye da halittu masu rarrafe da tsirrai da sandararrun abubuwa masu alfarma. Duk da haka ba sa sanya wa ‘ya’yansu sunayen ƙasƙantattun abubuwa don gudun kada ɗabi’unsu su yi tasiri ga rayuwarsu. A sakamakon haka ne suke da sunayen laƙabi da suke ɗauke da ma’anonin nau’o’in abubuwan kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya kamar haka:
Laƙabi da Sunayen Dabbobi
Dabba wata halitta ce mai ƙafa huɗu. Ba ta magana kuma ba ta da cikakken tunani. Ita ma ta kasu kashi uku kamar haka:
(1) Dabbar gida
(2) Dabbar dawa (daji)
(3) Dabbar ruwa.
Bayyanar addinin Musulunci
a tsakanin al’ummar Kanuri (Barebari)
bai hana su ci gaba da amfani da irin waɗannan sunayen gargajiya ba. Hasali ma, sai irin waɗannan sunaye suka zama sunayen laƙabi gare su. Sakamakon
haka ne akan samu mutane suna karɓar sunayen dabbobi
a matsayin laƙabinsu.
Misalai daga cikinsu
sun haɗa
da:
Jad. na 12: Laƙabin Dabbobi a Sunayen Kanuri
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Baltu |
Kure |
|
2. |
Bundi |
Zaki |
|
3. |
Kenna |
Maraƙi |
|
4. |
Kinyeri |
Kurege |
|
5. |
Kutta |
Gajeren doki ƙaƙƙarfa |
|
6. |
Ngaran |
Barewa mai ƙaho mai reshe |
Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 35)
Sanya wa ɗan’adam laƙabi
ta amfani da sunayen dabbobi,
lamari ne da ya zama
ruwan dare game duniya da ake iya samu
a tsakanin al’ummomi daban-daban. Kodayake yayin da wasu al’ummomin suka karɓi adinin Musulunci sai sunayen suka sauya suka zama na laƙabi
a madadin na yanka.
Duk da haka, al’ummar Larabawa sun cigaba da amfani da irin waɗannan sunaye a matsayin na yanka.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.