Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Saurayi yaro ne wanda bai wuce daga shekara 16 zuwa 25 ba, wanda ya kai munzalin balaga, amma ba a yi masa aure ba. A ma’ana ta ƙamusu, an bayyana cewa: “Saurayi shi ne yaron da ya balaga, amma bai yi auren fari ba” (CNHN, 2006 sh. 394). A irin waɗannan shekarun nasa yana jin kansa wani mai ƙarfi tare da ganin cewa zai iya aikata komai. A irin waɗannan matakin ne ake kulawa da shi sosai wurin tarbiyya da ba shi shawara domin duk abin da ya saba da shi a wannan matakin shi zai ɗore da shi har tsufa.
Samartaka matakin rayuwa ne mai
muhimmanci. Wannan ne ya sa karin maganan Hausa daban-daban suka kawo zancen
surayi. A wasu lokutan, akan yi zance ne kai tsaye game da saurayin. A wasu
lokuta kuwa, akan yi amfani da kalmar saurayin ne kawai domin isar da wani saƙo
cikin falsafa. Ga wasu daga cikin karin maganan da suka ambaci saurayi:
1. Saurayi abokin ‘yanmata
Yawanci akan yi amfani da wannan
karin magana a matsayin kirari ga samari, ko ma yaran da ba su kai matakin
samartaka ba. Bugu da ƙari, wannan karin magana yana nuni da cewa komai da
mazauninsa, kamar dai yadda aka nuna abokin burmin saurayi, ‘yan mata ne (kowace ƙwarya
da abokiyar burminta).
2. Idan saurayin bana da kyau, na
baɗi ya fi shi
A tubalin gina wannan karin
magana, an yi la’akari da ‘faɗaɗɗen’ al’amari da aka lura
da shi a rayuwar yau da kullum – wato cewar ana ƙara haifo kyawawa a duniya. Duk da haka,
a ɓangare ɗaya karin maganar yana nuni
da cewa gaba ta fi baya yawa; kuma idan da rai, da rabo.
Wasu ƙarin misalan karin magana
a ƙarƙashin
wannan rukuni sun haɗa
da:
a. Dutse, maganin saurayi
b. Ko da magana, karuwa ta ga
samari?
c. Shinge gabanka samari
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.