Ticker

6/recent/ticker-posts

Gamayyar Maza da Mata a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Bayan misalan kare-karen magana da suka yi tsokaci game da mata da maza a keɓance, akwai kuma waɗanda suke gwama maza da matan domin yin batu a kansu a lokaci ɗaya. Sukan nuna alaƙarsu ga juna ko gurbinsu a rayuwar juna ko kuma yadda zamantakewarsu take kasancewa. A ƙasa an kawo misalan waɗannan:

1. Juriya namiji ce, raki ko mace

Wannan karin magana, tana nuna bambancin halitta tsakanin namiji da mace wadda ke nuna ƙarfin halitta da ɗabi’a ta namiji da kuma raunin halitta da ɗabi’a ta mace. Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya rena wani a wajen daidaita su ta fuskar ƙwazo da juriya. Sai a nuna ɗayan a ce masa " mace", don raunin sa. Wannan karin magana tana fito da rauni da rashin juriyar mace da saurin yin raki a duk lokacin da ta ji wuya. Haka kuma, ana ƙara tabbatar da cewa halittar mace ba ta kai namiji wurin ƙwazo da juriya ba a rayuwar Hausawa.

2. Namiji dutsi, mace sakaina

Wannan karin magana tana nuna ƙarfi da jaruntaka ta namiji da kuma rauni da ƙarancin jaruntaka ta mace, inda aka kwatanta namiji kai tsaye da dutsi, ita kuwa mace aka kwatanta ta kai tsaye da sakaina (ƙwarya). Shi ma wannan kusan duk ana amfani da su a wuri ɗaya da ta farkon.

3. Namiji tabarmar ƙashi, inji wadda mijinta ya ɓata wa rai

Duk tabarmar da aka saƙa ta da ƙashi ba za ta yi daɗin zama ba, balle daɗin kwanciya, da sauran mu’amalolin rayuwa da hutawa. Mata su ke amfani da wannan karin magana idan suka fuskanci mummunar zamantakewa daga mazansu, domin su rage raɗaɗin ɗacin mu’amalar rayuwa da suke ji, su kuma mayar da martani a lokacin ɓacin rai.

4. Matar mutum kabarinsa

Wannan karin magana tana nuna cewa duk matar da aka ƙaddara namiji ya aura, to duk yadda aka kaɗa aka raya sai ya aure ta. Ana kwatanta mace da kabari kai tsaye domin bayyana cewa duk inda kabarin mutum yake a ciki ake rufe sa bayan mutuwarsa, haka nan wani mutum ba zai auri matar wani mutum ba sai dai tasa. Ana amfani da shi a cikin zance, idan ana son a nuna cewar abin da yake rabonka ne bai wuce ka.

5. Darajar mace – miji

Wannan karin maganar tana nuna muhimmancin aure ga mata, haka kuma kome matsayin mace, abin da yake zama ƙololuwar darajarta da mutuncinta, shi ne mijinta. A wurin Hausawa, macen da ta kai munzalin aure ba ta yi ba, ko mijinta ya mutu ba ta sake wani aure ba, ko aurenta ya mutu ta daɗe ba ta yi wani aure ba, darajarta ba daidai ta ke da ta matan da suke da aure ba.

6. Mace darajar namiji ce

Ita ma wannan karin maganar kamar dai wadda ta gabata ce, tana nuna cewa kome matsayin namiji, abin da yake zama ƙololuwar darajarsa da mutuncinsa ya kasance yana da mata.

Ana amfani da wannan karin magana da wanda ya gabace shi, a nuna cewa, wani abu ba zai kammala ba, sai da wani abu.

7. Kan mace na miji ne

Wannan karin magana tana nuna babban matsayin miji a wajen matarsa ta hanyar bayyana cewa mafi ƙololuwar abin da mace take tinƙaho da shi to mallakar mijinta ne. Gaɓa mafificiyar darajja a sassan jikin ɗan'adam shi, ne kai, wanda duk ya mallaki kan mutum, to ya mallake sa gaba ɗaya. A nan abin da ake nufi da kai shi ne, duk abin da mace ta mallaka ko take taƙama da shi ko take alfahari da shi mallakar mijinta ne, domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne inji Hausawa.

Ana amfani da shi ne, don nuna karfin ikon maza a kan matansu.

8. Maganin mace, mijinta

Wannan karin magana tana nuna irin yadda miji yake da ƙarfin ikon sarrafa rayuwar mace da kuma saita lamuranta tare da kawar da damuwarta. An kwatanta miji kai tsaye da magani ga matarsa, saboda matsayinsa a mahangar alada na magance matsalolinta da samar da natsuwa da kwanciyar hankali ga rayuwar ta. Ana amfani da shi wajen nuna wani abu, wanda yake kwantar da wani abu ko kawar da matsalar da ta same shi ko ya samar.

9. Maza ba mata ba

Wannan karin magana tana nuna cewa maza sun bambanta da mata ta fuskar halittarsu da ɗabi’unsu da wasu halayensu. Don haka abubuwa da dama waɗanda maza suke gudanarwa a zamantakewa, mata ba za su iya yi ba. Haka kuma, akan samu bambancin fahimta da ra’ayoyi tsakanin mata da maza saboda tsarin halittarsu.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments