Ticker

6/recent/ticker-posts

Budurwa a Madubin Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Da ka ga wata za ka ga Zara – da zarar an ambaci saurayi, to na gaba budurwa za a ambata. A ma’anar da ƙamusu ta bayar, “budurwa ita ce yarinyar da ba ta yi auren fari ba” (CNHN, 2006 sh. 51). Budurwa yarinya ce wadda ba ta wuce shekara 12 – 19 ba, kuma ba a yi mata aure ba, amma watakila an tsayar mata da manemi. Budurwa a irin wannan yanayi ana sa ran ta kasance mai hankali da jin kunya da kamun kai da barin wasa da ƙasa da kuma nisanta kanta da wasa cikin ‘yan maza har dai idan ta fara al’ada. Duk wasu abubuwa marasa kyau za ta nisanta kanta da su, saboda kada ‘yan gidan maneminta ko shi manemin kansa ya gan ta a cikin yanayin da za ta ji kunya.

Tamkar dai samartaka ga maza, matakin ‘yanmatantaka (budurtaka) matakin rayuwa ne mai muhimmanci ga mata. A wannan lokaci ne tauraron mace yake haskawa, har ake yi mata kirari da allurar cikin ruwa, mai rabo ka ɗauka. Karin maganar Hausa da suka taɓo budurwa sun haɗa da:

1. Budurwa da safe maɗaci, da marece zuma

Wannan karin magana yana nuni da abubuwa daban-daban. Cikinsu kuwa har da ɗabi’ar budurwa da suke nuni da ajizancinta. Tana iya saɓa wa mutum har ta ɓata masa rai. Sai dai idan aka yi haƙuri kuwa, tana iya faranta masa rai ɗin. A taƙaice dai ke nan, tana da abubuwa a rayuwa masu ban takaici, sannan tana da abubuwa na soyuwa ga zuciya a ɗaya fannin.

2. Budaren bana da kyau ba hali

Wannan karin maganar yana nuni da abin da yake faruwa game da sauyawan halayen mutane a sakamakon tasirin zamani. Kyawawan halaye da ɗabi’u suna ƙara ƙaranta a kowace rana da har ake ganin gwamma jiya da yau. A haka lamarin ya kasance, wanda ya tuna bara bai ji daɗin bana ba.

Wasu ƙarin misalan karin magana a ƙarƙashin wannan rukuni sun haɗa da:

1. Budurwa haja ce, kowa ya gani yana so

2. Cab! An ce wa budurwa, ta auri tsoho

3. Gajin haƙuri, shi ya kawo budurwa ta yi ciki

4. Idan budurwar bana da kyau ta baɗi ta fi ta

5. Rashin haƙuri, shi ka sa budurwa farka

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments