Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Laƙabi ta Yanayin Jerin Zuwan Haihuwa
Al’ummar Kanuri sukan yi wa ‘ya’yan da aka haifa musu laƙabi ta hanyar la’akari da tsarin zuwan abin haihuwar da kuma rayuwarsa. Irin waɗannan laƙubba sun haɗa da:
Jad. na 22: Laƙabi ta La’akari da Yanayin Haihuwa a Sunayen Kanuri
|
|
Suna |
Ma’ana |
|
1. |
Ma’aji |
(Daidai da Kur) Ɗan fari (babban ɗa a gida)[1] |
|
2. |
Kur |
(Daidai da Ma’aji) Ɗan fari (babban ɗa a gida) |
|
3. |
Gaji |
Ɗan’auta |
|
4. |
Gabciya |
Wanda
aka haifa bayan haihuwar jerin ‘ya’ya suna mutuwa |
|
5. |
Kolo |
Yaron
da mahaifiyarsa ta rasu bayan haihuwarsa |
|
6. |
Durtu |
Yaron
da mahaifinsa ya rasu
(maraya) |
|
7. |
Chellu |
Shi
ne yaron ko yarinyar da aka haifa a tsakanin haihuwar mata biyu
ko macen da aka haifa a tsakanin haihuwar maza biyu.
|
|
8. |
Kawu |
Su ne
tagwaye, wanda aka fara haihuwa
ana ce masa Hussaini ko Wasainiji, wanda ke
bi masa kuwa Hassan. |
|
9. |
Gambo |
Shi
ne wanda aka haifa
bayan haihuwar tagwaye |
Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 21)
Sanya Suna ta Yanayin Haihuwa
Yanayi a nan yana nufin nau’in halin da ake ciki na damina
ko sanyi ko zafi da makamantansu. Su ma Kanuri sukan amsa sunayen lokacin da aka haifi mutum.
Misali:
Jad. na 23: Raɗa Sunayen
Kanuri ta La’akari da Yanayin Haihuwa
|
|
Suna |
Jinsi |
Ma’ana |
|
1. |
Aji (ana kuma kiran sa Baitu) |
Namiji |
Shi
ne wanda aka haifa a cikin watan salla babba
(Dhul-Hajji). |
|
2. |
ArMalam (ana kuma kiran sa Asham) |
Namiji |
Shi
ne wanda aka haifa a cikin watan azumi. |
|
3. |
Asham
(ana kuma kiran sa ArMalam) |
Namiji |
Shi
ne wanda aka haifa a cikin watan azumi. |
|
4. |
Baitu (ana kuma kiran sa Aji) |
Namiji |
Shi
ne wanda aka haifa a cikin watan salla babba
(Dhul-Hajji). |
|
5. |
Jabba |
Namiji |
Shi
ne wanda aka haifa a tsakiyar lokacin da ake ruwan
sama sosai.
|
|
6. |
Maulud |
Namiji |
Shi
ne wanda aka haifa ranar
12 ga watan Rabi’ul
Auwal. |
|
7. |
Ngumuri |
Mace |
Yarinyar
da aka haifa ranar salla.
|
|
8. |
Sarwa |
Namiji |
Shi
ne wanda
aka haifa a ƙarshen damana. |
|
9. |
Shawwallam |
Mace |
Yarinyar
da aka haifa a cikin watan
Shawwal |
Tushen Bayani: Wazir, (2000 p. 21)
Al’ummar Kanuri (Barebari) ba sa amfani da sunan ranakun haihuwa wajen yi wa mutum laƙabi don gudun makaru.
[1]Shi ne wanda aka fara haihuwa. Shi ne babba a zuri’ar (tamkar dai Magaji ko wa ko babban yaya a Hausa).
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.