Ticker

6/recent/ticker-posts

Samuwar Hardaddun Lakuba Na Sunayen Hausawa

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Samuwar Harɗaɗɗun Laƙubba

Su ne laƙubban da yake ƙunshe da abubuwa guda biyu a haɗe wuri ɗaya. Koyaushe irin waɗannan laƙubban a haɗe ake rubuta su ba a rarrabewa domin samar da ma’ana ɗaya. A harshen Hausa ma akwai irin waɗannan harɗaɗɗun laƙubban. Harɗaɗɗun laƙubban Hausa sun kasu rukuni uku kamar haka:

i. Laƙubba masu Tushen mallaka

ii. Laƙubba masu tushen tsigalau

iii. Laƙubba masu Tushen aikatau

Za a ɗauke su ɗaya bayan ɗaya a yi bayanin su gwargwadon abin da Allah Ya fahimtar da mu.

Laƙubba Masu Tushen Mallaka

Wasu laƙubban Hausawa ne da suke ɗauke da yankin ƙwayar ma’anar mai wadda ke nuna mallaka, sannan a haɗa ta da suna gama-gari, su bayar da dunƙulallen laƙabin mutum. Akasarin nau’o’in waɗannan laƙubban sun kasance na jinsin mutane maza ne, akan sami na mata. Kaɗan daga cikinsu ne suke da karin sautin sama a wasalin a na sassauƙar gaɓar ƙarshe. Kuma suna ƙunshe da gajeren wasalin ƙarshe, kamar a waɗannan misalai:

Jad. na 45: Misalan Harɗaɗɗun Sunayen Hausawa

 

Harɗantawa

Harɗaɗɗen Suna

Tsokaci

 

Ƙwayar Ma’ana

+

Suna

 

 

1.       

Mai

+

gari

Maigari

Laƙabin da ake yi wa wanda aka raɗa masa sunan sarkin garinsu. Idan an lura za a tarar cewa, ƙwayar ma’ana ta mai tana nuna Mallakar abu, wato an haɗa ta da gari da ya kasance suna ne na wurin da mutane suka zauna, suka gina gidaje. A taƙaice yana

nufin sarkin gari.

2.       

Mai

 

ɗaki

Maiɗaki

Matar mutum ko uwargida. Anan an haɗa ƙwayar ma’anar mai da ɗaki wanda yake suna ne na ginin da aka yi ƙunshe da ƙofa

da murfi don kwanciya ko ajiya ko yin wani abu.

3.       

Mai

 

riga

Mairiga

Laƙabin da ake yi wa wanda aka haifa da tantani lulluɓe da jikinsa. A nan an haɗa ƙwayar ma’anar mai da riga wadda take suna na abin da ake sanya wa mai wuya da hannaye domin suturce jiki tun daga wuya har zuwa ƙwabri.

4.       

Mai

 

wada

Maiwada

Laƙabin da ake yi wa wanda aka haifa a lokacin kaka, wato lokacin da ake girbe amfanin gona, ƙarshen damina. A nan an haɗa ƙwayar ma’anar mai da wada wadda take suna ne da yake ɗauke da ma’anar arziki ko wadata. A taƙaice gaba ɗaya ana nufin maiwadata. Ko wanda ya mallaki arziki ko yakana.

5.       

Mai

 

gado

Maigado

Laƙabin da ake yi wa wadda ake kira da suna Balkisu. An haɗa ƙwayar ma’anar mai da ke da ma’anar mallaka da kalmar suna ta gado da ke nufin abin kwanciya.

 

6.       

Mai

 

kuɗi

Maikuɗi

Laƙabin da ake yi wa wanda aka samu gudummawar kuɗi a lokacin da aka haife shi. A nan an haɗa kalmai mai da ke nufin mallaka da kalmar suna, wato kuɗi. Wani abin da hukuma ta aminta a yi amfani da shi wajen saye da sayarwa, wato takardu ko ƙarafan musamman da aka bayar a madadin kayan da ake sayarwa, ko ladan aikin da aka yi maka.

7.       

Mai

+

Unguwa

Mai’unguwa

 

Laƙubba Masu Tushen Tsigalau

Su ne laƙubban da suke da tushen ɗan ko ‘yar sannan a haɗa da suna. Idan za a rubuta su akan haɗe su ne. Misalansu sun haɗa da:

Jad. na 46: Misalan Harɗaɗɗun Sunayen Hausawa

 

Harɗantawa

Harɗaɗɗen Suna

 

Ƙwayar Ma’ana

+

Suna

 

1.       

Ɗan

+

Binta

Ɗanbinta

2.       

Ɗan

+

wanzam

Ɗanwanzam

3.       

Ɗan

+

gwaggo

Ɗangwaggo

4.       

Ɗan

+

ƙwairo

Ɗanƙwairo

5.       

Ɗan

+

Tannin

Ɗantanin

6.       

‘Yar

+

gwaggo

Yargwaggo

Wani zubin kuwa akan haɗa sifa da suna ne su bayar da laƙabi ɗaya. Misali:

Jad. na 47: Misalan Harɗaɗɗun Sunayen Hausawa

 

Harɗantawa

Harɗaɗɗen Suna

 

Sifa

+

Madanganci

+

Suna

Laƙabi

1.       

Ja

+

-n

+

kiɗi

Jankiɗi

Wani lokacin kuwa sai a haɗa tsigalau da sifa su samar da laƙabi, kamar a waɗannan misalai:

Jad. na 48: Misalan Harɗaɗɗun Sunayen Hausawa

 

Harɗantawa

Harɗaɗɗen Suna

 

Tsigalau

+

Sifa

Laƙabi

1.       

‘Yar

+

Ja

‘Yarja

2.       

Ɗan

+

Ja

Ɗanja

Laƙubba Masu Tushen Aikatau

Akan sami wasu laƙubban Hausawa da suka kasance harɗaɗɗu ne da aka samar da su ta hanyar amfani da kalmar aikatau mai gaɓa ɗaya da yankin suna. Misalan irin waɗannan sunaye sun haɗa da:

Jad. na 49: Misalan Harɗaɗɗun Sunayen Hausawa

 

Harɗantawa

Harɗaɗɗen Suna

 

Aikatau

+

Suna

 

1.       

Sha

+

Gari

Shagari

2.       

Ci

+

Tumu

Citumu

3.       

Ƙi

+

Giji

Ƙigiji

Naɗewa

Haƙiƙa sauye-sauyen zamani ya zo da sababbin sunaye a ƙasar Hausa. Kamar yadda aka tattauna a wannan babin, waɗansu daga cikin sunayen sun samu ne sakamakon cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu makusanta, wato Fulani da Barebari. Waɗansu kuwa sun samu ne sakamakon faruwar abubuwa na musamman da ke haifar da alkunya ga waɗansu sunaye, sannu a hankali har su ɗore ya zamo sunaye sanannu. A ɓangare guda kuwa, Hausawa sun ƙago waɗansu ne ta hanyar harɗanta kalmomi. Lura da yadda faruwa abubuwa ke tsirar da sababbin sunaye, ana iya hasashen cewa har gobe Hausawa za su ci gaba da samun bunƙasar sunaye.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments