SUNAYEN HAUSAWA (BUNƘASAR SUNAYEN HAUSAWA DA MAƘWABTANSU)
Na
Adamu Rabi'u Bakura
Da
Abu-Ubaida Sani
Sunaye kamar yadda suke a ƙasar Hausa a yau, ba lokaci guda aka buɗe ido aka gan su haka ba. Akwai matakai da aka biyo tun farkon lamari zuwa yau. A kowace gaɓa, akan samu sauye-sauye da suka shafi samuwar sababbin sunaye ko kwaskwarima ga waɗanda ake da su. A waɗansu lokutan kuma, akan samu salwanta ko ɓacewar waɗansu sunayen a bisa dalailai da suka haɗa da sabuwar fahimta ta al’ada ko ta addini da ke ɗaukar su a matsayin ƙauyanci ko saɓo, da dai makamantansu. Haka kuma, akan samu sauye-sauye ga sunaye musamman yayin da Hausawa suka yi cuɗanya da waɗansu baƙin al’ummu. A irin wanan yanayi, Hausawa na aron sunaye daga al’ummomin tare da yi musu kwaskwarima a mafi yawan lokuta. A taƙaice ke nan, sunaye na bunƙasa sakamakon dalilai da dama. Wannan babi ya mayar da hankali wajen tattauna muhimman fitilun kalmomi da za su yi jagora ga mai karatu.
Suna kalma ce
da ke cikin tsarin jerin jinsin maza. Jam’in kalmar kuwa ita ce sunaye. A fahimtar Abubakar, (2015 p. 438), “Kalmar suna lafazi ne da ake kiran mutum ko wani abu
da ita, kamar yadda ya nuna.” CNHN, (2006
p. 401) ya bayyana cewa, kalmar tana
cikin jerin sunaye jinsin namiji.
Ya kuma nuna cewa,
jam’in kalmar ita ce: suunaayee ko sunannaki kamar yadda ake amfani da ita wajen kira ko Ambaton wani abu.
Amfani, (2004) ya bayyana cewa, masana harsuna ta fuskar gargajiya suna da fahimtar cewa suna “kalma ce ta kiran mutum
ko bagire (muhalli) ko abu, wato sunan mutum ko sunan muhalli
ko sunan abu. ”
Su kuwa masana binciken harsuna ta hanyar zamani, sun bayyana ma’anar suna
ta la’akari da irin ayyukan da suke a cikin jimla, kamar haka:
Suna shi ne
kalma da take ɗaukar alamar jam’i, misali: yaro– yara. Takan kuma
zama cibiyar tawagar kalmomi, ta kuma yi aikin miƙau ko karɓau a cikin jimla. Wannan ma’ana tana ƙunshe da naƙasu,
domin babu gamsasshen bayani mai ma’ana
game da rabe-raben suna.
Sakamakon haka, hanyar gargajiya ta fi ma’ana da amfani ta wannan haujin. Misali, kalmar abu na iya zama: “tukunya, ko riga, ko aiki kamar shuka,
ko noma, ko abin da ake ji a zuci ko jiki. Misali, soyayya, ko zafi, ko sanyi, ko mutum ko dabba ko wani wuri da
sauransu, kamar yadda Amfani, (2004) ya bayyana.
Lura da ire-iren waɗannan muhawara
tsakanin masana, ana iya cewa, sunaye
na nufin keɓantattun kalmomi
da ake amfani da su wajen ambaton mutane da wurare da abubuwa da sauran halittu
masu rai ko marasa rai, waɗanda ake iya gani
ko taɓawa ko shaƙa ko koma bayansu,
ko suke wanzuwa ko kuma ake rayawa a zuci kawai. Za a iya fahimtar suna da
ma’anar kalmar ambaton abubuwa ta yadda za a iya bambanta wannan abu da waninsa, don gudun kada komai ya kasance komai. Kalmar tana iya zama ta yi ishara ga keɓantaccen abu na musamman da ake magana a kansa.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.