Ticker

6/recent/ticker-posts

Alkunyan Sunayen Hausawa a Sakamakon Faruwar Wasu Abubuwa

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Bayan kafuwar Daular Usumaniyya, wasu abubuwa sun auku ga shugabannin al’ummar. Irin waɗannan abubuwa sun wanzar da samuwar alkunya domin sakaya sunayen jagororin, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya:

a. Bello: Akan yi wa mai suna Bello alkunya da Maiwurno. Wannan ya faru ne sakamakon wafatin (rasuwar) Sarkin Musulmi Muhammadu Bello a garin Wurno, aka kuma rufe shi a can Wurno ɗin. Wannan ya sa Wurno ta kasance mazauni na har abada gare shi tun da can ne kabarinsa yake. Sakamakon haka, duk mai suna Bello, a gundumar Sakkwato ana kiransa da Maiwurno. Hasali ma Wurno ce Cibiyar Masarautarsa, wadda ya jagorantar daga 1817 zuwa 1837, bayan ya taso daga Sakkwato.

b. Dabagira: Laƙabi ne da ake kiran aduwa da shi, domin jin nauyin ambaton sunan saboda sunan ya so ya yi kama da sunan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, kamar yadda Sufi (1993 p. 86).

c. Magajin Gari: Alkunya ce da ake yi wa mai suna Mamuda a Kano, akan taƙaita shi a ce Magaji.

d. Maichimola: Alkunya ce da aka yi wa Sarkin Musulmi Ahmadu ɗan Abubakar Atiku (1859-1866), saboda ya mayar da garin Chimola a matsayin sansaninsa, kamar yadda Sokoto (2014 p. 394) ya nuna. Wannan ne ya sa duk mai suna Ahmadu akan yi masa laƙabi da Maichimola, saboda jin nauyin faɗar sunan, musamman a ƙasar Sakkwato.

e. Maiharara: Alkunya ce da ake yi wa mai suna Mariya a Kano, musamman a fada. Ana yi mata laƙabi da Maihara, wani zubin sukan taƙaita su ce: Harara. Sunan ya samo asali ne daga wata jikarta da ake kira Magajiya, wadda babban ɗanta, Sarkin Kano Abdullahi Bayaro ya haifa. Binciken Sufi (1993 p. 82) ya nuna cewa, Magajiya babbar ‘yar Sarkin Kano ce ta laƙaba mata suna Maiharar, saboda duk lokacin da suka haɗa ido da Magajiyar, sai Fulani Mariya ta harare ta. Don haka wata rana da aka ɗauki Magajiyar aka tunkari (nufi) Mariyar da ita, sai ta dinga cewa: “Ni ka da ku kai ni wajen mai hararar mutane”. Tun daga lokacin ne aka riƙa kiran Fulani Mariya da laƙabin Maiharara. Laƙabin ya yi tasiri matuƙa, har ya zama duk mai suna Mariya sai ana kiranta Maiharara ko ma a taƙaita da Harara, saboda kara irin ta fada. Daman fada suna da irin wannan salo na saka wa mutum wani suna idan suna jin nauyin faɗar sunansa kai-tsaye.

f. Maikano: Alkunya ce da Kanawa suke yi wa Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo. An yi masa alkunyar ne saboda sakaya sunansa na yanka, sakamakon kwarjininsa da himmarsa da ƙwazonsa da cika alƙawali da riƙon amana da jaruntaka, waɗanda suka taimaka masa wajen daɗa inganta mulkin Kano tare da ƙara kyautata shi. Ya kuma tsaida da mulki mai ƙarfi kamar mahaifinsa Malam Ibrahim Dabo. Wannan ya sa akan yi masa kirari da cewa:” Abdullahi dagi maganin ƙasa mai tsauri”. An sami cigaba a zamaninsa, Kano ta bunƙasa sosai, ta hanyar cinikayya, addinin Musulunci ya daɗa inganta da bunƙasa, bai zauna ba sai da ya kafa mulki mai adalci, ƙasa ta yi daidai (Waziri, 2008 p. 53-5). Sakamakon haka ne aka yi masa alkunya da Maikano (Dokaji, 1978 p. 47).

g. Maikaturu: Alkunya ce da ake yi wa Sarkin Musulmi Abubakar Atiku na 1, wanda ya jagoranci Daular Usmaniyya daga 1837 zuwa 1842. An yi masa alkunyar ne saboda a Katuru Allah Ya yi masa wafati (rasuwa). A can aka yi masa kabari, kamar yadda Sokoto, (2014 p. 392) ya nuna. Mai takwaran sunansa (Abubakar) akan kira shi da Maikaturu, saboda kunyar faɗar sunansa, domin jin nauyin ambaton sunan.

h. Maiƙaura: Alkunya ce da aka yi wa Sarkin Musulmi Umaru ɗan Aliyu Babba (1881 -1891), saboda ya rasu a garin Ƙaura Namoda, aka yi masa kabari a can. Sakamakon haka ne akan kira mai suna Umaru da laƙabin Maiƙaura saboda jin nauyin faɗar ainahin sunan.

i. Maisango: Alkunya ce da ake yi wa Sarkin Kano Aliyu, saboda shi ne sarki na farko da ya fara amfani da wani makami da ake kira sango a ƙasar Hausa. Don haka duk mai suna Aliyu ana yi masa laƙabi da Maisango a Kano. Irin wannan alkunyar ta shafi abubuwan da ake amfani da su. Misali, Allura ana kiranta maɗinkiya, saboda sunanta ya so ya yi kama da sunan Sarkin Kano Alu, kamar yadda Sufi (1993 p. 86).

j. Maishinaka:Alkunya ce da ake yi wa Sarkin Musulmi Aliyu Babba ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. An naɗa shi Uban ƙasar Shinaka a matsayin Durumbun Shinaka. Yana bisa wannan matsayin ne aka ba shi sarautar Sarkin Musulmi. A garin na Shinaka ya wanzar da tsare-tsare masu amfani. Sakamakon kunyar faɗar sunansa na yanka aka rinƙa kiran duk mai suna Aliyu da laƙabin Maishinaka a ƙasar Sakkwato.

k. Maisunan Malam: Alkunya ce da ake yi wa mai suna Ibrahim, saboda sakaya sunan Sarkin Kano Ibrahim Dabo kamar yadda Sufi (1993 p. 86). Haka kuma, an yi masa alkunya da Cigari saboda ya yi yaƙe-yaƙe da dama inda ya cinye garuruwa. Hasali ma, duk inda ya fuskanta ba mai iya taron sa. Wannan ne ya sa mutane suka yi masa laƙabi da Saifullahi Cigari kamar yadda Waya (2000 p. 39) ya kawo. Daga baya ne aka taƙaita laƙabin zuwa Cigari, inda ake laƙaba wa mai suna Ibrahim, wanda hakan ya kasance sakayawa ga sarkin Kano Ibrahim Dabo.

l. Maiturare: Alkunya ce da aka yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu (1915 – 1924). Ana kyautata zaton an yi masa laƙabin ne sakamakon yawan tu’ammali da yake yi da turare. Saboda shi mutum ne mai zarafi (dukiya).

Irin wannan alkunyar a ƙasar Hausa ba ta tsaya kawai ga sunayen mutane da abubuwa ba, har ma ta shafi lokacin da mace ta haihu, wanda ya sanya mace ba ta faɗar sa’ar haihuwarta, saidai ta kira ta mutumin, idan namiji ne, mutumiyar, idan mace ce.

Haka kuma a sakamakon auratayya da ta auku a tsakanin Hausawa da Fulani, ya wanzar da ƙarin wani fagen shigowar wasu sunaye ga al’ummar Hausawa. Misalai daga cikinsu sun haɗa da:

a. Baba: Uba.

b. Babandi: Laƙabin da ake yi wa wanda aka raɗa wa sunan kakansa, daidai yake da Babando ko Babangida.

c. Bello: Wanda ke nufin mataimaki.

d. Ɓoyi: Yaron da aka haifa bayan mahaifiyarsa ta yanke ƙauna daga samun haihuwa. Mace kuwa ana kiranta Nebi.

e. Buwa: Yana nufin mai shanu.

f. Cisob: Wanda mahaifinsa ya ƙara aure yana ciki kafin haihuwarsa, idan mace ce aka haifa sai a kira ta Susi.

g. Dada:Uwa.

h. Dikko: Ɗanfari, mace ko namiji.

i. Dudu:Wadda aka haifa bayan haihuwar ‘ya’ya maza da dama (masu yawa).

j. Giɗaɗo:Yana nufin abin ƙauna.

k. Ige: Wadda aka haifa bayan maza.

l. Inna:Laƙabin da ake yi wa yarinyar da aka raɗa wa sunan kakarta.

m. Iri: Yaro ko yarinyar da mahaifinsa/ta ya rasu kafin haihuwarsa/ta.

n. Jaɓɓi: Wanda ko wadda aka haifa ranar da aka yi baƙo ko lokacin da baƙo zai zo.

o. Jaɓɓo: Sannu da zuwa.

p. Juli: Wanda aka haifa ranar Idi.

q. Lamiɗo: Wanda aka haifa bayan babansa ya samu sarauta, a wasu wurare shi ake kira Riskuwa.

r. Macciɗo:Wanda aka haifa ya rayu bayan wasu suna rasuwa. Mace kuwa ana ce mata Aberta ko Joda.

s. Manga: Laƙabin da ake yi wa mai suna Muhammadu.

t. Nene: Yaya mace.

u. Sajo: Wanda aka haifa bayan haihuwar tagwaye.

v. Sambo: Laƙabin da ake yi wa mai suna Muhammadu. Kuma ana yi wa ɗa na biyu da aka haifa laƙabin Sambo, yana kuma daidai daTabari (CNHN, 2006 p. 387).

w. Sumaye: Wanda ko wadda aka haifa cikin azumi.

x. Tabo/Modiyam: Wanda ko wadda aka haifa lokacin malka.

y. Wakkala: Wanda ko wadda aka haifa mahaifiyarsa/ta ta rasu bayan haihuwarsa/ta.

z. Woɗi: Yarinyar da aka haifa kyakkyawa.

aa. Yuguda: Wanda aka haifa bayan haihuwar jerin ‘ya’ya mata masu yawa.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments