Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Laƙubban Sunaye Masu Nuna Aukuwar Abubuwa
Akan yi wa abin haihuwa laƙabi ta la’akari da zuwan haihuwar a lokacin faruwar wani sha’ani. Wato, wata hidimar rayuwa kamar nuna farin ciki dangane da bikin aure ko naɗin sarauta ko salla. Irin waɗannan lamurran kan wanzar da nishaɗi ko sheƙe-aya tare da watayawa a tsakanin al’umma. Aukuwar haihuwa a irin waɗannan lokutan shi ya haifar da laƙubba kamar:
a. Ango: Wanda aka haifa ana
shagalin bikin aure. Mace kuwa ana yi mata laƙabi da Amarsu ko Amare.
b. Gagarau: Wanda aka yi ƙoƙarin
zubar da cikinsa abin ya buwaya.
c. Kilishi: Wanda aka faifa dab
da samun sarautar mahaifinsa. Wannan suna ya kasance suna ne na tarayya domin
ana kiran namiji da mace da shi.
Laƙabi ta
Lura da Zuwan Haihuwa
Sau da yawa, al’ummar Hausawa kan
ba abin haihuwa suna ta hanyar mayar da hankali ga halin da haihuwar ta auku.
Wannan ne ya samar da sunayen da suka haɗa
da:
a. Ɓoyi: Wanda aka haifa bayan an ɗauki tsawon (dogon) lokaci
ba a haihu ba.
b. Daɗe: Wadda aka haifa bayan iyayenta sun yi
shekaru da dama ba su sami haihuwa ba. A wasu ƙasashen Hausa kuwa akan kira ta Samu.
c. Daran-Tuwo: Laƙabin
da ake yi wa wanda aka haifa bayan mahaifiyarsa ta ɗauki tsawon lokaci ba ta samu haihuwa ba.
Wato, sai bayan ta manyanta, ta samu juna-biyu aka haife shi.
d. Dimajo: Wanda aka haifa bayan
an auri mahaifiyarsa a yayin da take baiwar wani, daidai da Bacucane (CNHN,
2006 p. 103).
e. Farke: Wanda aka haifa a
lokacin da mahaifinsa ya tafi fatauci. A wani karin harshen akan ce Falke.
f. Kyauta:Ɗanfarin da tsohuwar mace
ta haifa.
g. Rabo: Ɗa ɗaya tilo da mace ta haifa a tsawon rayuwarta
ta aure, mace kuwa ana ce mata Raboci.
h. Tunau: Wanda aka haifa bayan mahaifiyarsa ta ɗauki tsawon lokaci rabonta da haihuwa. Wasu kan kira shi Tune. Mace kuwa su ce Tuni.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.