Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Al’ummar Hausawa sukan sa wa ‘ya’yan da aka haifa musu sunaye ta kula da wata rashin jituwa da ta auku da kan haddasa rabuwar aure idan ba a kai zuciya nesa ba. Wasu lokutan kuma shigar juna biyu kan zama sanadin sasantawa. Wani zubin kuwa sai an haihu ɗin ne akan sasanta. La’akari da irin wannan halayyar ne Bahaushe ya tanadi sunaye da suke nuni ga yadda yanayin yake kafin ko bayan an haifi abin haihuwar. Wannan ne ya samar da sunaye kamar:
a. Dawai: Yaron da aka saki
mahaifiyarsa da ciki, sai ta haife shi bayan ta yi wani aure.
b. Gwanda: Laƙabin
da akan yi wa wanda shigar cikinsa ya hana mutuwar auren mahaifiyarsa. A wasu
sassan garuruwan ƙasar Hausa akan kira shi da Sadau.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.