Alummar Kanuri sun shahara wajen raɗa wa ‘ya’yansu sunayen Sahabban Annabi S. A. W., musamman ma na khalifofi shiryayyu. Wato, Abubakar, Umar, Usmanu da Aliyu. Waɗannan sunayen suna ƙunshe da ma’anoni na musamman a harshen Larabci. Al’umma sun fi mayar da hankali ga kwarjinin masu sunayen na asali, saboda gudummawar da suka bayar wajen haɓaka addinin Musulunci. Irin waɗannan sunayen al’ummar Kanuri ta yi musu laƙabi na musamman da take kiran waɗanda suke amsa su. Misali:
Jad. na 30: Sunayen da Kanuri Suka Samo Daga Sahabbai
|
|
Suna |
Laƙabi |
|
1. |
Abubakar |
Aboorand,
Garwa, Garbai, Kawai |
|
2. |
Umar |
Bunu
(taƙaita “Ibn Khatab),
Sanda, Gasau, Yarema |
|
3. |
Usman |
Ngari |
|
4. |
Aliyu |
Garga |
|
5. |
Abu-Talib |
Butali |
|
6. |
Ƙassim |
Kashim |
Ta fuskar sunayen mata kuwa, akwai matan Annabawa
da suka yi imani kuma suka taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa addinin Allah a doron ƙasa. Waɗannan mata al’ummar Kanuri sukan yi amfani da sunayensu wajen raɗa wa ‘ya’yansu. Hasali
ma sun yi wa irin waɗannan sunaye laƙubba kamar
yadda za a gani ɗaya
bayan ɗaya:
Jad. na 31: Sunayen Mata a Kanuri Daga Sunayen Muhimman
Mata a Tarihin Musulunci
|
|
Suna |
Laƙabi/Laƙubba |
|
1. |
Aminatu |
Sato |
|
2. |
Khadijatu |
Banna |
|
3. |
A’ishatu |
a. Boli b. Maida c. Mali |
|
4. |
Halimatu |
a. Kula b. Kodo c. Kawudi |
|
5. |
Hafsatu |
a. Mara b. Kawul c. Kawule d. Kalu |
|
6. |
Fatima |
a. Batul b. Botula c. Busam d. Fusam e. Fandau f.
Koshi g. Kului h. Lefa i.
Lewa j.
Dungule |
|
7. |
Hauwa’u |
a.
Mada b.
Madari |
|
8. |
Ruƙayyatu |
a. Ruwaya b. Arkwaya |
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.