Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Annabi, shi ne wanda aka ba annabta. Ita kuwa annabta, tsani ce tsakanin mahalicci da halittunsa domin isar da shari’o’insa a doron ƙasa. Yana bayar da wannan matsayi ne ga wanda ya so, ya kuma zaɓa daga cikin bayinsa. Allah Yana cewa:
Allah Yana zaɓar manzanni daga Mala’iku kuma daga mutane, haƙiƙa, Allah mai ji ne, maigani (22:75).
Annabta baiwa ce daga Ubangijin sammai da ƙassai, ba nemanta ake ba, ba a kuma samunta ta hanyar yawan ibada ko ɗa’a ga Allah. Hasali ma ba zaɓin wanda aka ba annabtar ba ne, ko nemansa, sai dai keɓanta ce da darjewa daga Allah Mabuwayin Sarki Maɗaukaki. Allah Yana cewa:
…Allah Yana zaɓen wanda yake so zuwa gare Shi, kuma Yana shiryar da wanda Yake tawakkali gare Shi, ga hanyarSa (42:13).
Allah Ya kammala manzanninsa da kyawawan ɗabi’u tare da kiyaye su daga shubhohi da sha’awowi domin su zama abubuwan koyi nagari ga sauran al’ummomi. Allah Yana cewa:
Waɗancan ne Allah Ya shiryar, saboda haka ka yi koyi da shiriyarsu. . . (6:90).
A wata surar kuwa Allah cewa Ya yi:
Haƙiƙa kyawawan abin koyi a gare ku ya tabbata a cikin lamarinsu. . . (60:6).
Annabawan Allah su ne mafi kamalar mutanensu a halittun jikunkunansu da halayensu, an kuma kare su daga afkawa cikin zunubai tare da kuɓutar da su daga dukkan wani aibu.
Sunayen Annabawa, an samo su ne daga cikin Alƙur’ani Maitsarki. A cikin alƙur’ani an kawo sunaye guda ishirin da huɗu (24) kamar haka:
Adamu, Alyasa’u, Ayuba, Dauda, Haruna, Hudu, Ibrahimu, Idris, Iliyas, Isa, Is’haƙa, Isma’ila, Lutu, Nuhu, Zulkifilu, Muhammad, Musa, Hudu, Salihu, Shu’aibu, Sulaiman, Yahya, Yaƙub, Yunusa, Yusuf, da kuma Zakariya’u.
Al’ummar Kanuri (Barebari) suna sanya wa ‘ya’yansu irin waɗannan sunaye kai-tsaye ko su yanke (gutsure) wani sashen kalmar sunan su yi amfani da gutsuren don taƙaitawa.
Binciken Waziri (2000 p. 15) ya bayyana cewa, akwai wasu jerin sunayen Annabawa da ba kasafai al’ummar ke raɗa wa ‘ya’yansu su ba. Irin waɗannan sunayen sun haɗa da:
Alyasa’u, Hudu, Ilyasu, Lutu, Nuhu, da Zulkifil. Duk da yake bai bayar da musabbabin rashin amfani da sunayen ba.
Ta fuskar sunayen annabawa da suke sa wa ‘ya’yansu kuwa, sukan ba su na musamman a cikin harshen Kanuri wanda suke kiran su da shi. Misali:
Jad. na 28: Sunayen Kanuri da Suke da Tushen na Annabawa
| Suna | Laƙabinsa a Kanuri |
1. | Adamu | Kontoko Kontoma |
2. | Ibrahim | YuramkoYurai |
3. | Idrisu | Mele |
4. | Muhammad | Dunoma |
5. | Musa | Karam |
Sun kuma yi ƙoƙarin gutsire wasu kalmomin sunaye suka gajarta su kamar yadda Hausawa sukan aiwatar ga wasu sunayen yanka na Musulunci. Misali:
Jad. na 29: Sunayen Kanuri Daga Gutsurarrun Sunayen Annabawa
| Suna | Ma’ana |
1. | Muhammad | Mamman ko Mammadu |
2. | Mustafa | Mutsi |
3. | Habibu | Habib |
4. | Ahmad | Hamat |
5. | Mukhtar | Tar |
6. | Ibrahim | Biri ko Burahim ko Bura |
Tushen Bayani: Waziri, (2000 p. 16-17)
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.