Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakubban Fulani Masu Nason Musulunci Da Girmamawa

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Laƙabi Tsakanin Fulani

Kowace al’umma ba za ta rasa wasu hanyoyin da takan bi ba wajen yi wa abin da aka haifa musu laƙabi ba. Kodayake irin waɗannan hanyoyi kan bambanta ne kawai a sakamakon bambancin harshe. Wasu lokutan al’ada da addini kan yi shige-da-fice wajen sanya laƙabi a tsakanin al’umma.

Laƙubban Nason Musulunci da Tarihi

Waɗannan nau’in laƙubba ne da ke nuna aukuwar wasu abubuwan tarihi a lokacin da aka haifi abin haihuwar, wato wanda ke karɓa sunan. Irin waɗannan sunayen na ishara ne ga rana ko lokaci (yanayi) da mai sunan ya zo duniya. Domin taskace bayanin yanayin da aka haihu ne ya sa Fulani ke yi wa ‘ya’yansu irin waɗannan laƙubban da haihuwar mai karɓa su ta auku. Misalai daga cikinsu sun haɗa da:

Jad. na 38: Samammun Sunayen Fulani daga Musulunci da Tarihi

 

Suna

Ma’ana

1.       

Altine

Wanda aka haifa ranar Litinin

2.       

Laaminde

Wadda aka haifa ranar Juma’a

3.       

Julde

Wanda aka haifa ranar salla

4.       

Suumeye

Wadda aka haifa cikin watan Azumi

5.       

Maude

Wanda aka haifa ranar Juma’a

Laƙubban Girmamawa a Tsakanin Zamantakewar Al’umma

A kowace al’umma akan samu wasu hanyoyi da ake amfani da su wajen mutunta zamantakewar da ke tsakaninta, musamman ta haujin gabatar da zantuttuka. Su ma Fulani sun shahara ta wannan fannin. Wannan ne ya sa ba sa faɗar sunayen surukansu da ainahin sunansu nayanka, sai dai su yi musu laƙabi da:

a. Soomooje

b. Jammooje

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments