Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Bahaushe kan bai wa ‘ya’yan da aka haifa masa sunaye ta kula da kamannu da ƙirar jikin abin haihuwar, wato siffa mai kyau ta rashin nuna alamun tsufa ko kuma mai muni. Hasali ma dai yana sane da irin sauye-sauyen da ɗan’adam kan samu tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwa. Wannan dalili ne ya haifar da al’adar bai wa mutane sunaye ta la’akari da siffofi ko ƙirar jikinsu. Hakan ne ya wanzar da samun sunaye kamar:
a. Agwaidu: Sunan da ake sa wa
gajeriyar yarinya. A wasu yankunan ƙasar Hausa akan kira ta da sunaye
daban-daban da suka haɗa
da: Agwiduwa, ko Afire, ko Kumbulo. Namiji kuwa akan ce masa Gajere, ko kuma
Wada. A wasu wurare kuwa a ce Malam Dogo.
b. Ɓakutu: Wadda aka haifa da ƙiba ga
kuma uwa uba muni.
c. Cigoro: Wanda aka haifa da
jan-baki.
d. Cindo: Wanda aka haifa da
yatsu shida.
e. Ɗanja: Wanda aka haifa ja-jawur da shi. A
wasu sassan ƙasar
Hausa akan ce masa Jatau. Mace kuwa ana kiran ta ‘Yarja, ko Maija.
f. Doguwa: Wadda aka haifa da
sigar tsayi.
g. Dugurguji: Wanda ya kasance
gajeren mutum, kuma shi ake kira Wada, a wasu garuruwan ƙasar Hausa. A wasu sassan
kuma su ce, Malam Dogo. Haka akan ce masa Guntau a wasu wuraren ƙasar
Hausa.
h. Duna: Wanda aka haifa baƙi ƙirin.
i. Gadangama: Laƙabin
da ake yi wa kyakkyawar mace (Sufi, 1993 p. 316).
j. Gurso: Wanda bai da ƙira da
fasalin jiki mai ma’ana
da ke jan hankalin al’umma
har su ga sha’awarsa,
wato mummunan mutum.
k. Ƙarami: Wanda aka haifa da ƙaramin
jiki. Wasu kan kira shi da Jariri.
l. Kumatu: Wadda aka haifa da
kaurin kunci (Ibrahim, 1982 p. 136).
m. Kutumbi: Sunan da ake yi wa ƙaton
mutum gajere.
n. Maicibi: Wanda aka haifa da
babbar cibiya. Wannan laƙabin gama-gari ne, wato ana kiran mace da namiji da shi.
o. Maikaciya: Wanda aka haifa da
kaciya (kugunu).
p. Mairiga: Wanda aka haifa cikin
yanar (rigar) haihuwa. Mace kuwa ana kiran ta da Sutura a wasu garuruwan ƙasar
Hausa.
q. Ziza: Laƙabin da ake yi wa kyakkyawar yarinya.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.