Ticker

6/recent/ticker-posts

Samar Da Suna Ta La’akar Da Dorewar Rayuwar Abin da Aka Haifa

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Wata hanyar da Bahaushe ke amfani da ita wajen sanya wa abin da aka haifa masa suna, ita ce ta kirdadon (sanya wa a rai) ɗorewar rayuwarsa. Wannan yakan faru ne ta la’akari da kusantar daidaituwar zuwan haife-haifan da suka ba ta. Kamar ta fuskar aukuwar ɓari (zubewar juna-biyu ko raggwan-kaya) da mahaifiyar ta saba fuskanta.  A wasu lokutan akan sami aukuwar wasu ayyukan da suke da alaƙa da zuwan haihuwar. Wannan ne ya haifar da samuwar sunaye kamar:

a. Abarshi: Wanda aka haifa ya rayu bayan mahaifiyarsa ta yi ta haihuwar wasu kafin sa suna rasuwa. A wasu sassan ƙasar Hausa na Gabas, kamar Zazzau da wasu ana kiransa Ajuji, ko Mantau, ko Amantai, ko Dangana, ko Kyauta. Yayin da a Hausar Yamma ake kiran sa da sunaye kamar: Bawa, ko Bawale, ko Barau, ko Allabbari, ko Abara, ko kuma Jijji. Su kuwa Hausawan da ke sashen ƙasar Nijar sukan kira wanda ya girma wajen wata mace wadda ba mahaifiyarsa ba da laƙabin Bawa.

b. Abarta: Wadda aka haifa ta rayu bayan mahaifiyarta ta sha haihuwar ‘ya’ya suna mutuwa kafin ta. Ana kiran ta da mabambantan sunaye a sassan ƙasar Hausa, da suka haɗa da: Ajefas, ko Barauka, ko Barto, ko Nabara, ko Bayi, ko Kyauta.   A Hausar Yamma akan kira ta da sunaye kamar: Baiwa, ko Barmani, ko Taure, ko Araga, ko Yada, ko Ayashe ko Ayas, ko Ajuji, ko Nabara, ko Bayi. Duk waɗannan ‘ya’yan wabi ne. Kuma kowane yankin ƙasar Hausa da irin yadda suke kiran sunan. Shi ne ya sa aka kawo gwargwadon sunayen da muka samu damar kalato wa mai nazari.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments