Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Yanayi Ɗibar Kayan Amfanin Gona
Bahaushe yana ba lokacin da yake cire kayan amfanin gonarsa muhimmanci. Wannan ne ya sa yakan sa wa ‘ya’yan da ya haifa sunayen da suka dace da kayan da ake cirewa a zamanin. Kasancewar shi manomi ne na gaske da ke noma dangogin kayan gona. Wannan ne ya haifar da mabambantan sunayen da suka danganci kayan amfanin gona, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya kamar haka:
a. Cidawa: Wanda aka haifa a
daidai lokacin da ake girbin dawa. A wasu wurare kuwa shi suke kira Dawa ko
Dawi, ko Maidawa musamman a ƙasar Nijer. Yayin da Maguzawa kan kira
shi Cida.
b. Cirama: Wanda aka haifa a
daidai lokacin da ake cin rama.
c. Citumu: Wanda aka haifa a
lokacin da gero ya yi tumu, wato ya yi fari kafin ya bushe, a daidai lokacin da
ake gasa shi don cin marmari.
d. Ƙumbule: Wanda aka haifa lokacin da dawa
ke ƙunshi.
e. Maidamma: Shi ne wanda aka
haifa a daidai lokacin da ake ɗauko
damma daga gona.
f. Maigero: Wanda aka haifa a
daidai lokacin da ake girbin hatsi a gidansu. A ƙasar Sifawa kuwa, shi suke kira Maihatsi.
Yayin da wasu sassan ƙasar Nijer ke kiran sa Gerau.
g. Roro: Wanda aka haifa a
lokacin da ake roron wake. A wasu garuruwan ƙasar Hausa akan kira shi da Ciwake, wasu
kuwa su ce Maiwake. A ƙasar Mafara kuwa akan ce Ɗanmaiwake. Mace kuwa sai a kira ta
Taroro. A wasu wurare sukan ce Hanaroro, wanda ya kasance suna ne na tarayya da
ya haɗa namiji da
mace.
Yanayin Hunturu
Hunturu lokaci ne na ɗari, wato sa’ilin da sanyi
da hazo suka fi tsananta. Bahaushe kan ba ‘ya’yansa sunaye ta la’akari da cikin
irin yanayin hunturun da aka yi masa haihuwa, domin samar wa abin da aka haifa
masa laƙabin
da ya dace da yanayin. Sakamakon haka ne ya samar da waɗannan sunayen:
a. Buda:Wanda aka haifa a lokacin
iska mai sa hazo da ke wanzuwa a lokacin sanyi.
b. Shaɗari: Wanda aka haifa ana matsanancin sanyi, a
wasu yankunan ƙasar Hausa sukan kira shi Ɗari, mace kuwa ana kiran ta Taɗari.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.