Ticker

6/recent/ticker-posts

Samar Da Suna Ta La’akar Da Yanayin Yini

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Bahaushe kan ba abin da aka haifa masa suna ta la’akari da lokacin da haihuwar ta auku tun daga wayewar gari har zuwa tsakiyar dare. Sakamakon haka ne ya haifar da samuwar sunaye kamar:

a. Dare: Wanda aka haifa da tsakiyar dare ko da daddare, wasu kan kira shi Ɗandare. A wasu wuraren kamar Sifawa sukan ce Dari, wasu su ce Adare, Baƙo, ko Baƙondi, ko Baƙon-dare, mace kuwa ana kiran ta da sunaye kamar haka: Maidare, ko Baƙuwa.

b. Nahantsi: Wanda aka haifa da hantsi, wato lokacin da rana ta fito sosai kafin ta kai tsaka. A wasu garuruwan kai-tsaye suke kiransa Hantsi.

c. Ranau: Wanda aka haifa da rana. Mace kuwa ana kiran ta Tarana.

d. Sammako: Wanda aka haifa tun da sassafe, kafin fitowar rana.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments