Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Hanyar samar da sunaye a tsakanin al’ummar Hausawa kafin bayyanar Addinin Musulunci na dogara kacokam ta la’akari da yanayin da aka haifi jaririn ko jaririyar. Don haka a nan za a tarar cewa, yanayi na nufin halin da ake ciki, kamar: damina ko sanyi ko ƙoshi ko yunwa da sauransu. Da faruwar abun a lokacin da aka haifi yaro ko yarinyar, sai a sa sunan ta hanyar la’akari da yanayinsa. Sakamakon haka waɗannan sunayen da Hausawa kan sa wa ‘ya’yansu suke nuna yanayin aukuwar haihuwar mai sunan. Misali:
Bahaushe kan samar
da sunaye ga ‘ya’yansa ta duban yanayin da aka
haifi abin haihuwar a cikinsa. Misali:
a. Anaruwa: Shi ne wanda aka haifa a
lokacin da ake tsuga ruwan sama. A
wasu yankunan ƙasar Hausa
akan ce Ruwa, ko Makau. Wasu ma
sukan kira shi da Mairuwa, mace kuwa a kira
ta da Malka, ko Marka, a karin harshen Hausar Gabas. Hausawan ƙasar Nijar kuwa shi sukan kira Makau wato wanda
aka haifa lokacin da ake shata ruwan sama kama da
bakin ƙwarya.
b. Damana: A wani karin
harshen akan ce Damina, wasu kuwa su ce Damuna.
Damina wani yanki ne na yanayin shekara, lokacin
da ruwan sama ke sauka.
Lokacin damina ya kasu zuwa rukuni-rukuni dangane
da yadda ake samun saukar ruwan sama. Wannan ne ma ya wanzar da
samuwar mabambantan sunaye ga ‘ya’yan da aka haifa a lokutan da
ke tattare a cikin damana, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya:
c. Damina: Wanda ko wadda aka haifa
a lokacin damana. Sunan na iya kasancewa na tarayya,
wato ana kiran namiji da mace. Wasu kan taƙaita shi su ce Dama wanda mace da
namiji kan karɓa sunan.
d. Maifari: Shi ne wanda aka haifa a
lokacin da ake ƙamfar ruwan sama. Wato, lokacin ƙarancin ruwan sama a damuna da
ke haddasa bushewar amfanin gona.
e. Nashuka: Shi ne wanda aka haifa a
lokacin da ake shuka, mace kuwa akan ce mata ta Tashuka.
A Hausar yamma sukan ce Shibkau a madadin Nashuka.
f. Nomau: Shi ne wanda aka haifa a lokacin da ake noma, mace kuwa akan kira ta Tanoma.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.