Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Bahaushe kan yi la’akari da jerin jinsin abin da aka haifa masa wajen bayar da suna. Wato jinsin maza ne matarsa ta haifa masa kafin ta haifi mace ko mata ne tai ta haifa masa kafin ta haifi namiji. Duka abubuwa ne da yake amfani da su wajen samar da sunaye ga ‘ya’yansa maza da mata. Wannan ne ya wanzar da samun sunaye kamar haka:
a. Auwa: Yarinyar da aka haifa
‘yan biyu tare da namiji, (Ibrahim, 1982 p. 136).
b. Dangali: Wanda aka haifa shi
kaɗai tilo a ɗaki.
c. Delu: Wadda aka haifa a ɗakinsu bayan an sami
haihuwar jerin ‘ya’ya maza uku zuwa huɗu
jere da juna. A wasu garuruwan ƙasar akan kira ta da sunaye mabambanta
kamar haka: Dela, ko Deluwa, ko Ige, ko Dudu/Duduwa, ko Kande, ko Baɗɗo, (Hausa/Fulani).
d. Gwamma: Wadda aka haifa a ɗakinsu bayan an haifi mata
da yawa, ana sa ran a haifi namiji, sai ta kasance mace. A wani yankin ƙasar
Hausa akan kira ta Hakama.
e. Kanta: Wanda aka haifa ‘yan
biyu tare da mace (Ibrahim, 1982 p. 135).
f. Leko: Wanda aka haifa bayan
haihuwar tagwaye (‘yan biyu). Wasu yankunan ƙasar Hausa akan kira shi da mabambantan
sunaye da suka haɗa
da: Gambo, ko Gambaji, ko Gado, ko Agada. A ƙasar Ɓurmi kuwa akan kira mai bi ma ‘yan biyu da laƙabin
Manga.
g. Tanko: Wanda aka haifa a ɗakinsu bayan haihuwar jerin
‘ya’ya mata uku zuwa huɗu.
a wasu yankunan ƙasar Hausa akan kira shi da mabambanta sunaye kamar haka:
Mato, ko Mati, ko Tankari. A wasu sassan ƙasar Zamfara akan kira shi Jigo, yayin da
a Arewacin Zamfara sukan kira shi Shinge. A tsakanin Hausa Fulani kuwa su ce
Guda ko Yuguda. Wasu kuma sukan yi masa laƙabi da Namata.
h. Tsakani: Wadda aka haifa bayan haihuwar maza da yawa aka kuma haifa mata ƙannai maza, sai ta kasance mai yayye da ƙannai maza.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.