Ticker

6/recent/ticker-posts

Rikon Amanar Iyayen Gidan Makada Ibrahim Narambada Tubali Isa

"Wai akan ce Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali Isa ya ɗara wa tsaransa ta ɓangaren riƙon amanar iyayen gida."

Masu wannan da'awar na ganin cewa, duk yadda Narambaɗa zai yi wa Basarake kiɗi da waƙa, bai cika wasa/ koɗa mutum ba yadda za ta wuce ta uban gidansa watau Sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa.

Misali a waƙar da ya yi wa Sarkin Zazzau Jafaru yana cewa:

"Ke Jakkadiya hwaɗa mashi baƙonshi ya zaka,

Ba baƙo ba na Narambaɗa na malamin kiɗi,

In an ce maraba mui ta kiɗi ham mu kwan bakwai.

Sarkin Gobir na Isa Amadu shi yak kira mu,

Na ji bayanin da yai muna,

Ban zauna ba naish shigo jirgi,

Sai hwaɗi nikai

Jirgi kai mu Zariya,

Kai dai kai mu lahiya bisa yadda Ubangiji,

Im mun jiɗa mun ga Jafaru mun bi da alkawai.

Abin lura a nan yana ƙoƙarin faɗa wa Sarkin Zazzau a kaikaice cewa ba wai don ya isa ba Ibrahim Narambaɗa ya zo wurinsa, a'a ya zo ne bisa ga umurnin uban gidansa.

Haka ma akwai wata waƙa da ya yi wa Sarkin Kiyawa na Ƙaura, yana cewa:

Ai da waɗan Moriki da Ƙaura,

Da mutan Moriki da Ƙaura,

Da sanin dattako da girma,

Da tsaran aikin ga na zamani,

In dai baka koma Isa ba,

Mai Ƙaura babu kamatai

A kalli yadda ya yi amfani da salo na kambamawa ga Sarkin Kiyawa na Ƙaura, amma sai ga shi Makaɗa Ibrahim Narambada ya waske inda ya nuna cewa duk waɗannan muhibba daga Amadu Sarkin Gobir na Isa sai Sarkin Kiyawa na Ƙaura.

Idan muka ɗauki a ƙalla tsaransa bisa ga misali Aliyu Ɗandawo da Salihu Jankiɗi, za mu ga inda suka kambama wasu fiye da iyayen gidansu. Misali a waƙar da Aliyu Ɗandawo ya yi wa Sarkin Yawuri.

Yana cewa:

"Mai Yawari bangon duniya,

Abdullahi sadaukin maza,

Allah Shi yai ma ɗaukakad da kowa ba shi da ita Hausa dut"

Abin lura a nan shi ne kamar yadda tarihin rayuwar Aliyu Ɗandawo ta gwada, uban gidansa na farko shi ne Sarkin Musulmi Sir Abubakar na III, amma sai ya tsallake zuwa Yawuri, ya tare can ya yi ta kambama Sarkin Yawuri fiye da Sarkin Musulmi Sir Abubakar na III.

Idan muka kalli   Salihu Jankiɗi a waƙarsa wadda ya yi wa Sarkin Kano Sanusi I, yana cewa:

"An yi ohis Kano Hawa biu

Lanjeriya arewa kwata,

Ba wanda ad da ohis haka,

Fanka ukku,

Hitila huɗu,

Nan wurin zaman Sarkin Kano,

Babban malami dag gabas,

Dag ga huskar arewa mata,

..............

Ga harabar zaman 'yan ƙara,

 ....................

....................

Ga katanga ta dutci ya yi,

Duh ya gyara gidan Alhaji,

Lallai mulki ya kammala,

............"

Abin lura a nan shi ne, Sarkin Musulmi Sir Abubakar na III ne ubangidansa. Amma a kalli irin yabo na kambamawa da ya yi ga Sarkin Kano. Ya nuna cewa duk faɗin ƙasar nan ta Nijeriya, babu irin ƙawataccen gida da ofis irin na Sarkin Kano.

Ibrahim Narambada Tubali

Post a Comment

0 Comments