Ticker

6/recent/ticker-posts

Tagwan Wasula

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Tagwan Wasula

68. Wasulan Hausa su biyar na da tagwaye,

 Wasu dai kan zamo guda sai ka kiyaye,

 Gun furunci na sautukan kar a yi tauye,

 Biyu ne ke zuwa a tare kuma goye,

Biyu aka tabbatar da su babu musawa.

 

69. Akan haɗa ‘a’ da ‘u’ a tare ga gwamawa,

 Haɗuwar ‘a’ da ‘u’ a nan ‘au’ muka cewa,

Yanzu a dubi ‘yan misalan ganewa,

Audi da gauɗe ga ko kalmar zaunawa,

  Audu a ɗauki auduga don aunawa.

 

70. ‘A’ kan ɗauri ‘i’ ya zan ‘ai’ ga rubutu,

 Yanzu a gwama sautukan nan ga karatu,

 Duba misalansu nan ƙasa don ka fahimtu,

 Mai rairaye ƙaiƙayi ƙwarai ya aikantu,

  Aikin in akwai kunu iya aikawa.

 

71. Abin sha’awa guda biyun nan na lura,

Sun ɗau hankalin mutane tun bara,

Kowa na da tasa hujja ƙwarara,

 Duk masana na Hausa manyansu da yara,

Ba su haramta ‘ai’ da ‘au’ gun zanawa.

 

72.  To masana da sunka yo duddubawa,

 Sun ga yana da kyau a ce an yi daɗawa,

 Don cike giɓin da anka yi mancewa,

 Wasu sun ka ce da ‘i’ da ‘u’ na sajewa,

Don su fitar da ‘iu’ ga sautin Hausawa.

 

73. Babu yawa a gun misalin wasalin nan,

 Shi ɗai ne barazana gun sautin nan,

 Duba misalin da zai biyo kan sautin nan,

 Motoci na ƙetare Turis ke nan,

  In sun zo uzurce fiu! Za su wucewa.

 

74. Akwai wani sauti guda a tsarin wasulanmu,

 In aka jera ‘u’ da ‘i’ ‘ui’ ta samu,

 A misalansa ‘yan ƙalilan harshenmu,

 Sai dai tunda har muna da misalinmu,

Wasu masana suna ganin ba a hanawa.

 

75. Kalmar nan sumui-sumui ya yi fitowa.

 Kalmar guiwa, kuiɓi duk sun ratsawa,

 To ma ga shi nan kirarin Hausawa,

 Yaro shi da goriba sai lasawa,

  Babba guiguya yakai sai cinyewa.

 

76. Ka ji tagwan wasal da ke nan harshenmu,

 ‘Au’, ‘ai’ har da ‘iu’ da ‘ui’ ga tsarinmu,

 Ai dukkansu sautuka biyu sun gwamu,

 In ka san waɗanga komai ya samu

  Su huɗu ne ka lura domin ƙirgawa.

 

Baƙaƙe Masu Ƙugiya

77. Hausa yawa gare ta in har muka duba,

 Sai a wuce a bar ka ma ba ka gane ba,

 Ma’ana za ta dulmuye ba sharri ba,

 Gagara Gwari mun shigo fasali babba,

  Baubawan mutum a nan aka ganewa.

 

78. Akan sanya ƙugiya a inganta rubutu,

 Hakan na sa a samu sauƙi ga karatu,

 Baƙaƙe da ke kama wasu kan bambantu,

Ma’anar ƙugiya alama ga rubutu,

A yi ‘yar lanƙwasa samansa ga zanawa.

 

79. Harafin ‘b’ yakan zamo ‘ɓ’ ga rubutu,

 In an saka ƙugiya a dole su bambantu,

 Ba wani jinkiri ga ajen karatu,

 Misali ɓarna, ɓari, haɓa ga ɓaɓatu,

  Ɓaɓura,[1] Ɓurmi,[2] ga ɓagas ga ɓaɓewa.

 

80. Ka san ‘ɓ’ ga wassula shi bai zaɓi,

 Dukkan wassula da an sa zai karɓi,

 Duba daɗin missal a nan mai ɗan gwaɓi,

 Ga ɓorai muna da kuiɓi ga Jaɓɓi,

  Ɓaɓatun ɓarawo sai ɓoyewa.

 

81. Sautin ‘d’ da lanƙwasa ‘ɗ’ aka ce mai,

 Ba a kiran sa ‘d’ zama an ɓata mai,

 Ma’ana za ta sha wuya don gane mai,

 Sai a yi lanƙwasa a huta malammai,

  Daɗin ɗanɗanar maɗi dai suɗewa.

 

82. Duba daɗin misalai kadan ba ka gane ba,

 Ya ɗale ɗakin Ɗayyabu da bai ɗamara ba.

 Ɗansanda ya ɗage ɗan da bai kauce ba.

 Ɗanlami ɗiyarsa matar Ɗanbaba,

Tai muna ɗegiyan ɗumamen karyawa.

 

83. ‘K’ ma na da lanƙwasa kui ganewa,

 Harafin ‘k’ da ƙugiya ‘ƙ’ aka cewa,

 Za ai lanƙwasa a fayyace su ga furtawa,

Shi ko lanƙwasa ka fayyace su ga dubawa,

  Ƙarshen ƙanjamau ga ƙato shurewa.

 

84. Ƙam-ƙam yara ke saye don taune shi,

Ƙolin ƙoluwar ƙuli na Baƙoshi,

Ƙwazo ya sha fura har ya yi gyashi,

 Ƙasimu ya ci ƙulƙule sai da ya ƙoshi,

Ƙanzon wanda yar rage yake ƙunshewa.

 

85. Baƙaƙe masu ƙugiya ke nan su du,

 Da akwai mai kama da su ɗin kumadu,

 A cucin ƙugiya akan sa masa shaidu,

 Harafin ‘y’ samansa nan za a yi shaidu,

  Don a yi ‘ya ta zana ‘ya’ya, ‘yantawa.

 

86. Je ka yi bita ka ji ƙarshen tsarin ga,

 Da ka gane su to ya kamata ka farga,

 Ba sa da yawa, ka gane su hakan ga,

 ‘Ɓ’, da ‘ɗ’, da ‘ƙ’ da ma ‘y’ ɗin ga,

  Su huɗu ke da ƙugiya gun Hausawa.

 

Tagwayen Baƙaƙe Masu Ƙugiya

87. Mun yi tagwan baƙi a baya ga tsarinmu,

Mun kuma bayyana a tsarin sautinmu,

Duk sharuɗansu mun faɗa na rubutunmu,

Akwai su ɓaro-ɓaro a duba aikinmu,

 Amma babu ƙugiya can ga fitarwa.

 

88. Harufa masu ƙugiyar na fa zamowa,

 Cikin tsarin tagwan baƙaƙe gwamawa,

 Sai ku biyo mu sannu mui yo leƙawa,

Yanzu a nana ƙugiya za mu sakawa,

Ga tagwayen baƙi ga bokon Hausawa.

 

89. In aka tsara ‘ƙ’ da ‘w’ ‘ƙw’ ce lura,

 Wasalin ‘a’ kaɗai ka bi na ba tara,

 Ƙwi, ƙwo da ƙwu duk kira su kurarra,

 Ga misalansu nan a kalma zan tsara,

  Ƙwazo ƙwadago ƙwarewa ƙwacewa.

 

90. ‘Ƙ’ in ta game da ‘y’ to ‘ƙy’ ke nan,

 Wasalin ‘a’ kaɗai ka bi nai a baƙin nan,

 ‘Ƙyi’, ‘ƙye’ ko ‘ƙyo’ ka san babu waɗannan,

 Sa natsuwa ka duba misalan nan:

Ƙyara, ƙyanƙyashe da ƙyasfi ƙyashewa.

 

91. Su biyu ke gare mu nan sai a kiyaye,

 Wato ‘ƙw’ da ‘ƙy’ ga tsari na tagwaye,

 Masana harsuna haɗa har da gwanaye,

 Sun yarda da su biyun kai ko a waye,

  Baya gare su ɗan’uwa babu daɗawa.


[1] Ɓaɓura ƙaramar hukuma ce da ke jahar Jigawa a Nijeriya.

[2] Ɓurmi ƙasa ce da ke cikin jahar Zamfara a Nijeriya. Ta malala har zuwa wasu yankunan jahar Sakkwato a Nijeriya. Ta haɗe yankin Bakura da wani yanki na ƙaramar hukumar Tureta da wani yanki na ƙaramar hukumar Tambuwal wato Jabo.

Post a Comment

0 Comments