Ticker

6/recent/ticker-posts

Daga Bakin Makada Salihu Alasan Jankidi Rawayya - Game Da Kafuwar Daular Usmaniya Da Zuwan Turawan Mulkin Mallaka

Jagora:

Hwarkon zaman Shehu cikin Gimbina

Jagora /Y/amshi :

Sai Magabci da Alkalawa,

Dag ga Alkalawa Gwandu,

Dag ga Gwandu sai Sihwawa,

Dag ga Sihwawa sai Sakkwato,

Yau rabon Usumanu da duniya,

Shekarash shi ɗari da sittin hadda biyab bisa an masu lange,

Ta inda an kabi an dawo nan,

Abinga Allah ya mai kai dashi,

Sarauniya ta yarda a bayas,

Sardauna an miƙa maka su dut,

Turawa saura bankwana,

Mai abin ya amshi abinai,

Turawa sai dai bankwana,

Mai abin ya amshi abinai,

Ga darajja Amadu Bello,

Da arziki na mazan jiya kayyi

Jagora :

Zak kuwat Turawa nan tudu

Jagora /Y/Amshi :

Shekara hamsin da tara,

Wurin da sun ka biyo Bidda,

Gwanga yayi hwaɗa da nasara,

Shekaras su biyab bisa daga,

Sai Kahin Ɗan Yamusa,

Magaji yayi hwaɗa da nasara,

Kwantagora garin Ibrahim,

Gwanga yayi hwaɗa da nasara,

Dag ga Zaria sai birnin Kano,

Koramaz Zorori wurin hwaɗa,

San Kano ya tarbi

nasara,

Sai Giginya an rafkewa,

Sakkwato sun yi hwaɗa da nasara,

A jama Giwa shi aƙ ƙarya,

Yara sai da rashin albarka,

Ga darajja Amadu Bello,

Da arziki na mazan jiya kayyi.

Wasu batutuwa ne☝️☝️☝️da Makaɗa Salihu Alasan Jankidi Rawayya wato Sarkin Taushin mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Sir Abubakar III ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Amirul muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo ya taskace wani sashe na Tarihin farkon kafuwar Daular Usmaniyya a farkon ƙarni na 19 da yadda Turawan mulkin mallaka na Ingila suka kassara ta a farkon ƙarni na 20, da yadda suka sake dawo da mulkin yankin Daular a hannun jikan jagoran assassata da sunan "Yancin kai na Nijeriya" a shekarar 1960 wato Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na ƙarshe ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II /Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi wanda shi ne babban jagoran Jam'iyyar NPC da ta fara kafa mulki a lokacin da su Turawan suka baiwa Tarayyar Nijeriya Yancin kanta, a cikin waƙar da yayi masa (shi Sardauna Sir Ahmadu Bello) mai amshi "Ga darajja Amadu Bello da arziki na mazan jiya kayyi".

Makaɗa Salihu Alasan Jankidi Rawayya ya bayyana wasu daga cikin wuraren da Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo ya zauna kafin da bayan kafuwar Daula. Gimbina gari ne da Mujahidi Abdulsalam ɗan Ibrahim ya kafa bayan tasowarsa daga ƙasar Gobir shiyoyin shekarar 1797(tsohon garin yana a cikin ƙasar Gwadabawa ta Jihar Sakkwato ta yau) wanda a lokacin zaman Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo a wurin ya kawo rashin jituwa tsakaninsu da masu mulkin Daular Gobir har ma ana ganin shi ne musabbabin ɓarkewar yaƙi a tsakaninsu a shekarar 1803/1804.

Makaɗa Salihu Alasan Jankidi Rawayya ya nuna cewa Mujaddadi ya zauna a wani wuri da ake kira Magabci ( a cikin yankin Dagawa ta ƙasar Yabo a Jihar Sakkwato ta yau) daga nan ya ce Shehu Usmanu Danfodiyo ya zauna a Alkalawa wato hedikwatar Daular Gobir da Sarkin Gobir Ibrahim Babari ya assasa bayan Gobirawa sun mamaye Daular Zamfara a shiyoyin 1764/67, bayan faɗuwar wannan gari ga hannun masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniyya shiyoyin shekarar 1808.

Ya ci gaba da cewa Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo ya zauna Gwandu (garin ƙanensa Malam Abdullahi Ɗanfodiyo) dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Gwandun Jihar Kebbi ta yau, daga nan kuma sai Sifawa dake cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Boɗinga ta Jihar Sakkwato ta yanzu kafin daga bisani ya dawo da zama a cikin birnin Sakkwato cibiyar Daular Usmaniyya inda ya yi wafati a shekarar 1817, Allah SWT ya jaddada masa rahama, amin.

A cikin waɗannan batutuwa da ya ambata kamar yadda muka kawo su a sama☝️, Makaɗin ya bayyana yadda Turawan mulkin mallaka na Ingila suka shigo wannan yanki ta kogin Binuwai suka zo Ida ( ta Jihar Kogi, yankin Nijeriya ta Arewa ta tsakiya) zuwa Bida ta Jihar Neja a shiyoyin 1897, har shigowarsu Keffi da Kwantagora da Zaria da Kano da Sakkwato da kuma irin gwabzawar da Sarakuna da al'ummar waɗannan ƙasashe suka yi dasu a tsakanin 1897 zuwa watan Maris na shekarar 1903 a lokacin da suka ci Cibiyar Daular Usmaniyya wato Sakkwato a filin daga na Giginya.

Bayan Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I ya bar Sakkwato a watan Maris na shekarar 1903 tare da wasu daga cikin jama'arsa riƙe da tutar jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniyya, Turawan sun bishi har sai da suka kashe shi a Ɓormi/Ɓurmi ta Ƙasar Funakaye dake cikin Jihar Gombe, Nijeriya a cikin watan Yuli na shekarar 1903 su ka ɗauke wannan tuta suka yi gaba da ita.

Sai gashi a shiyoyin shekarun 1958/59/60 a lokacin da suke shirye - shiryen baiwa ƙasar Nijeriya Yancin kai sun dawo da wannan tuta wanda Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello GCON KBE ya jagorance su zuwa wajen yayansa/wansa mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Sir Abubakar III suka miƙa masa ita(wannan tutar ta na nan a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi dake Sakkwato).

Wato "ta inda an kabi an dawo nan, an karɓe mulkin Daular Usmaniyya a yaƙin Giginya na Sakkwato a shekarar 1903 ta hannun kisan mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I, gashi a shekarar 1960 an baiwa Nijeriya yancin kai ciki kuwa har da yankin da ya ƙumshi mafi yawancin ƙasashen/garuruwan Daular Usmaniyya kuma ta hannun gwamnatin da wannan gwarzon jikan ma'assasin Daular suka kafa, "Sarauniya ta yarda a bayar, Sardauna an miƙa maka su dut, Turawa saura bankwana, mai abin ya amshi abinai".

A matsayinsa na Firimiyan Jihar Arewa tun daga Sakkwato har Adamawa shi ne shugaba, kenan Tutocin Shehu Mujaddadi duka suna ƙarƙashin ikonsa, Allahu Akbar! Haƙiƙa Makaɗa Sarkin Taushi Salihu ɗan Alasan ɗan Tigari mai abin kiɗa ya nuna ƙwarewa da fasihanci da zalaƙa da hikima da basira wajen taskace wani sashe na kafuwar Daular Usmaniyya da yadda aka ɗaiɗaitar da ita da kuma yadda gaskiya tayi halinta aka dawo da lamurran ga masu su na asali.

A wannan hoto Marigayi mai girma Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na ƙarshe  Alh. Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato ne.

Allah SWT ya jiƙan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Fiyayyen Halitta Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

Daga Alƙalamin:
Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji ) Jihar Zamfara, Nijeriya.
18/07/2026.

Post a Comment

0 Comments