Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamani Zo Mu Tafi: Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet (Shafukan Farko)

Citation: Sani, A-U. (2021). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

Zamani Zo Mu Tafi: Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet

ZAMANI ZO MU TAFI: AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET

NA

ABU-UBAIDA SANI
Email: abuubaidasani5@gmail.com ko official@amsoshi.com
Site: www.abu-ubaida.com
WhatsApp: +2348133529736

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan kundi ga masu neman sanin gaskiya, da rayuwa bisa gaskiya da riƙon amana, tare da wasiyya da riƙon gaskiya.

GODIYA

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai. Tsira da mincinSa su tabbata ga shugaban halitta manzon tsira Annabi Muhammadu da iyalansa da sahabbansa. Na gode wa Ubangiji da ya ba ni damar kammala wannan kundi cikin nasara.

Godiya ta musamman ga jagororin wannan aiki bisa namijin ƙoƙari da suka yi tare da jajircewa wajen tabbatar da wannan aiki ya kammala. Ba kammaluwar aikin ba kaɗai, sun tsaya tsayin daka domin tabbatar da aikin ya samu ingancin da ake buƙata:

a.      Dr. Yakubu Aliyu Gobir

b.      Dr. Muhammad Mustapha Umar

c.        Dr. Abba Almu

Allah Ya saka musu da mafificin alkairi.

Bayan haka, ina miƙa godiya ta musamman ga ɗaukacin malaman Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, musamman waɗanda suke Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Ina jinjina musu bisa namijin ƙoƙarin da suka yi na ganin mu ɗalibansu mun samu ilimi da tarbiyya nagartatta. Malaman Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da na sha daga tafkin iliminsu, su ne: Prof. BIRNIWA, Abdullah Haruna da Prof. AMFANI, Ahmed Haliru da Prof. DANTUMBISHI, Muhammad Abdulhameed da Prof. YAHAYA, Abdullahi Bayero da Prof. YAKASAI, Salisu Ahmed da Prof. DUNFAWA, Atiku Ahmed da Prof. BUNZA, Aliyu Muhammad da Dr. ABDULLAHI, Ibrahim Sarkin Sudan da Dr. USMAN, Bello Bala da Dr. ABDULLAHI, Isah Muhammad da Malam UMAR, Sama’ila da Dr. BUNZA, Dano Balarabe da Dr. MUSA, Shehu da Dr. MUHAMMAD, Mustapha Umar da Dr. IDRIS, Yahaya da Dr. IBRAHIM, Nazir Abbas da Dr. AMINU, Nasiru da Dr. BUNZA, Umar Aliyu da Dr. ABDULBASIR, Ahmad Atuwo da Dr. ABDULLAHI, Sarki Gulbi da Dr. RABI’U, Aliyu Rambo da  Malam MUKOSHY, Jamilu Ibrahim

Ina kuma gode wa iyayena (Malam Sani Abba, Malama Habiba Hamza (‘Yar’aljanna), da abokiyar zamanta Malama. A’ishatu Gambo) bisa ɗawainiyoyinsu kan dukkan abin da ya shafi rayuwata. Ina gode musu bisa addu’o’i da sauran nau’ukan gudummuwa da suke ba wa rayuwata tun daga haihuwa har zuwa yau. Ina addu’ar Allah Ya biya su da gidan Aljanna.

Daga ƙarshe, ina jinjina ga abokaina baki ɗaya. Abokan karatu sun ba da gudummuwa ƙwarai ta hanyar ƙarfafa guiwa da shawarwari da addu’o’in nasara. Ina kuma miƙa godiya ga dukkannin mutanen da suka ba ni gudummuwa komai ƙanƙantarta har wannan aiki ya kammala. Na gode. Allah Ya saka da alheri.

ƘUNSHIYA

SADAUKARWA - ii

CERTIFICATION - iii

GODIYA - iv

ƘUNSHIYA - vi

Abstract - xi

Tsakure - xii

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0 Shimfiɗa - 1

1.1 Dalilin Bincike - 3

1.2 Manufar Bincike - 5

1.3 Maƙasudi - 6

1.4 Tambayoyin Bincike - 6

1.5 Muhimmancin Bincike - 7

1.6 Farfajiyar Bincike - 8

1.7 Hanyoyin Gudanar da Bincike - 14

1.8 Kalmomin Fannu - 18

1.9 Naɗewa - 20

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 Shimfiɗa - 21

2.1 Bitar Muhimman Batutuwa - 21

2.1.1 Intanet - 21

2.1.1.1 Duniyar Intanet Jiya da Yau - 24

2.1.1.2 Intanet a Kadadar Hausa da Hausawa - 32

2.1.2 Al’ada - 38

2.1.3 Tasirin Intanet a Kan Al’ummomi da Al’adunsu - 42

2.2 Bitar Ra’i - 48

2.3 Bitar Ayyuka Masu Dangantaka ta Kai Tsaye da Aikin - 63

2.4 Hujjar Ci Gaba da Bincike - 72

2.5 Naɗewa - 73

BABI NA UKU

BUNƘASAR AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET

3.0 Shimfiɗa - 74

3.1 Intanet da Taskace Al’adu - 74

3.2 Intanet da Al’adun Hausawa - 76

3.2.1 Intanet da Bayyanannun Al’adun Hausawa (Fasahar Hannu) - 77

3.2.1.1 Intanet da Wasannin Hausawa - 77

3.2.1.2 Intanet da Abincin Hausawa - 79

3.2.1.3 Intanet da Gine-Ginen Hausawa - 81

3.2.1.4 Intanet da Sana’o’in Hausawa - 83

3.2.1.5 Intanet da Suturun Hausawa - 84

3.2.1.6 Intanet da Magungunan Hausawa - 86

3.2.1.7 Intanet da Bukukuwan Hausawa - 87

3.2.2 Intanet da Ɓoyayyun Al’adun Hausawa (Fasahar Baka) - 89

3.3 Amfanin Intanet ga Hausa da Hausawa - 90

3.4 Aibin Intanet ga Hausa da Hausawa - 99

3.5 Naɗewa - 107

BABI NA HUƊU

NASARORI DA ƘALUBALEN KAFAFEN INTANET NA HAUSA

4.0 Shimfiɗa - 108

4.1 Kafafen Intanet na Hausa - 108

4.1.1 Ƙamusu - 113

4.1.2 Labarai - 114

4.1.3 Sadar da Zumunta - 116

4.1.4 Kimiyya da Fasaha - 117

4.1.5 Makaranta - 118

4.1.6 Adabi - 119

4.1.7 Kasuwanci - 120

4.2 Ƙalubalen Bunƙasar Kafafen Intanet na Hausa - 121

4.2.1 Saɓa wa Al’adu - 122

4.2.2 Kurakuran Rubutu Barkatai - 124

4.2.3 Ƙarya - 126

4.3 Dalilan Koma-Bayan Kafafen Intanet na Hausa - 127

4.3.1 Muhalli - 127

4.3.2 Ƙarancin Tallafi da Ƙarfafa Guiwa - 127

4.3.3 Yanayin Intanet - 129

4.3.4 Ƙin Karɓar Sauye-Sauyen Rayuwa - 130

4.3.5 Rashin Ingantattun Injunan Gyara Rubutun Hausa - 132

4.3.6 Baƙaƙe Masu Ƙugiya - 135

4.3.8 Rashin Ilimin Amfani da Kafafen Intanet Daga Ɓangaren Hausawa - 136

4.4 Naɗewa - 136

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 Taƙaitawa - 138

5.1 Sakamakon Bincike - 140

5.2 Shawarwari - 143

MANAZARTA - 149

MANAZARTAN INTANET - 163

KAFAFEN INTANET DA AKA ZIYARTA - 165

WAƊANDA AKA YI HIRA DA SU - 168

RATAYE - 169

Abstract

The internet has become an indispensable aspect of human life. Today, if the internet should cease to exist for just an hour, the magnitude of catastrophic consequential loss that will follow is unimaginable. Several academic fields and languages have wholeheartedly embraced the internet. Hausa is one of the developing languages on the internet. By the end of 2020, there were at least 44 highly visited Hausa websites with diversed contents and high online visibility. On this basis, research works should be conducted about the Hausa on the internet to ascertain the current situation and scenarios as well as to see to the improvement of same. The objectives of the research are to study the (i) Hausa culture-based internet contents, (ii) the attainments and challenges surrounding Hausa websites and blogs, and (iii) determining sustainable measures for enriching and dissemination of Hausa culture-based contents on the internet. The scope of the study is limited to Hausa culture within the domain of the internet. The study methodologically used interviews and online textual analysis in obtaining the research data. Platonism is adapted as a theory that guides the research, on the basis of which the research opines the existence of a physical world and an incorporeal world – the latter being the internet. It is also based on the Hausa philosophy that “zamani riga ce” (change before you have to), which emphasizes that the Hausas should embrace and utilize the internet as a precaution to being poorly represented. The research confirms that today, nothing can be successful and earn global recognition and acceptance without the help of the internet. It also realizes that, though the Hausa culture is spreading more on the internet, Hausa websites and blogs face a lot of challenges one of which is inadequate knowledge of the language by the websites and/or blogs administrators. Finally, the research offers some recommendations among which one is that the individuals and authorities concerned - including agencies, departments, instructors, and researchers - should make efforts to ensure adequate representation and presentation of Hausa on the internet.

Tsakure

Tuni intanet ya zama wani ɓangaren rayuwar ‘yan’adam. A yau, ba za a iya ƙiyasin mizanin ɗumbin munanan matsalolin da za su auku ba idan aka ce babu intanet daidai da minti guda. Ɓangarorin ilimi da harsuna da dama sun rungumi alamarin intanet kain-da-nain. Hausa na ɗaya daga cikin harsunan da suke tasowa a duniyar intanet. A zuwa ƙarshen shekarar 2020, akwai a ƙalla manyan kafofin intanet na Hausa guda arba’in da huɗu (44). Lura da haka, ya zama dole a gudanar da nazarce-nazarce a wannan fanni domin daidaita al’amarin wanzuwar Hausa a duniyar intanet. Maƙasudin wannan bincike shi ne nazartar (i) yanaye-yanayen al’adun Hausawa cikin duniyar intanet da (ii) ci gaba da ƙalubalen da ke dabaibaiye da kafafen intanet na Hausa, da kuma (iii) hanyoyi da matakan amfani da intanet wajen bunƙasawa da yayata aladun Hausawa. Farfajiyar binciken ba ta wuce al’adun Hausawa da ke cikin duniyar intanet ba. An yi amfani da manyan hanyoyi biyu domin gudanar da binciken. Hanya ta farko ita ce hira. Ta biyu kuwa ita ce nazarta da ƙwanƙwance ƙunshiyar kafafen intanet kai tsaye. An yi amfani da rain Pulatoriyya (Platonism) wajen gudanar da binciken inda aka ɗauki intanet a matsayin duniya mai zaman kanta wanda kuma al’amuranta ke da alaƙa da abubuwan da ke gudana a duniyar yau da kullum. Sannan an yi amfani da hanyar ɗora aiki da ta dace da tunanin Bahaushe cewa “zamani riga ce.” Lallai kuwa ya zama wajibi Hausawa su taka rawar kiɗan zamani domin tabbatar da wakilcinsu a duniyar intanet bai faɗa hannun waɗanda za su masa riƙon sakainar kashi ba. Binciken ya tabbatar da cewa, a yau babu wani alamari da zai iya ci gaba, ya ɗaukaka, duniya ta san shi kuma ta karɓe shi, ba tare da an haɗa da intanet ba. Har ila yau, binciken ya gano cewa, tuni al’adun Hausa suka yaɗu a duniyar intanet. Bayan haka, ya fahimci cewa akwai matsaloli da dama da ke dabaibaye da kasancewar Hausa a duniyar intanet, ciki har da matsalolin da suka shafi ƙarancin ilimin Hausar ga masu gudanar da kafafen intanet na Hausa. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da hukumomi da malamai da manazarta, da su waiwaici al’amarin Hausa a duniyar intanet domin samar da kyakkyawan wakilci. 

Post a Comment

0 Comments