Ticker

6/recent/ticker-posts

Hangen Nesan East a Kan Rawar Tatsuniya Da Labari a Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa

Article Citation: Adamu Ibrahim Malumfashi (2019). Hangen Nesan East a Kan Rawar Tatsuniya Da Labari a Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 17, No. 1. ISSN 0794-9316

HANGEN NESAN EAST A KAN RAWAR TATSUNIYA DA LABARI A RUBUTACCEN WASAN KWAIKWAYON HAUSA

Na

Adamu Ibrahim Malumfashi
Ahamdu Bello University, Zaria
malumfashiadamu@gmail.com

Gabatarwa

Tatsuniya da sauran labarai sun taka muhimmiyar rawa a wajen samar da rubutaccen wasan kwaikwayo na Hausa da kuma bunƙasarsa. Ma fi yawan wasannin da ke cikin littafin Siɗ Hausa Plays na Dr. R.M. East, littafin da aka buga a 1936 da bazarsu suka yi rawa. Wannan alaƙa tsakanin adabin baka da rubutacce gadadda ce. Masana irin su Osundare sun yi bayani a kanta tuni.

Marubucin Siɗ Hausa Plays, ko kuma SHP a taƙaice, ya nuna ya yi amfani ne da tatsuniyoyi da labarai domin ya nuna wa Hausawa, ko ma ya koya masu cewa su ma suna iya rubuta wasannin kwaikwayon ta yin amfani da adabin nasu. Kila East ya yi wannan koyarwa ce domin ya lura cewa duk da yake Hausawa sun fara nuna ƙwarewa da sha’awa wajen rubuta ƙagaggun littafai, amma babu mutum ɗaya da ya ga ya karkata wajen rubuta wasan kwaikwayo. Tunda yake East ba masanin ƙabli da ba’adin rubuta wasan kwaikwayo ne ba, sai ya nemi tallafi daga W.S de G. Rankin ya sanya shi a hanya, wanda da ma shi ne ya bayar da shawarar ya rubuta wasan kwaikwayo.

Za a yi mamaki yadda SHP ya zama angulu da kan zabo. (ko dai zabo da kan angulu?), domin kuwa wasanin da ke cikinsa duk da Hausa suke, amma kuma sunansu Banasare! Wannan hautsinawar ta ba manazarta damar faɗin albarkacin bakinsu. Wasu na ganin ko dai fassara shi aka yi daga Ingilishi? Wasu ma irin su Pwedon cewa suka yi ba East ne ya rubuta wasannin ba, a’a Abubakar Imam ne (1977:139, 154, 155, 157-8). Wannan ƙasida ba ta sayi wannan ra’ayi ba. Ta yi amanna cewa East ne marubucin wasannin, ya kuma sami tallafi daga W.S. de G. Rankin, da kuma wasu malamai kamar yadda shi da kansa ya faɗa (1936:10), kamar yadda wannan marubucin ya nuna a cikin wata ƙasida.

Ba East ne mutum na farko da ya rubuta wasan kwaikwayon Hausa ba. Bajamushen nan Dr. Rudolf Prietze kamar yadda bincike a yau ya nuna, shi ne na farkon. Marubucin ya samu wasu labaran Hausawa (alhali shi ko ƙasar ma bai zo ba) wajen wani falke Alhaji Ahmadu Kano a Tarabulus, ya kuma juya wasu daga cikin labaran zuwa wasannin kwaikwayo. Ta haka aka samu wasanni guda shida kamar yadda Ahmed ya tace su:

1. Turbar ƙudus wanda aka rubuta a 1898

2. ’Yan Matan Gaya, 1900

3. Tarihin Rabeh, 1902

4. Turbar Tarabulus, 1902

5. Wasan Gizo da ƙoƙi, 1910

6. Wasan Boka da Majinyaci, 1910

To amma fa, East ne na farko wanda da gangan ya rubuta wasannin kwaikwayo, kuma ya bi duk hanyoyin da suka dace domin ya koya wa Hausawa yadda su ma za su iya rubutawa. Ya duba, kuma ya hango cewa za su iya. Akwai jini a tsoka sai dai idan ba a yanka ba.

Hangen Nesa

A wata gabatarwa wadda ita ma East ya yi da Ingilishi, ya faɗi dalilan rubuta wasannin kwaikwayon. Ya kuma ƙara da cewa fatarsa ba ta tsaya ne kurum ga cewa Hausawa su shiga rubuta wasan kwaikwayo ba, a’a, su ma riƙa rubuta waɗanda suka fi nasa kyau (1936:5). Tunda gabatarwar da Ingilishi ta zo, bari waƙar a ji ta a bakin mai ita:

The object of these short plays is to suggest to Northern Nigerians a possible way in which their folk-lore and other stories might be dramatized. If, when they haɓe tried them, the idea appeals to them, it is hoped that they will then produce ɓery much better plays on their own lines…

Domin East ya tabbatar da cewa hangen nesansa ya zo kusa, sai ya rubuta wani dogon bayani wanda ya samo daga Rankin (1936:9-14), a kan yadda ake aiwatar da wasan kwaikwayo. Duk kuwa wanda ya koya maka yadda za ka yi wasan kwaikwayo, ai ya koya maka yadda za ka rubuta shi ne. Ga wasu daga cikin ƙa’idojin (guda goma) da Rankin ya ba shi. (1936:11-12).

1. Ka tada murya da kyau yadda kowa zai ji, amma banda ihu…

2. Kada ka juya wa ‘ya kallon baya sa’ad da kake Magana

3. A ɗauki abu ɗaya kaɗai da za a yi cikin lokachi, domin

4. A kada hankalin masu kallo ya rabu biyu.

5. Ku tuna fa wannan wasa ne kawai…

A kan zaɓen yan wasan kuwa ga abin da ya ce:

ZOMO: Da fari a zaɓi wani yaro ƙarami mai wayo da lafazi, wanda zai ɗauki matsayin Zomo.

MATAR ZOMO: Wanda zai ɗauki wannan ma yaro ƙanƙane ne, mai murya irin ta mata.

GIWA: Wani babban yaro kakkaura zai ɗauki wannan.

RAƘUMIN DAWA: Wannan ma babban yaro ne siriri in ya samu…

A wani wuri kuwa (1936:13), sai Rankin ya nuna ai ana ma iya tsarma waƙoƙi cikin wasannin. Amma fa kada su yi tsawo. Banda waɗannan ƙa’idoji goma na Rankin, sai kuma ya nuna wa East cewa ana kuma buƙatar jagorar dandamali. Shi ma wani jigo ne a harkar wasan kwaikwayo! Bari mu taƙaita da kawo misalin da ya bayar a kan wasan farko, “Wasan Gonar Zomo” (1936:15-16).

Misalin wurin da ake yin wannan wasa, gonar daji che. Sai a zaɓi wurin da aka ga zai fi kyau chikin makaranta, inda akwai itatuwa daga baya da sarari a tsakani wanda zai zama misalin gona. Sa’an nan a kafa bukkoki guda uku a bayan filin, ko a chikin itatuwa in akwai su, amma ba kurkusa da juna ba. Watau gidajen Zomo da na Giwa da na Raƙumin Dawa kenan. Na tsakiya shi ne na Zomo na gefe ɗaya na Giwa na gefe ɗaya na Raƙumin Dawa… a yi ƙoƙari a yi dabara yadda masu wasa za su bayyana kamar waɗanda suka zama matsayinsu. Misali: Zomo: a yi masa dogayen kunnuwa…

Duk wanda ya karanta Malam Inkuntum zai ga yadda aka kwaikwayi wannan tsari. Da yake kuma Rankin ya gwada cewa ana iya tsarma waƙoƙi a cikin wasa, sai aka nuna wasu daga cikin ginshiƙin ’yan wasan irin su Giwa, da Raƙumin Dawa da wasu Bi-Yarima kamar ’ya’yan Raƙumin Dawa suna waƙoƙi da kirari kamar haka: (1936:2, 23, 24-25).

Waƙar Giwa:

Ni sagagi, ni makasau

Ni ne kichibis, manya ginsau

Kowa biɗi, Giwa tarayya

Ya huche takaichin yin gayya

Waƙar Rakumin Dawa

Ni ga ni Amale gaban gayya

Lalle na fi gaban tarya

A taɓa a ji ni chizgari

Ni naman kai manyan tauri

Waƙar Zomo

Ina wutsiyarka ta yi nisa?

Sai ni na kai ta ƙasa!

Banza ne girman mahaukachi

ƙaramin mai wayo ya fi shi

ƙarfinsu masu ƙarfin fahari,

Kowa taka kunama ya ji gari.

Waƙar ’Ya’yan Giwa

Giwa ta wuche tarya,

Kilmau manyan gayya,

Garƙami bukkar daji!

Kowa tsaya mata ya ji!

Wane wanda ya isa?

Yanzu ta kashe shi ƙasa!

Waƙar ’Ya’yan Raƙumin Dawa

Amale! Kas dabaibuya!

Dogo mai kauda kaya

Kishimi mai wuyar bugu

Taka sannu ba bago!

Wutsiyarka ta yi nisa,

Lalle ba ta kai ƙasa!

Wasannin:

Wasan “Gonar Zomo”

Wasa na farko a littafin shi ne Wasan “Gonar Zomo” (15-28). Wasan ya bu&e da nuna Zomo yana ta ƙoƙari ya gwada wa matarsa cewa shi ma namiji ne, wanda kuma zai iya kulawa da matarsa kamar sauran mazaje irin su Giwa, da Raƙumin Dawa, domin dai kada ta bar shi. Bayan ta yi tafiyarta, sai Zomo ya sami Giwa suka yi yarjejeniya za su noma hurumin Zomo tare, idan wannan ya yi yau, wannan ya yi gobe. Sai kuma ya sami Raƙumin Dawa, suka yi irin wannan yarjejeniya. Bayan Giwa da Raƙumi sun gama aikin gona, sai Zomo ya tsara yadda ya ba su tsoro ɗaya, bayan ɗaya, suka gudu suka bar masa amfanin gonar. Kwamfa sai ga matarsa ta komo. Nan take ya nuna mata abin da ya noma. Ta yi mamaki, kuma ta yi magiya ya yi haƙuri ya yafe mata, za ta yi duk abin da ya ce. A saboda haka ita ce ma ta kwashe hatsin ta kai gida. Da ma bai iya jidewa.

Ga irin gardamar da mata da mijin suka yi kafin ta kwashe kayan (1936:27-8).

Matar Zomo: Kai ko da mafarki ban zachi za ka yi zuciya haka

 ba.

Zomo: To ga shi na ba mara ɗa kunya.

Matar Zomo: To sai ka yi haƙuri, ka san halinmu na mata.

Zomo: A’a ba ni haƙura. In yi aiki haka ba ki nan, sa’an nan yanzu

 ki komo ƙerere don ki chi amfani a huche? Amma kin chika

 rashin kunya (ya tura ta) tafi abinki. (Matar Zomo ta faɗi a

 gabansa tana kuka).

Zomo: To, maza ki jide waɗannan ki kai gida. (Ta shiga jidon hatsi

 da rawar jiki, Zomo ya bi ta yana taƙama).

Wannan wasa ya yi amfani da irin tunanin Hausawa kan waɗannan dabbobi ne. A tatsuniyoyi da labaran Hausawa da dama an nuna cewa Zomo ’yar dabba ce ƙarama amma mai &an karen wayo. Har ma an &auka Zomo bai bacci da dukkan idanuwansa rufe, sai dai ɗaya. Bayan yana jiran ko ta kwana. Ta haka aka samu kalmar “baccin zomo”. Su kuwa sauran dabbobin biyu manya, Bahaushe ya ɗauka cewa ba su da wayo. Huhun ma’ahu ne. Wai gafiya ma sai ta ja akalar raƙumi ta kai shi ta baro.

Wasa na biyu, “Gawa Huɗu” (29-33), ya rataya ne a kan wasu manyan dabbobin daji guda biyar. Tatsuniyoyi da labaran Hausawa sun nuna girma da muhimmanci, da ma ƙwari, na Zaki da Maciji da Kura da kuma Damisa, waɗanda aka nuna cewa gidansu ɗaya a wasan. ɗan wasan na biyar shi ne Dila, wanda ya gaya wa dabbobin nan cewa zamansu wuri ɗaya ba zai yiwu ba. Shi ya sa ma ya kira su “gawa huɗu”. Shi kuwa Dila wanda Hausawa ke kira “malamin dawa”, dabba ce mai wayo. Amma maimakon dabbobin nan huɗu su yi tunani a kan kalamin “masani” Dila, sai ma suka nemi su tozarta shi. Ga yadda karon su ya kwashe (1936:31).

Dila: Sannunku Gawa Huɗu

Zaki: Mene ne Gawa Huɗu?

Dila: Ku ne.

Damisa: Malamin banza! Ka soma haɗe-haɗenku na malamai! Tafi abinka.

Kura: Bar shi mana ya zo ya ga irin zamammu, wata kila bai taɓa ganin gari mai lafiya irin wannan ba.

Dila: Ke, ni mahaukachi ne, ina ganin mutuwa a sarari in kai kaina?

Machiji: Ya kamata ka faɗa mana dalilin, in ba zancen banza kake yi ba.

Dila: Ku dai girmanku na wauta ne, wa ya taɓa ganin sarakuna hu&u sun zauna wuri &aya, ba tare da talakawa ba?

Duk (su yi tsaki). Rabu da mu tsohon banza! (Dila ya tafi abinsa yana shewa. Suna ta yi da Dila a tsakaninsu).

Zaki: Kai kun ga tsofaffin zamani!

Damisa: Ai mahaukaci ne…

Da yake sarakunan nan, sun ƙi jin zancen mai hangen abin da kan je ya komo, a yayin da Dila ya komo yawonsa, sai ya iske dabbobin nan sun mutu. Sun kashe juna. Abin da ya fa&a ya tabbata. Maganar tasa kamar ta malaman birni. Ga abin da ya faɗa da ya komo ya ga haka (1936:33).

Dila: Sannunku, Gawa Huɗu (shiru ya daga murya. Sannunku Gawa Huɗu! (shiru dai) kai kuna barchi ne? Ba ku ji ina gaishe ku ba? (Ya guso ya zunguri ɗaya da sanda. Ba motsi) M! ko da na san a yi mutuwar kasko! Ya wuce abinsa).

Wasa na uku, “Baki shi kan yanka wuya” (1936:35-40), da na huɗu, “Larabgana”, (1936:41-54), ba su da alaƙa kai tsaye da tatsuniya. Kila bayan da marubucin ya yi wasanni biyu a kan tatsuniyoyi sai ya ga ya dace ya sauya salo ya rubuta waɗannan wasannin biyu masu ’yan adam a matsayin ’yan wasa, a maimakon dabbobi. Wannan kuwa zai sa a fahimci cewa ba fa sai da dabbobi ne kurum ake yin ’yan wasa ba.

An gina wasan “Baki shi kan yanka wuya” a kan (wasu) mutum uku. Ali da “abokinsa” Tanko, da wata budurwarsa wadda ba a ma ji ta ba, balle a gan ta a cikin wasan. An kuma nuna abokan sun $ata saboda budurwar! Wannan salo na yin amfani da ’yan wasa taƙaitattu, salo ne da zai taimaka wa mai koyon yadda ake rubuta wasan kwaikwayo cikin sauƙi, domin kuwa duk wanda ba gwani ne ba, ya cika wasansa da ’yan wasa tuli, to za su ba shi ruwa. Zai kasa sarrafa su, ya ba kowa dama ya taka rawarsa yadda ya kamata.

Shi kuwa wasan “Larabgana” akasin na ukun ne ta fuskar ’yan wasa. A nan mutanen gari aka tara. Akwai mabarata makafi su uku, waɗanda kowa ya gaji da ƙunatarsu. Akwai Sarki tare da manyan muƙarrabansa, tunda ba Sarkin caca ne ba. An kuwa gina “Larabgana” a kan wani camfi da ke nuna cewa akwai wata laraba a wani wata na musamman, wadda rana ce marar sa’a, saboda haka ba a son mutum ya yi wani abu a wannan rana. Amma shi ƙaramin cikin makafin, sai ya ƙaryata wannan magana, ya je bara, ya kuma ha&u da fitina, wadda ta biyo shi har gida ta shafi ’yan uwansa. Zance na ƙarshe da aka yi a wasan ya ƙara jaddada munin ranar (1936:54) “Ban ta$a ganin an ƙulla wani abin kirki ranar Larabgana ba”.

Wasa na biyar, “Makas Sarki” (55-67), an gina shi ne a kan labarin Bayajida, wanda wasu masana irin su Abubakar Sarkin Tarihin Fadar Daura (2007:10-13) suka ɗauka tarihi ne. Wasu malaman adabin Hausa kuma na ganin tarihihi ne. An nuna cewa Bayajida ya iso Borno, kuma shugabannin garin sun karɓe shi hannu bi-biyu, kafin ya gane ashe giri ne. A ci gaba da wasan, an gwada yadda ya gudu har ya isa Daura, ya kashe macijin da ake gani mai waibuwa. An kuma nuna ya auri mai mulkin garin Sarauniya Daurama, duk kuwa da cewa a al’ada, Sarauniya ba ta aure. Ga yadda aka yi neman auren. (1936:67).

Bayajida: A’a ba ni son rabin garinki.

Daurama: To me kake so in ba ka?

Bayajida: Ba ni son kome, sai ke nake so da aure.

Fadawa: Daidai ne!

Daurama: Shi ke nan na yarda (mutane su yi gudu, su juya su koma gaba ɗaya).

Dogarawa: Mun gode mun gode! A gaishe da Makas Sarki!

Shi ma wasa na shida, wasan “Yanka Masabki Baƙon Sanau” (69-80), irin wanda ya gabace shi ne. Wasa ne na labarin wani. A wannan wasa wanda aka yi a kan wani Sarkin Katsina mai suna Sanau da abokinsa Korau, wasa ne wanda ya nuna yadda abokin ya yaudari matar Sarkin, har ya yi galaba ya amshe sarautar garin, kuma ya halaka mijin da matar. Ga yadda wasan ya ƙare (1936:79-80).

korau: Ku jawo mai ɗaki (yara kaman huɗu su tafi su jawo ta a ƙasa, su kada ita a gaban Korau. Ya sa ƙafa ya take kanta. Ya aza wuƙa bisa wuyanta). Daga gareni ba za ki sake wa kowa makirchi ba. (Ya yanke ta ya miƙe tsaye) ku ji dalilin da ya sa na yanka mache nan. Ita ce ta yi makirchin da ta sache ƙirin Sanau har ta ba ni don kwaɗayin ɗan samun da nike ba ta. Ku kuma na baya wannan za shi zama gargaɗi gareku. Duk wanda ya aminche wa mache shi ga ta kanshi. Ni kuwa na yi umurni a feɗe ta a yi alli da ƙassanta, a ajiye don shi zama shaida da gargaɗi ga dukkan wanda za shi chi sarautar Katsina bayana. (Ya nufi gida, mutane duk su raka shi suna ta kiɗi).

Tabbatar Da Hangen Nesan

Tarihin Adabin Hausa ya nuna cewa wasannin kwaikwayon Malam Inkuntum da da Wasan Marafa, su ne wasannin farko da aka yi bayan SHP. Kuma kafin a buga su, musamman ma dai Wasan Marafa, an yi ta aiwatar da shi a wurare daban-daban, kamar yadda gabatarwar littafin ta nuna. (1956:0) “Mun yi wannan wasa a Midil ta Sakkwato sau da yawa. Kuma mun je Talata Mafara da Gusau da Ƙauran Namoda duk mun yi shi a cikin 1943”.

Idan aka duba wasan Malam Inkuntum aka ga irin cikakken bayanin da aka yi na jagorar dandamali, nan ma ana iya yanke hukunci a ce an sha gabatar da wasan tun kafin NORLA ta buga shi. (1954:1).

Bayanin Shirin Rabon Wasa Na I

Shi wannan filin wasa da ke a kan sura an shirya yadda za a yi amfani don &aukan rabon wasanni na cikin littafin nan. Za a kekkeɓe da zanaki a shirya wurin ’yan kallo waje ɗaya. Gidajen nan 3 da keɓewar da za a yi bayansu su za a yi amfani da su. Inda aka nuna cikin gari zana ɗaya ɗaya ne zai kewaye kamar bukkoki don a nuna gari. A yi bukkokin nan 2 sama ga bukkokin gari. Su ma cikin gari ne. Duk abin da za a yi sun isa.

Banda wannan bayani na gaba &aya sai kuma marubucin ya kawo jagorar dandamali a kan yadda za a yi fitowa ta &aya (kashi na ɗaya), wadda ya kira “Rabo I”. Ga yadda ya nuna (19:1).

A sami mutane don su zazzauna suna shawagi a cikin gari. A sami makaɗin ’yan mata da ɗan mu’abba su yi ta wasa. A sami buzaye ko wundaye a shimfiɗa a ƙofar gidan M. Katakoro, Malamai da littafai su gewaye. A waje ɗaya a shirya yara maza da mata suna karatu. Malam Lawali a tsakaninsu da bulala…

Ana iya bugun ƙirji a ce ko da ma Malam Inkuntum ne kaɗai wasan da Hausawa suka rubuta, ana iya cewa hangen nesan East ya tabbata. Hausawan ba su ba shi kunya ba. Malam Inkuntum cike yake da barkwanci da wasanni, ko zantuka iri-iri waɗanda ake yi tsakanin Bahaushe, wato ɗan riga, da Bamaguje Bahaushe arne, haka kuma a gefe guda ga wata rahar da ta shafi fulani. Ga yadda aka kwashe tsakanin Bamaguje da Liman, a lokacin da Bamaguje ya kawo ɗiyarsa ’Yarkudunu a ba Ladan sadaka (1946:6-7).

Bamaguje: Allah jiƙe Malam

Liman: Ah manyan Maguzawa, sannu da zuwa. Kaifa hal?

Bamaguje: A’a ni ba kafiri ne ba

Liman: Ai ba kafiri na ce ba, kaifal hal na ce. Larabci ne, ma’anarsa yaya ka ke?

Bamaguje: Towo! Ai ka san ni ban san Larabci ba, yi mini Hausa. Kai ni tafowa na yi da ɗiyata ’Yarkudunu in gwada ma ita don a ba yaron nan ɗan babban Malamin nan da ya mutu ita aure. Sadaka ko na ba shi.

Liman: (Yana murmushi, ya ga yarinya daƙwalwa guda, kyakkyawa). To madalla, abu ya yi, watau ka rigaya ka faɗa masa ko tukuna?

Bamaguje: Ban faɗa masa ba, amma dai shi na yi niyya

Liman: To Allah ya amsa

Bamaguje: Allah ya amshi me? So kake ta mutu halama?

A wannan ganawa an ga irin barkwancin da mutanen suka yi cikin hikima. Liman miyansa ya biya, amma bai nuna maitar a fili ba. Malami ne Bamaguje ya gane haka, shi ya sa shi ma ya cije, ya tsaya a kan cewa lallai ga wanda ya kawo wa sadaka! Ko me ya haɗa Bamaguje da yin sadaka? Oho! Idan aka duba zantukan za a iya cewa Bamaguje ne ya fara takalo zolayar nan. Bai ba Liman girmansa ba. Ya ma gaida shi yadda ake sa ran kowa zai yi, sai ya ƙiya, sai ya yi wasa da harshe irin yadda ƙur’ani ya nuna Yahudawa na yi in suna magana da Annabi Muhammad (SAW), su caɓa magana yadda suke so ba tare da an gane ba, idan ba an kai hankali nesa ba.

A cikin Alƙur’ani (2:104) kamar yadda Mohyidin ya fassara, Allah ya nuna yadda wasu Yahudawa suka riƙa amfani da wata kalmar Larabci wadda a harshensu tana da wata mummunar ma’ana. (1996:37).

“Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya kada ku fa&i kalmar ra’ina saboda tana da wata ma’ana marar kyau. Ku ce “unzurna”, ku saurara. Haƙiƙa kafirai suna da sakamakon azaba mai raɗaɗi”.

A fassarar ƙur’ani ta Ingilishi wadda Dr. Muhammad Taƙi-ud Din Al Hilali da Dr. Muhammad Muhsin Khan suka yi (1996:37) sun yi sharhi a kan wannan ayar suka ce, a fassarata.

Ra’ina da Larabci tana nufin yi a hankali. Saurare mu, kuma za mu saurare ka. Amma da Yahudanci kalma ce ta ɓatanci. Sai Yahudawa suka riƙa fada wa Annabi Muhammad (SAW) kalmar da nufin ɓatanci.

Haka ma a aya ta 46 a Surat An-Nisa’i, Allah ya sake kawo wannan magana kamar yadda fassarar Mohyidin ta nuna. (1996:227).

Akwai wasu Yahudawa da suke juyar da kalmomin Attaura daga bigirensu na haƙiƙa, suna kuma cewa, “Mun ji mun kuma ƙi yarda, kuma ka sani abin da ka faɗa bai shiga kunnuwanmu ba. Kuma suna cewa ra’ina. Suna tsiwa da harshensu da suka cikin addini. Da dai su ce: “Mun ji mun kuma bi, kuma ka ji mu, ka dakanta mana” to da ya fiye musu alheri, ya fi kuma daidai. Sai dai Allah ya riga ya tsine musu saboda kafircinsu, sannan ba masu ba da gaskiya sai ’yan kaɗan daga cikinsu.

“Allah jiƙe Malam” Bamaguje ya ce, maimakon “Allah jiƙan Malam”. Wato maimakon ya yi masa addu’a, ya roƙi Allah Ya yi masa gafara, sai ma ya yi masa fatar Allah Ya sa ruwa ya ba shi kashi. To amma sai wanda ya natsu, zai gane inda Bamaguje ya dosa. Liman shi ma ba kanwar lasa ne ba. Idan Bamaguje ya san wata ai bai san wata ba. Sai nan da nan aka ba shi ruwa! Tilas ya koka. Ya ce kai yi mani Hausa. Wai shi ba kafiri ne ba! A duba ma yadda Bamaguje ya ƙi ya amince da addu’ar da Liman ya yi ta “Allah Ya amsa”. Ai idan Allah Ya amshi rai, an mutu ke nan! Bamaguje bai son ladar Allah, amma ya yi sadakai!

An sake ganin irin wannan barkwanci a lokacin da Arne ya zo masallaci yana neman bawan Allah. Irin shigar da ya yi; baƙar taguwa, da baƙar hula, da walki ƙudu, da gatari, da idanuwa tulu-tulu, ta tsorata Malam Almu, wanda shi ne a masallacin a lokacin. Wannan shiga ta Arne, da zuwan sa wurin da ba a zaton zai zo, sun sa Malam Almu ya yi ta addu’a a ruɗe. “La haula wa la ƙuwata ni kai”. Kila ma yana neman ya gudu. Ga yadda suka gana (1954: 19).

Arne: Kai tsaya tambayarka zan yi. Akwai mutane cikin akurkin nan naku?

Malam almu: Ai tukuna, yanzu dai mu ke harama. An jima kaɗan za a taru. Sallar za ka yi yau?

Arne: Tir! Me ya kai ni wannan abin duƙe-duƙe ba wurin noma ba.

A dubi irin amsar da Arne ya bayar da aka nemi a ji ko yau zai yi sallar ne. Bai tsaya kurum ga cewa a’a ne ba, sai ma da ya ce tir! Wato Allah ya tsare shi da yin wannan abu marar kyau. Idan har zai yi duƙe-duƙe sai dai a gona! Wasan ya nuna yadda aka ci gaba da wannan raha bayan masallata sun gama salla. Da Arne ya tambayi Liman ko shi bawan Allah ne, Limamin ya ce: (1954:21) “To da kam bawansa ne ni, amma yanzu ya ’yanta ni”. Idan Liman zai ce shi ba bawan Allah ne ba, ai kuwa kila an ji wa salla!

Da yake Bahaushe mutum ne mai dangantaka wani abu na wauta da shirme da ƙauyanci ga wasu ƙabilu musamman Fulani, to a cikin wasan nan ma an yi haka. An nuna cewa yunwa ta sa wasu Fulani su uku sun ci biri a daji, amma suka yi alƙawari kada wani cikinsu ya yi maganar. An nuna sai da da suka bari sun shigo bainar jama’a, inda aka taru ana kallon Takai, sai suka fasa ƙwai! (1954:15).

Bafillace na Farko: Ho ɗan kare da ba da ƙishirwa.

Bafillace na Biyu: Hala kana so ka faɗi.

Bafillace na Uku: He ku faɗi, mun ci biri, mun ci biri, mun ci biri.

Da yake marubucin SHP ya nuna ana iya tsarma waƙa a wasan kwaikwayo, mun ga yadda aka kawo waƙoƙin Takai da raye-raye da waƙoƙin aure na ’yan mata. An kawo wata waƙar ’yan mata wadda kila yanzu gane ma’anarta ma sai maguzawan asali. (1954:14).

’Yan mata: Allah ba karo rana,

 Allah ba karo rana.

 Allah sa ango ya ishe,

 Im bai sihe ba ya kashe,

 Ya kai ga bango-ya matse

 Assalah-Salamu alaikum

 Assalah-Salamu alaikum

 Assalah baƙo ba zai rasa

 Gai da mai gida ba.

 Ga ɗiyarku nan,

 Ango kar ka zo ka koya mata ƙarya.

Haka ma idan aka duba halin wasu daga cikin manyan ’yan wasan (ginshiƙai), tun daga Liman na “rabo na biyu”, har ya zuwa Malam Kotakwana (rabo na bakwai), za a fahimci abu ɗaya; kishi tsakanin malamai musamman ga Malam Inkuntum. A ire-iren labaran Hausawa ana nuna cewa wai malamai kishin juna gare su. Wai kamar mata ne. To an nuna haka a cikin Malam Inkuntum. An gwada yadda malamai daban-daban suka yi ta jin haushi a kan irin falalar da Inkuntum ya riƙa samu, alhali kuwa shi ba mai jin ƙyashin su ne ba. Har wani gari dai da ya je duk al’amarin ɗaya ne. A can ma haushinsa aka riƙa ji. Ko da kuma ya nemi a rufa masa asiri saboda ƙarancin iliminsa, ko an yi alƙawarin ba rufawa ake yi ba. (1954:39).

Malam Inkuntum: Malam ho! Malam ho! To, ka dai san ni, ni kam na san ka. Saboda haka ina roƙon ka rufa mini asiri…

Malam Kotakwana: In Allah ya so haka za a yi.

Idan aka duba waɗannan misalan labarai, ana iya yanke hukunci a ce lallai wasan Malam Inkuntum, ɗaya daga cikin wasannin da suka biyo bayan SHP, ya bi sawun tsarin da East ya yi. An nuna yadda almara, da labarai, da wasanni tsakanin Hausawa da wasu maƙwabtansu, suka zama tushen wasan kwaikwayo. Wani kuma abin yabawa shi ne fatar da East ya yi ta cewa Hausawa su rubuta wasannin da suka fi nasa, ita ma ta tabbata. Malam Inkuntum, wasa ne da aka sarrafa Hausa a cikinsa ta salo mai ƙayatarwa, da birgewa, da dariya fiye da wasannin SHP. Ko da Malam Inkuntum ne kaɗai wasan da Hausawa suka rubuta, to ana iya cewa ba su ba East kunya ba. Buƙatarsa ta biya. Hasashen da ya yi ya tabbata. To ba ma shi kaɗai ne ba, ya bi sawun SHP.

Wasannin kwaikwayon da suka zo daga baya irin su “Ba tsimi da dabara”, na cikin Wasannin Yara na Umaru Dembo, da “Bora da Mowa” na cikin Bora da Mowa na U.B Ahmed, ai wasanni ne da za a iya danganta su da tatsuniyoyi. Wasan Amina Sarauniyar Zazzau na U.B Ahmed, da Gamji wanda Malumfashi ya fassara na Farfesa S.J Timothy – Asobele, duk sun shafi labarai ne da tarihi. Waɗannan kaɗai sun isa su nuna irin inda hangen nesan East ya kai. Amma bayani ba zai iya kai wa a kansu ba a nan, sai dai a tarbi gaba.

Kammalawa

Muna iya jaddadawa a nan domin naɗewa cewa ’yan Nijeriya ta Arewa, ko kuma mu fito fili ƙarara mu ce Hausawa, ba su ba East kunya ba. Sun tabbatar da abin da ya hanga. Idan an yi la’akari da abin da ya faɗa a farkon gabatarwarsa, da ya ce: (1936:3), “wannan littafi an tsara shi don ya bayyana muku wani irin wasa, wanda mutane suke ta yi ko’ina a cikin duniya tun tun tun tuni har yanzu…” to su ma Hausawa ba su bari an bar su a baya ba. Sun shiga fagen rubuta wasannin kwaikwayo, kuma suna taka rawar gani. Idan aka ɗebe wasanni guda shida da Dr. Rudolf Prietze ya rubuta, tun kafin a samu SHP, ana iya cewa Hausawa sun rubuta wasanni aƙalla hamsin a kan fannoni daban-daban daga 1936 zuwa yau. Ashe ke nan ba su bari duniyar ta tafi ta bar su ba. Wannan lissafi bai shafi ɗumbin wasanni da aka yi a rediyo, da talabijin, da dandamali ba, waɗanda ake yi kullum. A yau kuma ga wani salon wasan kwaikwayon ya ɓullo mai amfani da sabbin na’urori mai suna bidiyo. Shi ma kuwa yana sane da sanin muhimmancin tatsuniyoyi da labaran Hausawa, kamar yadda wasanni irin su “Salma-salma dudduf”, da “Kogin Bagaja”, da kuma “Diskin da riɗi” suka nuna. Da Hausawa na faɗa a ji a manyan kamfanonin ɗab’in da ake da su guda uku a ƙasar nan, ko kuma a ce suna da nasu kamfanonin da suka san inda aka dosa, ko kuma akwai wata hukuma da ta damu da adabin Hausa, da idan aka gaya wa East adadin wasannin kwaikwayon da Hausawa suka rubuta, da sai ya some domin murna.

Manazarta

Abubakar, M.S (2007), Taƙaitaccen Tarihin Daura. Kano : Ammani

Ahmed, U.B. (1971), Bora da Mowa, Zaria, NNPC.

Ahmed, U.B (1983), Amina Sarauniyar Zazzau, Zaria, Huda-Huda

Al Hilali, M.T, da Khan M.M. (1996), Interpretation of the Meanings of the Noble Ƙur’an in the English Language. Riyadh: Darussalam Publishers

Asobele, S.J.T (1993), Gamji, Lagos, Foundation Publishers.

Dembo, U. (1971), Wasannin Yara, Zaria, NNPC.

Dogondaji, A.A (1954), Malam Inkuntum, Zaria, NORLA.

East, R.M (1936), Siɗ Hausa Plays, London, West Africa Publicity Limited.

Furniss, G. (1997), Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburg, Edinburg University Press Ltd.

Idris, B. (1981), Matsolon Attajiri, Zaria, NNPC.

Imam, A. (2004), Magana Jari Ce, Zaria, NNPC.

Malumfashi, A.I. (2006), Gamji, Lagos, Upper Standard Publication.

Malumfashi, A.I. (2006), “Folktales, Hausa Drama and the ‘Prophecy’ of Dr RM East” in (eds) Rasheed, A and Aliyu, S.A. The Folktale in Nigeria, Zaria Ahmadu Bello University Press Limited 2014: 315-330

Mohyidin, B.A (2004), Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma, Fassara da Bayani USHUS India, Kerala Continental Book Centre.

Pwedon, B. (1977), “Thematic Conflict and Narratiɓe Techniƙue in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja,” Ph.D, University of Wisconsin

Sabir, A. (1976) Mutanen Kogo, Zaria, OUP.

Tunau, A. (1956), Wasan Marafa, Zaria, NORLA.

Usman, H. (2002), “Tatsuniya a matsayin tubulin wasan kwaikwayo: Nazari Kan Wasannin Kwaikwayon Hausa na Bidiyo”, B.A Project, Ahmadu Bello University Zaria.

Yahaya, I.Y. (1971), Daren Sha Biyu, Zaria: NNPC.

 Degel Journal

The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

Post a Comment

0 Comments