Ticker

6/recent/ticker-posts

5.5.1 Karigizo

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.5.1 Karigizo

 Jagora: Karigizo da girgiza Ɗan’malam.

 Amshi: Karigizo.

 Jagora: Inna ina bara ki ba ni na Allah.

 Amshi: Karigizo.

 Jagora: Ko ɗanɗanki nib buga ke Inna.

 Amshi: Karigizo.

 Jagora: Inna ki hanƙure ki ba ni na Allah.

 Amshi: Karigizo.

 (Karigizo)

Amshin wannan waƙa shi ne kalmar “karigizo”. Kalma ɗaya ce amma kalmar ba ta ɗauke da wata ma’ana, domin ba wani abu da ake ce wa karigizo. Haka ma amshin waƙar “Mata Dangin Fatsima” shi ma kalma ɗaya ce maras ma’ana. Misali:


Post a Comment

0 Comments