Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Sunayen alkunya su ne waɗanda ake ba mutum domin sakaya sunansa na yanka wanda ake jin nauyin faɗarsa.
A al’adar Larabawa, kunya takan
soma ne da kalmar Abu wadda take ɗauke
da ma’anar Baban. . . Akan jingina ta ga ɗan
fari na mutum ne. Misali, idan ɗan
mutum ya kasance sunansa Musa, kunyarsa sai ta zamanto Abu-Musa. Duk da haka,
ba kullum takan zama hakan ba. Akan iya yi wa mutum kunya da sunan wani daga
cikin ‘ya’yansa, ko kuma wani daga cikin dangi ko wani abu da yake so. Misali,
shahararren Sahabin Annabi S. A. W. wanda yake son ‘yar kyanwa. Ya shahara ne
da alkunyarsa ba da sunansa na yanka ba, wato Abu – Hurairah, wadda HURAIRAH
tana nufin ‘yar kyanwa.
Al-Miƙdad bin Amr, shi ne sojan
dawaki na farko a Musulunci. Ana yi masa kunya da Abul–Aswad, akan kira shi Abu–Umar, an kuma kira shi Abu–Sa’id.
Shi ne mutum na bakwai da ya bayyana karɓar
Musuluncinsa a sarari (fili).
Hamza bin Abdul-Muttalib an yi
masa kunya da ‘ya’yansa guda biyu ‘Ya’ala da Umarah.
Umar bin Al-Khattab an yi masa
kunya da Abu Hafs da dai sauransu.
Akwai kuma wasu sunayen alkunya
da suka zama na yanka da al’ummar Musulmi suke raɗa
wa ‘ya’yansu. Misalan irin waɗannan
sunayen su ne:
a. Abu-Bakar: Sunansa na yanka
shi ne, Abdullahi bin Amir bin Amr bin Ka’b bin Taim bin Murrah Alƙurashi
At-Taimi.
b. Jawairiyah bint Al-Harith:
Sunanta na yanka Barrah.
c. Maimuunah bint Al-Harith:
Sunanta na yanka shi ne Barrah.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.