Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Zuwan addinin Musulunci ya wanzar da samuwar sababbin sunaye a farfajiyar ƙasar Hausa. Wannan ya faru ne sakamakon yadda al’ummar Hausawa suka karɓi addinin Musuluncin da suka tsunduma gadan-gadan wajen koyon fannonin iliminsa. Hakan ya wanzar da samuwar mashahuran masana a cikin al’ummar, waɗanda suka taimaka wajen baza sunayen da suka dace al’ummar su raɗa wa ‘ya’yansu, tamkar yadda sunna ta bayyana.
Masanan sun yi ƙoƙari
bayyana wa al’ummar
muhimmancin saka wa abin da aka haifa sunayen da suke nuni ga bayar da wuya ga
Allah Maɗaukakin
Sarki. Irin waɗannan
sunaye sun haɗa da:
a. Abdul-Alim
b. Abdul-Aziz
c. Abdul-Ganiyyu
d. Abdul-Hakam
e. Abdul-Jabbar
f. Abdul-Jalil
g. Abdul-Ƙadir
h. Abdul-Karim
i. Abdullahi
j. Abdul-Malik
k. Abdul-Muminu
l. Abdul-Wahhab
m. Abdur-Rahman
n. Abdur-Razaƙ
o. Abdus-Salam, da sauransu.
Haka sun yi ƙoƙarin
bayyana wa al’ummar
Hausa sunayen Annabawan Allah da ManzanninSa da ya kamata su rinƙa raɗa wa ‘ya’yansu maza. Daga
cikin irin wannan sunayen sun haɗa
da:
1. Adamu
2. Al-Yasa
3. Ayyub
4. Dawud
5. Dhul-Kifl
6. Harun
7. Hud
8. Ibrahim
9. Idris
10. Ilyas
11. Is’haƙ,
12. Isa
13. Isma’il
14. Lut
15. Muhammad
16. Musa
17. Nuh
18. Salih
19. Shith
20. Shu’aibu
21. Sulaiman
22. Uzair
23. Ya’ƙub
24. Yahya
25. Yunus.
26. Yusha’u
27. Yusuf
28. Zakariyya
Sun kuma kawo tsarin sunayen
matan Annabi S. A. W. domin a yi amfani da su wajen raɗa wa ‘ya’ya mata da aka haifa. Daga cikin irin
waɗannan sunayen
akwai:
1. A’ishah
2. Hafsah
3. Jamilah
4. Juwairiya
5. Khadija
6. Maimunah
7. Mariyah
8. Raihanah
9. Ramlah
10. Safiyyah
11. Saudah
12. Umm Salamah
13. Zainab
Darussalam, (2004 p. 1-134) da
Hareeri & Tahir, (2009 p. 79).
Sun kawo jerin sunayen ‘ya’yan
Annabi S. A. W. duka domin al’ummar Musulmi su yi amfani da su wajen raɗa wa ‘ya’yansu. Sunayen
kuwa su ne kamar haka:
1. Abdullahi
2. Fatimah
3. Ibrahim
4. Ƙasim
5. Ruƙayya
6. Umm Kulthum
7. Zainab
(Hareeri & Tahir, 2009 p.
79).
Ba nan kaɗai suka tsaya ba, sun kawo jerin sunayen waɗanda aka yi wa albishir da
shiga Aljanna. Mutanen kuwa sun haɗa
da:
1. Abdur-Rahman bin Auf
2. Abubakar Siddiƙ
3. Ali bin Abu Talib
4. Amir bin Abdullah bin
Al-Jarrah
5. Sa’d bin Abu Waƙƙas
6. Sa’id bin Zaid
7. Talhah bin Ubaidullah
8. Umar bin Al-Khattab
9. Uthman bin Affan
10. Zubair bin Al-Awwam
(Hareeri & Tahir, 2009 p.
79).
Sun kuma kawo jerin sunayen waɗanda suka yi shahada a
fagen yaƙin
Badar. Shuhada’un kuwa
su ne:
1. Aƙil bin Bukair bin Abd
Yalil
2. Ammar bin Ziyad
3. Auf ko Audh bin ‘Afra’
4. Harithah bin Suraƙah
5. Mihja’ bin Salih
6. Mu’awwidh bin ‘Afra’
7. Mubasshshir bin Abdul Mundhir
8. Rafi’ bin Mu’alla
9. Sa’d bin Khaithamah Al-Ansari
10. Sa’d bin Mu’alla
11. Ubaidah bin Harith bin
Muttalib
12. Umair bin Abd Umair
13. Umair bin Abu Waƙƙas
14. Umair bin Humam
15. Yazid bin Harith
(Hareeri & Tahir, 2009 p. 80)
Hasali ma sun yi ƙoƙarin
bayyana sunayen waɗanda
suka halarci yaƙin Badar daga ɓangaren
Muhajuruna da kuma na Ansar.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.