Ticker

6/recent/ticker-posts

Ramuwar Sallolin Da Ba a San Adadinsu Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Don Allah ina da tambaya: yaya ake yin ramuwar sallolin farilla idan mutum bai san adadinsu ba? Wane tsari ya kamata a bi? Misali, shin mutum zai iya yin salloli biyar lokaci guda (ramuwa) yana ci gaba da yi har sai ya ji ya gamsu cewa ya biya abin da ke kansa? Ko kuwa sai ya riƙa yin kowace sallah a lokacin da ya tuna da ita daban-daban?

Haka kuma, shin ya halatta mutum ya riƙa yin nafila alhali yana da bashin sallolin farilla a kansa? Don Allah, a yi mana bayani Allah ya saka da alheri.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ramuwar sallolin da ba a san adadinsa ba shi ne a yi ƙiyasin abin da ake ganin ya wuce mutum, sannan a fara biya a hankali har sai an gama.

Ba lallai sai kin yi salloli biyar a lokaci guda ba, amma ya halatta a yi hakan domin hanzarta biyan bashin. Mafi sauƙi shi ne duk lokacin da kika yi sallar farilla ta yanzu, sai ki biyo da ramuwar sallar da ta gabata a tare, kullum haka zaki dinga yi har sai zuciyarki ta amince cewa kin gama biyan bashin.

Idan ba ki san ainihin adadin ba, sai ki ƙiyasi (wato ki ɗauka misali shekaru biyu+ ko ƙasa da haka) sannan ki fara biya. Allah Yana duban niyyar bawa ne da ƙoƙarinsa na gyarawa.

A taƙaice dai, ki fara biya a hankali tare da kowace sallar farilla ta yau da kullum, kuma ki sa rai Allah zai karɓa tunda manufarki ita ce tsarkake tarihin ibadarki.

Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa ya fi kyau mutumin da yake bin bashin farilla ya mayar da hankali wurin biyan bashin da farko kafin ya shagaltu da nafila. Duk da hakan ya halatta, amma kiyaye farilla shi ne fifiko a wurin Allah.

Anan nake so inyi miki gargadi game da barin sallah ta wuceki da gangan, ko kuma yin sakaci wajen ramasu. Wannan haramun ne domin kuwa yana daga cikin wasa da sallah. Kuma Allah fada cewa:

فَوَيۡلٌ لِّلۡمُصَلِّيۡنَۙ‏ ۝ الَّذِيۡنَ هُمۡ عَنۡ صَلَاتِهِمۡ سَاهُوۡنَۙ‏

"tsananin azaba ya tabbata ga masallata wadanda suke masu shagala daga sallarsu" (Surah: Al-Maa'un, Ayat: 4-5).

Sa’ad Ibn Abi Wakkas (RTA) ya ce: na tambayi Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi), a kan wadanda suke masu shagala daga sallarsu, ya ce shagala daga sallah shi ne jinkirta lokaci, ma’ana kin yin sallah a kan lokacin har lokacin sallar gaba ya shiga. An kirasu masallata sai dai kuma ga shi suna wulakanta ta, tare da jinkirta ta daga lokacin ta, Allah ya yi musu alkawarin ‘WAILU’ shi WAILU wata Tsananin Azaba ce, a wata fadar kuma an ce wani rami ne a cikin wutar Jahannama da za a saka dukkan duwatsun duniya a cikin sa da sun narke saboda tsananin zafin da yake cikinsa. To nan ne mazaunin masu wulakanta Sallah ko jinkirta ta daga barin lokacinta, sai dai wanda ya tuba ya yi nadama a bisa aikinsa na baya.

Allah ya fada cikin Suratul Mudassir yana mai bayar da labarin ‘yan wuta cewa:

مَا سَلَـكَكُمۡ فِىۡ سَقَرَ‏ ۝ قَالُوۡا لَمۡ نَكُ مِنَ الۡمُصَلِّيۡنَۙ‏ ۝ وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ الۡمِسۡكِيۡنَۙ‏ ۝ وَكُنَّا نَخُوۡضُ مَعَ الۡخَـآٮِٕضِيۡنَۙ‏ ۝ وَ كُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ الدِّيۡنِۙ‏ ۝ حَتّٰٓى اَتٰٮنَا الۡيَقِيۡنُؕ‏ ۝ فَمَا تَنۡفَعُهُمۡ شَفَاعَةُ الشّٰفِعِيۡنَؕ‏

me ya shigar da ku cikin sakar? sai suka ce ‘ba mu kasance cikin masu sallah ba, kuma ba mu zamo cikin masu ciyar da matalauta ba, kuma mun kasance muna kutsawa tare da masu kutsawa, mun kasance muna karyata ranar sakamako har gaskiya (wato mutuwa) ta zo mana, saboda haka, ceton mai ceton masu ceto ba zai amfane su ba! (Suratul Mudassir aya ta 42-48).

Ubangiji mai girma da daukaka yana cewa:

فَخَلَفَ مِنۡۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٌ اَضَاعُوا الصَّلٰوةَ وَاتَّبَعُوا الشَّهَوٰتِ فَسَوۡفَ يَلۡقَوۡنَ غَيًّا ۙ‏ ۝ اِلَّا مَنۡ تَابَ وَاٰمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًـا فَاُولٰٓٮِٕكَ يَدۡخُلُوۡنَ الۡجَـنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُوۡنَ شَيۡــًٔـا ۙ

"Sai wadansu yan baya suka maye a bayansu suka tozarta sallah, kuma suka bi sha’awowinsu, to da sannu za su haɗu da azaba, face wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na kwarai to waɗannan za su shiga aljanna kuma ba za a zaluncesu da komai ba." (Surah: Maryam, Ayat: 59-60).

Kiji tsoron Allah, ki kiyaye dokokinSa. Sallah ita ce rukunin Musulunci na biyu bayan shahada, kuma ita ce ke raba musulmi da kafiri. Ita ce mafi girman dukkan ibadodi kuma ita za'a fara dubawa aikin ayyukanki aranar Alkiyamah. Idan tayi kyau kin tsira. Idan kuma ta ɓaci (saboda rashin yinta akan lokaci, ko rashin yinta da ilimi, ko rashin sanya tsoron Allah cikinta) to mutum yayi asara mai girma. (Allah shi kiyayemu).

Wajibi ne mutumin da ya tsinci kansa a wannan hali ya tuba zuwa ga Allah, ya kuma kiyaye lokutan sallolinsa a kan yadda addini ya tsara.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Za ku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments